Ta Yi Sallar Tarawihi Da Earpiece

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum Warahmatallahi Wabarkatahu. Wata ce naga zatayi sallar tarawih sai ta kunna karatun Qur'ani tasa earpiece, wai sai ta rinka bin karatun sabida ta tsawaita sallar. shin yin hakan ba laifi?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

    Qwarai kuwa akwai laifi domin kuwa hakan da tayi bidi'a tayi, babu wanda yasata yin hakan.

    Alqur'ani yakamata ta ɗauka ta riqe tana kallo tana karantawa, inkuma bata iya karatunba, saita samu wata sura wacce ta haddace koda qulhuwallahu ne, sai takama qulhuwallahu tayita maimaitawa taita maimaitawa, kai koda aya ɗaya rak ta haddace to ya halasta kiyita maimaita wannan ayar harki gama tsayuwar kamar ilahinnas misali wannan ayar ace ita kawai ka iya acikin alqur'ani toh babu laifi kayita maimaitata har kagama tsayuwan darenda zakayi, domin hadisi ya tabbata manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yayi tsayuwar dare guda babu ayarda yake karantawa face wani yankin wata aya can suratul ma'ida

    إِن تُعَذِّبْهُمْ فَإِنَّهُمْ عِبَادُكَ وَإِن تَغْفِرْ لَهُمْ فَإِنَّكَ أَنتَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ  

    ''Idan Ka azabta su, to lalle ne su, bãyinKa ne, kuma idan Ka gãfarta musu, to, lalle ne Kai ne Mabuwayi Mai hikima.'' (suratul Mâ'ida Aya ta 118)

    Wannan yankin ayar itace yayita maimaitawa har yagama tsayuwar dare, kuma kasan dai tsayuwar Annabi ba irin taka bace.

    Allah yasa mudace.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.