Ticker

Ranakun Da Ba A Azumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Ina son ƙarin bayani a kan ranakun da aka hana yin azumi. Na gode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Malamai sun lissafa ranaku da yanayin da shari’a ta hana musulmi yin azumi a cikinsu, kamar haka

1. Ranakun Idi Biyu, wato: Babba da ƙaramar sallah, ko na farilla ko na nafila. (Sahih Al-Bukhaariy: 1990, Sahih Muslim: 1137).

2. Ayyaamut Tashreeq, wato: Ranaku uku a bayan babbar sallah. (Sahih Al-Bukhaariy: 1997-1998).

3. Azumin Nafila a ranar Jumma’a sai dai in ya yi azumi kafin ita ko in zai yi a bayanta. (Sahih Al-Bukhaariy: 1985, Sahih Muslim: 1133).

4. Azumin Nafila a ranar Jumma’a, sai dai in wani azumin ne da ya saba yi. (Sahih Muslim: 1144).

5. Azumin Nafila a ranar Asabar in dai ba na farilla ba ne. (Sahih Ibn Maajah: 1403, Irwaa’ul Ghaleel: 960).

6. Azumin Nafila a ranar Shakka: Wato yinin da ba a tabbatar ko ƙarshen Shaabaan ne ko kuma farkon Ramadan ne ba. (Sahih Abi-Daawud: 2022).

7. Azumin Nafila kafin Ramadan da yini ɗaya ko biyu, sai dai in wani azumi ne da ya saba yi. (Sahih Al-Bukhaariy: 1914, Sahih Muslim: 1082).

8. Azumin Shekara: Wato wanda yake yin nafila a kullum har tsawon shekara. (Sahih Al-Bukhaariy: 1977, Sahih Muslim: 1159).

9. Azumin Nafila ga mace ba da izinin mijinta ba, alhali kuma yana gari. (Sahih Al-Bukhaariy: 5192, Sahih Muslim: 1026).

10. Al-Wisaal: Wato sadar da azumin nafila na yini biyu ko fiye ba tare da shan ruwa ba. (Sahih Al-Bukhaariy: 1965, Sahih Muslim: 1103).

Domin ƙarin haske ana iya duba littaffan Fiqhu na Sunnah, kamar: Fiqhus Sunnah na As-Sayyid Saabiq da Sahih Fiqhis Sunnah na Kamaal Bn As-Sayyid Saalim da Al-Mausuuatul Fiqhiyyatul Muyassarah na Al-Awaayishah da Tamaamul Minnah Fee Fiqhil Kitaab Wa Sahihis Sunnah na Al-Azzaaziy.

Allaah ya ƙara mana fahimta da kafewa a kan Sunnah Sahihiya.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments