Ticker

Ramuwar Azumi Ga Mai Olsa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Matar da ake bin ta Azumin Ramadan biyar, da kyar ta iya rama guda biyu saboda olsa, sannan kuma yanzu ga ciki, yaya za ta yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Marasa lafiya da suka kasa yin Azumin Ramadan nau’i biyu ne, in ji malamai

1. Idan rashin lafiyar da ake tsammanin samun waraka ne, to sai ya bari har sai ya warke sannan ya rama saboda ayar da ta ce:

 فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِیضًا أَوۡ عَلَىٰ سَفَرࣲ فَعِدَّةࣱ مِّنۡ أَیَّامٍ أُخَرَۚ

Daga cikinku duk wanda ya zama mara lafiya ko kuma yana cikin tafiya, to sai ya biya adadin wasu kwanakin na daban. (Surah Al-Baqarah: 184)

Idan kuma bai warke ba har zuwa ƙarshen ajalinsa, a nan malamai sun ce babu laifi a kansa, kuma babu komai a kan danginsa ta fuskar ramuwa ko ciyarwa, matuƙar dai ba ya warke ne sannan ya yi sakaci da jinkirin ramawa har zuwa aukuwar ajalin nasa ba.

2. Idan rashin lafiyan kuma irin wanda ba a sa ran warkewa ne kamar na tsufa, to sai ya bayar da abinci ga talakawa a maimakon duk yinin da bai yi azumin ba. Idan kuma ya bari har sai a ƙarshen Ramadan sannan ya tara talakawan ya ciyar da su, kamar yadda Sahabi Anas Bn Maalik (Radiyal Laahu Anhu) ya yi, hakan ma daidai ne.

Idan a bayan ya ciyar sai kuma ya warke, to duk da haka dai malamai sun ce ramuwa ba ta wajaba a kansa ba.

3. Ita mai ciki ko mai shayarwa kuwa idan ta kasa yin Azumin Ramadan malamai sun sha bamban a kan al’amarinta. Amma maganar da ta fi rinjaye a wurin malamanmu ita ce: Abin da Ibn Umar da Ibn Abbaas a cikin Sahabbai (Radiyal Laahu Anhum) da Ibn Al-Jubair a cikin Tabi’ai (Rahimahumul Laah) suka zaɓa cewa: Ciyarwa ce kaɗai a kan ta, amma ba ramuwa ba. Musamman dayake ba a samu wanda ya saɓa wa waɗannan Sahabban guda biyu a kan hakan daga cikin sahabbai ba, in ji Ibn Qudaamah a cikin Al-Mughnee: 4/395.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments