Ticker

Shin Ya Halasta Mace Ta Zauna Da Mijin Da Ba Ta So?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmatullah ta'ala wabarakatuhu, da fatan kun tashi lafiya, tambayata ita ce shin ya halatta a addini miji ya zauna da macen da ba ta son shi? Don yanzu shekara huɗu da aurensu amma har yanzu ba ta son shi, duk abun da za ta masa tana yi ne don kar Allah ya kama ta da laifin muzguna wa mijinta, wani lokaci ma hakan na gagararta kuma kullum sai ta roqi Allah ya ba su zaman lafiya, amma mijin ma ba ya ganin hakan, in ya tashi ya rinqa jefar ta da munanan kalamai, don Allah ga tambayata, mafita nake nema.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu Warahmatullah, ƴar uwa ya halasta mace ta zauna da mijin da ba ta so idan ta san za ta iya kiyaye masa haqqinsa na aure, saboda matuqar mace ba ta sauke haqqoqin mijinta saboda ba ta son shi, to Allah zai kama ta da wannan haqqi da ta qi bayarwa ga mijinta.

Don haka nake ba ki shawara a kan ki yi haquri ki ci gaba da zama da wannan miji naki tun da ga shi har kin yi haqurin zama tare da shi na tsawon shekaru huɗu, kuma ki riqa ba shi dukkan haqqoqin aure gwargwadon iko, in Allah ya so Allah zai daidaita tsakaninku matuqar kika ji tsoron Allah a al'amarinki.

Ayar Alqur'ani a suratul Baqara, aya ta 216 ta tabbatar da cewa

وَعَسَىٰ أَن تَكْرَهُوا شَيْئًا وَهُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ وَعَسَىٰ أَن تُحِبُّوا شَيْئًا وَهُوَ شَرٌّ لَّكُمْ وَاللَّهُ يَعْلَمُ وَأَنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ

 Za ku iya qin abu amma ya zamo shi ne mafi alheri a gare ku, za kuma ku iya son abu ya zamo shi ne mafi sharri a gare ku, Allah ne masani, ku ba ku da sani.

Saboda haka ki cire wa kanki wannan qiyayya da kike ma wannan mijin, saboda wata qila mijin da kika so ki aura amma Allah bai ba ki shi ba, wata qila shi ne mafi sharri a gare ki, sai Allah ya tausaya maki ya ba ki wanda ba shi ba, duk abin da kika ga Allah ya qaddara maki, to kawai ki sallama wa Allah, ki ɗauka hakan shi ne alherin, shi Allah ya san hikima da dalilin yin hakan. Kuma in kin san akwai wata kalma maras kyau, ko wata ɗabi'a maras kyau da kike yi masa, to ki ji tsoron Allah ki daina, domin wata qila ita ce dalilin da ya sa shi ma yake muzguna maki ba don yana da nufin yin hakan ba tun asali.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments