𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Malam ya
dawainiya da al'umma da taimako wajen fahimtar dasu akan abin daya shige musu
duhu. Allah ya karawa malam hakuri da juriya da mutane. Ameen.
Malam tambaya ta anan itace
'mutum ne ya kai shekaru hudu da rasuwa kuma ana binshi bashin Azumi, yaran shi
basu biya mishi azumin da ake binsa ba, amma dangin shi suke so su biya mishi'.
To yaya azumin zai kasance kenan wajen ramukon?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam wa
rahmatullahi wa barakatuhu.
Lallai akwai hadisi Sahihi wanda
Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) yace : "DUK WANDA YA MUTU DA
AZUMI AKANSA, TO WALIYYINSA YAYI MASA AZUMIN".
To amma Malamai sunyi ma hadisin
fahimta daban daban.
Wasu daga cikin Maluman Hadisi da
kuma Abu Thaur sunce ya halatta Waliyyin mutum (wato Makusancinsa) yayi masa
azumi amadadinsa, saboda hujjar wannan sahihin Hadisin.
Maluman Ahlul Baiti da Imamu
Malik da Abu Hanifah sun ce ba za'ayi azumi amadadin Mamaci ba. Abinda ya za
wajibi shine aciyar da Miskini guda bisa kowanne azumi guda da ake bin Mamacin.
Sun kafa Hujjah da Hadisi Sahihi wanda Imamut Tirmidhiy ya ruwaito daga
Sayyiduna Abdullahi bn Umar (ra) : "WANDA YA MUTU DA AZUMI AKANSA, TO
ACIYAR DA MISKINI GUDA BISA KOWACCE RANA".
(Ibnu Maajah ma ya ruwaito irinsa
acikin Sunanu nasa, kuma Hadisi ne Sahihi).
Abinda ke Qara Qarfafar wannan
shine Fatawar da aka samu daga Sayyidah A'ishah da kuma Ibnu Abbasin (ra) akan
cewa ciyarwar za'ayi.
Ibnu Qudaamah yace Wannan ita ce
Sahihiyar Fatawar Mafiya yawan Ma'abota ilimi. Kuma an ruwaito haka daga Nana
A'ishah da Ibnu Abbas (ra). Kuma ita ce Fatawar Maliku da Layth bn Sa'ad da
Auza'iy da Sufyanuth Thawree da Shafi'iy da Hasan bn Hayyin da Ibnu 'Ulayyah da
Abu Ubaidin acikin Sahihiyar Magana daga garesu.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
RAMUWAR AZUMIN MAMACI
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul
Laah. Malam, ’yar’uwarmu ce ta rasu a cikin Ramadan ɗin nan alhali ba ta yi waɗansu daga cikin azumman
watan ba. A bara ma akwai waɗanda
ake bin ta duk a sakamakon rashin lafiya. To wai yaya za a yi wurin rama mata?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laahi Wa Barakaatuh.
Malamai sun kasa azumman da ake
bin mamaci saboda dalilin rashin lafiya ne kamar haka
1. Idan tun farko rashin
lafiyarsa mai tsanani ne wanda shari’a ta ɗora
masa ciyarwa kaɗai a
maimakon duk yinin da bai iya yin azumin a cikinsa ba, sai kuma ya rasu a hakan
bai ciyar ba, to wajibi ne magadansa su ciyar masa. Ba rama masa azumi za su yi
ba.
2. Idan kuma rashin lafiyar irin
wanda aka ɗora masa
ramawa ne idan ya warke, sai kuma ya warken amma bai rama ba har ya rasu, to a
nan malamai sun sha bamban a kan hukuncinsa. Maganar da ta fi daidai, in
shaa’al Laah ita ce: Magadansa su ciyar masa da abinci kawai.
Dalilin hakan kuwa shi ne fatawar
da A’ishah da Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhum) suka bayar a cikin Sunan
Abi-Daawud: 2301, da Musannaf Ibn Abi-Shaibah: 3/113 da At-Tahaawiy a cikin
Mushkilul Athaar: 2/142 da Ibn Hazm a cikin Al-Muhallaa: 7/4. Ita ce kuma
sahihiyar fassara ga hadisan da suka riwaito a kan haka daga Annabi (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a cikin Sahih Al-Bukhaariy: 1952, 1953 da
Sahih Muslim: 1147, 1148.
3. Idan kuma rashin lafiyar irin
wanda yake fata ya rama ne idan ya warke, amma kuma sai bai warken ba har zuwa
rasuwarsa, to a nan malamai sun yarda cewa babu wani laifi a kansa. Haka ma
magadansa.
4. Idan kuma azumin da ake bin sa
na wani alwashi ko bakance ne da ya yi wa Ubangiji Ta’aala, kuma har ya rasu
bai biya ba, to shi kam lallai magadansa su rama masa, ko dai ta hanyar yin
azumin a ranaku mabambanta, ko kuma ta hanyar su haɗu dukkansu su yi a rana guda.
Ana iya duba Tamaamul Minnah:
2/172-174 na Al-Azzaaziy domin ƙarin bayani. Ko kuma: Tambaya ta A324 a
kan Rama Azumin Mamaci.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Ga masu tambaya sai su turo ta
WhatsApp number: 08021117734
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.