Tuwon ƙasari dai nau’i ne na tuwo da ake amfani da ƙasari yayin samar da shi. Ƙasari kuwa ruwa ne da aka yi amfani da shi wajen wanke geron da aka surfa. Irin wannan nau’in tuwo na ɗaya daga cikin daɗaɗɗun abincin gargajiyar Bahaushe. Baya ga haka, wannan nau’i na tuwo ba kullum ake yin sa ba. Dalili kuwa shi ne, akwai buƙatar tanadar wannan ruwa na ƙasari daidai gwargwadon adadin da zai isa a samar da tuwon. Wani lokaci mata da yawa kan yi karo-karon ruwan ƙasari ga mace guda domin ta yi amfani da shi wurin samar da tuwon ƙasari. Kodayake an fi samun irin haka a gidajen da ke da tsari na zaman gandu.
Mahaɗan Tuwon Ƙasari
Yayin samar da tuwon ƙasari, akan nemi kayan haɗi kamar haka:
i.
Gero
ii. Kanwa
iii. Ruwa
Yadda
Ake Tuwon Ƙasari
Abu na farko da za a fara tanada shi
ne gero wanda aka sussuke aka fitar masa da tsakuwa da sauran wasu hakukuwa. Daga nan sai a saka
geron a turmi a surfe shi sosai. Bayan an surfe, sannan sai a wanke, tare da fitar da ƙasari. Ruwan nan da aka wanke geron da shi, shi ake kira ƙasari. Za a iya tara shi mai yawa. Za
a rufe wannan ruwan ƙasari
har sai ya kwana. Wannan ne ma ya sa akan sanya kanwa ko toka ciki, domin ya
rage tsami.
Za a ajiye ƙasarin wuri mai kyau a rufe shi da
wani faifayi ko baho, har sai ya kwana ɗaya. Galibi idan aka bar shi ya yi kwana ɗaya ya fi daɗi matuƙa. Amma a wasu lokuta, akan bar ƙullin ƙasari a ajiye har na
tsawon kwanaki biyu. Da safe za a ɗauko ƙasarin a tsiyaye ruwan da ya kwanta a samansa. Ana kiran wannan ruwan da aka tsiyaye da tsagaro ko ruwan yami. Idan aka
tsiyaye za a tarar da ƙullin
ƙasarin ya kwanta ƙasa. Shi wannan ƙullun shi ne za a gauraya, ya haɗe wuri ɗaya ya yi kamar ruwa-ruwa. Daga nan
kuma sai batun hura wuta tare da aza tukunya.
Za a sanya ruwa madaidaici cikin tukunya. Yayin da ruwan ya tafasa, za a samo
wani kwano ko tukunya a rage a aje gefe, sauran a bar shi cikin tukunya. Daga
nan sai a ɗauko ƙullin ƙasarin
nan da ke aje a zuba a cikin tukunya ya haɗe da ruwan zafi. Sannan a ɗauko muciya a yi ta juyawa a hankali tun yana ruwa-ruwa har sai ya yi kauri sosai ya zama
tuwo. Daga nan za a rufe tukunyar, a bar
shi na tsawon wani lokaci don ya salale. Bayan nan wasu suna sake tuƙawa, Idan kuma ba a buƙata, sai a kwashe shi haka nan. Shi ke
nan an kammala tuwon ƙasari. Galibi ana cin wannan tuwon da miya mai yauƙi.
Misali miyar kuɓewa ko karkashi da sauransu.
Tsokaci
Ba koyaushe ake cin tuwon ƙasari ba. Sannan galiban, tsofafi da matan da ke zaune a cikin ƙauyuka ne suka fi yin tuwon ƙasari, saɓanin mutanen birni inda wasu ba su ko taɓa kallon wannan nau’in tuwo ba; sai dai ɗaiɗaikun lokuta musamman yayin da suka kai ziyara zuwa ƙauyuka. Tsofaffi na son wannan tuwo
kasancewar sun fi son abinci mai laushi, wato ba mai tauri ba. Bayan haka, an
fi samun irin wannan abinci a yankunan Sakkwato da Kabi da Zamfara. Ma’ana ba a faye samun irin wannan
tuwo a ƙasashen Zazzau da Kano, da kuma sauran garuruwan Hausawa ba.
Duk da haka wasu ba su buƙatar
cin tuwon ƙasari a
sakammakon tsamin da ke ga tuwon a sanadiyar tsamin zai iya jawo wasu cututtuka
ga wasu ɗaiɗaikun
mutane. Sai dai kuma tuwon zai yi amfani a wajen tsofaffinmu a yanzu. Yana da kyau a riƙa tuƙa musu shi don kauce wa
cin abincin zamani da zai iya ɓata masu ciki kai tsaye. Yin amfani wannan
nau’in tuwo zai taimaka ainun
wajen farfaɗo da abincinmu na gargajiya.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.