Wannan nau’in abinci ne da ake sarrafa dusa domin samar da tuwo. Za a tara dusa adadin yadda za ta isa a yi tuwo da ita. Kenan dai ba dusar kwana ɗaya za a yi tuwo da ita ba sai ta kwana biyu ko uku. Idan kuwa ta rana ɗaya ake buƙatar yin tuwo da ita, za a yi karo-karo ne a ba wa mutum guda don ya tuƙa tuwon dusar. Tuwon dusa dai ba kullum ake yin sa ba a gidan Bahaushe. Ana ɗaukar lokaci mai tsawo kafin a tuƙa shi. Abinci ne na gargajiya da ake gudanar da shi a ƙasar Hausa.
Mahaɗin
Tuwon Dusa
i. Dawa ko Gero
ii. Ruwa
Da farko, mutanen yankin Kabi na kiran wannan nau’in tuwo da ƙudu-ƙuduri. Idan za a yi shi, dusa za a samo ta dawa ko gero a zuba ta a turmi a yi ta dakawa sai ta yi laushi ta zama gari. Daga nan sai a mulmula ta kamar yadda
ake mulmula dawo in za a sanya
shi cikin tukunya. Da zarar an kammala, sai batun kunna
wuta tare da aza tukunya da ruwa.
Bayan ruwan ya yi zafi sosai, za a ɗauko
dunƙulan na dusa a sanya cikin tukunya kamar dawo. Za a bar shi nan cikin tukunya har
sai ya nuna. Da zarar ya nuna yadda ya kamata, sai batun fitarwa tare kuma da sanya miya domin ci. Shi ma tuwon dusa an fi haɗa
shi da miyar kwaɓe ko sansamin kuka.
Tsokaci
Shi ma tuwon dusa akasari mata da yara ƙanana ne ke yawan cin sa a yankunan ƙauyuka da garuruwan ƙasar Hausa. Da wuya a samu masu cin tuwon dusa daga cikin mutanen birni, hasali ma wasu ba su san yadda ake yin sa ba. Bayan wannan, a ƙasar Hausa ba kowane gari ake yin tuwon dusa ba. An fi yin sa a garuruwan Kabi da Sakkwato da Zamfara. Ba a cika yin tuwon a garuruwan Zazzau da Katsina da Kano da sauran garuruwan ƙasar Hausa ba. Tuwon dusa cin sa yana da amfani sosai musamman ga maza da mata saboda yana daga cikin abincin da ke ƙara wa jikin mutum ƙarfi da kuzari. Masana kimiyyar abinci sun tabbatar da alfanun abincin da aka yi da dusarsa ga lafiyar jiki tare da kariya ga cututtuka irin na suga (Diabetes) da dangoginsu. Kenan tuwon dusa ba mata da yara kaɗai ya kammata su riƙa cin sa ba, har da maza manya. Sai dai yana da kyau a kula sosai, tare kuma da kauce wa amfani da dusar da ta daɗe a ajiye. A koyaushe a riƙa amfani da saburwar dusa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.