Tuwon maiwa tuwo ne da ake amfani da maiwa a wajen yin sa. Maiwa kuwa ƙwaya ce daga cikin nau’o’in amfanin gonar Bahaushe da ke kama da gero. Galibi a ƙauye aka fi amfani da tuwon maiwa. Duk da cewa ko a ƙauyuka ba ko’ina ake yin tuwon maiwa ba. A hannu guda kuma, akasari a ƙauyuka ba kowace mace ce ta iya tuƙa tuwon maiwa ba. Wani lokaci abin da yakan hana wasu tuƙa tuwon maiwa shi ne wahalar da ke tattare da yin sa, ko kuma ma rashin iya shi. Tuwon maiwa dai nau’in tuwo ne wanda yara da manya, maza da mata duk suna ci.
Kayan
Haɗin Tuwon Maiwa
Abubuwan da ake buƙata yayin samar da tuwon maiwa sun haɗa da:
i. Maiwa
ii. Ruwa
Yadda ake samar da tuwon maiwa daidai yake da yadda ake samar da tuwon gero da na dawa. Sai dai akan ba da lokaci sosai
yayin dafa tuwon maiwa, sama da yadda ake bayarwa a tuwon gero da na dawa.
Tsokaci
Tuwon maiwa yana da matsala a wajen yin sa, saboda idan ba a iya ba zai lallace ya ɗanyance a yi asarar abincin. Wannan ya sa mutane da dama ba su
cika yin sa ba. Tuwon maiwar da bai nuna ba na iya sanya mutum ciwon ciki.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.