Shin Akwai Wasu Nafiloli Da Ake Yi A Watan Ramadan?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Barka da asuba antashi lfy ya gida ya kokari Allah taimaka. Mlm dan Allah wani tambaya ne Nike so à amsa mana wai acikin ramadan akwai wasu nafiloli da ake yi wai ɗaya ga azumi ayi nafila raka'a 2 har izuwa karshe haka za à dungayi wasu ace in ansalame ayi ya latifu ko ko duk Wanda mutum yayi ko ko daman akwai wayanda aka ware adunga yinsu???

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To bayin Allah ire iren wadannan nafilfilin duk basu da asali a sunnar manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam duk wata sallar nafila da akace muku kuyi raka'a adadi kaza bayan kun gama ku karanta wani wuridi adadi kaza zaku samu ladan Annabi kaza ko ladan shekaru dubu kaza dasauransu, to ire iren sallolinnan da zakuji wasu suna cewa ayi a daren ramadan kowane dare nau'in sallar daban haka dai har zuwa karshen ramadana duk Basu da Asali a sunnah. Kuma kuce dasu su fada muku wanda ya rawaito sallolin na tabbata har ramadanan ya wuce bazasu baku ingantaccen dalilin idan ma sun kawo muku hadisin to idan kuka bincika hadisin zakuga cewa Duk hadisan karyane wato hadisaine kawai na karya wasu suka kirkira suke umartar mutane.

Amma dai babu laifi mutum yayi sallar dare irin wacce sunnah ta koyar wato wutiri kenan, ita kuma mafi karanci shine mutum yayi raka'a ɗaya ko raka'a uku ko biyar ko bakwai ko tara dasauransu, Amma da dai Adadin raka'o'in da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya kasance yanayi sune raka'a 13 ko kuma raka'a 11 kuma wannan sune mafi dacewar sallolin dare, kamar yadda aka tambayi matar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam Wato Nana Aisha uwar muminai Allah ya kara mata yarda cewa: Yaya Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yake sallar dare a cikin ramadan??? Sai ta bada amsa da cewa: Baya wuce raka'a 11 acikin ramadan ko a wajen ramadan (Bukhaari, 1909; Muslim, 738).

Yaku masu shigo da sallolinda babu su a koyarwar manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam kuji tsoron Allah kunji dai ga yadda aka rawaito Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yana Sallar nafila a daren watan Ramadan da wajen watan ramadan, Shin ku da kuke umartan mutane cewa suyi sallar nafila raka'a kaza a dare na kaza a karanta sura adadi kaza da wuridi sau adadi kaza shin daga ina kuka samo sallar???

Allah shine mafi Sani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam


Post a Comment

0 Comments