Saduwa Da Wacce Ba Kwananta Ba

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As-Salaam Alaikum. Ni ce mijina ya neme ni ba a ranar kwanana ba sai na ƙi, to ko ina da laifi? Yana da’awar cewa wai lokaci kawai yake jira ya sake wacce kwananta ne.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

    Idan kin sani ko idan kina da marinjayin zaton cewa, da gangar yake son danne haƙƙin wata daga cikin matansa, to kin yi daidai, kuma babu wani laifi a kan ki, in sha Allah. Domin bai halatta a taimaka wa maɓarnaci a kan aikinsa na ɓarna ba. Ubangiji (Tabaaraka Wa Ta’aala) ya ce

    وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ وَالتَّقْوَى وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ وَاتَّقُوا اللَّهَ إِنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ

    Kuma ku taimaki juna a kan alheri da ƙarin taqawa, kar ku taimaki juna a kan zunubi da zalunci, kuma ku ji tsoron Allaah. Lallai Allaah mai tsananin uƙuba ne. (Surah Al-Maa’idah: 2).

    Da’awarsa cewa wai lokaci kawai yake jira ya sake ta, wannan bai isa dalilin da zai sa a goya masa baya a kan zalunci ba. Wajibi ne ya bari har sai igiyar auren da ke tsakaninsu da ita ta katse da farko. Daga nan ne zai zama babu sauran haƙƙin kwananta a kansa. Sannan ke kuma a lokacin ba ki da haƙƙin hana masa kan ki.

    Idan kuma ya ƙaurace wa waccan matar saboda gyara wani abu na mummunan hali ko ɗabi’arta ne, har kuma saboda haka ya daina shiga ɗakinta, to shi ma daidai ne. Kuma a nan ma bai halatta ke ki ƙi amincewa da shi ba. Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ƙaurace wa wata daga cikin matan aurensa na wani lokaci, kuma bai daina shiga wurin sauran matansa ba. Al-Imaam An-Nasaa’iy ya kawo shi da isnadi Sahihi a cikin littafinsa: Ishratun Nisaa’i: 7920-266.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.