𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum, malam barka,
malam dan Allah ina son in san actual shekarun da namiji azumi ya wajaba a gare
shi, muna da yaro yana cikin shekara ta 15 Amma muryar shi ta yi nauyi kuma
gashin hamata ya fito masa amma abun da ba mu sani ba ko ya yi mafarki, to shi
ne bai son yin azumi ni kuma ina ganin kamar azumi ya wajaba a gare shi amma
babansa yana yi masa daukar karamin yaro.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam, Duk yaron da
waɗannan abubuwa
guda uku suka tabbata a tare da shi, to babu shakka ya kai haddin balaga
1. Tsurowar gashin mara, ko na
Hammata.
2. Kai wa shekara goma sha biyar
(15).
3. Yin mafarki.
Matuqar ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa uku ya sami yaro namiji, to ya
balaga, kuma azumi da sauran ibadoji kamar sallah da sauransu, sun hau kansa.
Idan kuma mace ce sai a qara mata
da
4. Al'ada ko Haila.
Dazarar ɗaya daga cikin huɗun nan ya tabbata ga ƴa mace, to ita ma azumi
da sauran ibadoji sun wajaba a kanta. Saboda haka, kuskure ne a bar yaron da ya
kai shekara goma sha biyar (15), ko ya taɓa
yin mafarkin saduwa, ko gashin mara da hamata suka fito masa ya qi yin azumi.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖��𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.