Tuwon tsaki, wani nau’in tuwo ne da ake yi da tsakin masara. Ma’ana sai an tankaɗe garin masara bayan an daka. Daga nan ne za a yi amfani da tsakin da ya rage a mayar da shi tuwo. Galibi tuwon tsaki abinci ne da mata suka fi ta’ammuli da shi. Baya ga wannan, tuwon tsaki shi ma ba kullum ake yin sa ba, sakamakon sai an yi tuwo kusan biyu ko uku a gida za a tara adadin tsakin da zai isa a tuƙa tuwon na tsaki. Wannan nau’i na tuwo,na daga cikin dabarun mata na yin abincin gaggawa saboda rashin wadataccen lokaci da kuma tattalin kwananniyar miyar da ta yi saura domin gudun ka da a zubar da ita a banza. Haka kuma, idan an rasa abinci a cikin gida, akan ɗauko tsakin da aka aje a tuƙa tuwon da shi a matsayin abincin gaggawa.
Mahaɗin Tuwon Tsaki
Yayin samar da
tuwon tsaki. Akwai abubuwan da ake buƙata kamar haka.
i. Masara ko Dawa ko Gero
ii. Ruwa
Yadda
Ake Tuwon Tsaki
Da farko za a fara
tanadar tsaki. Ana iya yi da tsakin dawa ko gero ko na masara. Idan an samu tsakin ɗaya daga cikin waɗannan da aka ambata, za a tankaɗe don a rage masa garin da ke cikinsa. Daga nan sai a aza
tukunya bisa wuta a zuba ruwa a cikinta, a bar ta nan har sai
ruwan ya tafasa. Sannan za a ɗauko tsaki a wanke shi sosai a regaye. Kada a bari ya jiƙe ƙwarai don cire masa ƙasa
da sauran dusar da ke ciki. Bayan nan, sai a rage ruwan zafi a ajiye gefe ɗaya.
Sai kuma a riƙa ɗibar tsakinan ana barbaɗawa
a hankali a cikin tukunya. Sannan za a saka muciya cikin tukunyar ana tuƙawa har sai ya yi kauri. Sa’anan sai a
rufe tukunya a bar shi ya salale na tsawon wani lokaci. Idan ya ɗan jima, za a buɗe a sake tuƙawa. Da zarar an yi haka, haƙiƙa tuwon tsaki ya haɗu
kenan. Galibi shi tuwon tsaki akan ci shi da
kowace irin miya.
Tsokaci
Yara ƙanana da kuma mata su ne suka fi cin tuwon tsaki. Maza (manya) ba su cika cin wannan nau’i na tuwo ba. Sannan ba a cika ɗaukar wannan nau’in tuwo da ƙima ba. Wasu na ganin kamar ba tuwo ne da za a ci a ƙoshi ba. Wannan na faruwa ne kasancewar sa tuwo mai ruwa-ruwa. Wannan ya sa ake ganin sa abinci ne na yara da mata. An fi samun irin wannan abinci a garuruwan Zariya da Kabi da Zamfara, ba a cika samun irin wannan abinci a garuruwan Kano da Katsina da sauran garuruwa ba. Yana da kyau a riƙa yin tuwon tsaki kasancewar zai taimaka ainun wajen sarrafa abinci da ake ragewa don yin amfani da shi, musamman ga ƙananan yara waɗanda za su iya dawowa daga makaranta ba a gama abinci da wuri ba, tuwan tsaki zai iya tallafarsu kafin a gama abinci. Baya ga haka kuma, tuwon zai taimaka wajen tattalin abincin da ake da shi a gida.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.