Wannan nau’i ne na tuwo da ake samarwa daga dawa. Yana daga cikin tuwon da za a iya samun maza da mata da kuma yara na ci, a ƙauyuka da kuma wasu ɗaiɗai kun mutane da ke zaune a cikin birane. Duk da haka, akwai jama’a da dama da ba sa amfani da wannan nau’in na tuwo dalilin tasirin zamani da kuma samuwar wasu nau’o’in abinci daga baƙin al’ummu, musamman Larabawa da Turawa.
Mahaɗin
Tuwon Dawa
Akwai abubuwan da ake buƙata yayin samar da tuwon dawa, abubuwan sun kasance kamar haka:
i. Dawa
ii. Kanwa
iii. Ruwa
Yadda
Ake Yin Tuwon Dawa
Akwai matuƙar kama tsakanin yadda ake samar da
tuwon dawa da na gero. Kusan za a iya cewa, abin da ya
bambanta su kawai shi ne, ana yin amfani da gero wurin samar da tuwon gero,
yayin da a ɗaya ɓangaren kuma, da dawa ake amfani yayin samar da
tuwon dawa. A taƙaice, babu buƙatatar bayani dalla-dalla dangane da
wannan nau’i na tuwo saboda kamancin da ya yi da na gero.
Tsokaci
Tamkar dai yadda lamarin yake ga tuwon gero, tuwon dawa gama-gari ne ga mata da maza, yara da manya. Sai dai amfani da tuwon dawa na ƙara ja baya saboda tasirin da abincin zamani ke yi a kan na gargajiya. Wannan ya sa a gidajen masu hannu da shuni ba su kallon tuwon dawa a matsayin tuwo mai daraja da amfani ga jikin mutum. Hakan na sa yaran irin waɗanna gidaje su taso ba tare da sabo da wannan nau’i na abinci ba, tare da rashin ba shi daraja a cikin jerin abincin Bahaushe, hakan ya jawo wasu mata da dama ba su fahimci yadda ake tuƙa shi ba. Kusan akan samu gidajen da ke amfani da tuwon dawa a dukkanin yankunan ƙasar Hausa da suka haɗa da Kano da Katsina da Zamfara da Sakkwato da Kabi da dai sauransu.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.