Yadda Ake Abincin Hausawa Na Garau-Garau (Wasa-Wasa)

    Gabatarwa

    Abincin garau-garau, abinci ne da za a iya dafa shi ba tare da an tuƙa shi ba, kuma za a iya cin garau-garau haka nan ba tare da miya ba. Sannan akan iya cin sa da wani abu daban ba da miya ba, kamar manja ko mangyaɗa. Garau-garau ba sabon abinci ba ne a ƙasar Hausa, yana cikin nau’in abincin da aka gada tun iyaye da kakanni. Sai dai a yau, akan samu nau’o’in garau-garau da zamani ya zo da su waɗanda suka bambanta da waɗanda aka saba da su.

    Kashe-Kashen Garau-Garau (Wasa-Wasa)

    Kamar yadda nau’o’in abincin da aka lissafo a baya rukunan su ya kasu iri daban-daban, shi ma wannan nau’in abinci za a iya raba shi zuwa wasu rukunai ta hanyar la’akari da kayan haɗi da kuma yadda ake sarrafa shi. Ga wasu daga ciki kamar haka:

    Wasa-Wasar Dawa

    i. Barkono       

    ii. Dawa         

    iii. Gishiri

    iv. Mai             

    v. Ruwa

    Dawa za a surfe sosai, sai a wanke ta sannan a bar ta ta tsane. Idan ta tsane, za a ɗora tukunya saman wuta a zuba ruwa a cikinta. Bayan ruwa ya tafasa sai a ɗauko dawar a zuba a ciki, sannan a sanya gishiri a ci gaba da dafuwa. Idan ta dafu, za a sauƙe tukunyar ta ɗan huce, sai a riƙa ɗiba ana ci da mai da yaji kamar yadda ake cin shinkafa.

    Wasa-Wasar Shinkafa

    i. Barkono       

    ii. Gishir          

    iii. Mai

    iv. Ruwa         

    v. Shinkafa

    Da farko, za a gyara shinkafar a wanke ta, sannan a aza tukunya da ruwa bisa wuta. Bayan ruwan ya tafasa, sai a zuba wannan shinkafar a ciki tare da ɗan gishiri daidai gwargwado. Bayan shinkafar ta dafu akan ci ta da mai da yaji ko kuma da miya idan da hali.

    Wasa-Wasar Gero

    i. Barkono       

    ii. Gero            

    iii. Gishiri

    iv. Mai            

    v. Ruwa

    Yadda ake yin wasa-wasar dawa haka ake ta gero. Bambancin kawai shi ne, a nan ana amfani da gero ne a maimakon dawa.

    Wasa-Wasar Dambu

    i. Mai                           

    ii. Ɓarzazziyar Masara ko Shinkafa

    iii. Ruwa                     

    iv. Yaji

    Akan dafa dambun masara ko na shinkafa haka nan ba tare da an saka masa komai ba. Akan yi wannan dafuwa ne ta hanyar turara shi a madanbaci. Idan an tabbatar da ya yi yadda ake so sai a kwashe shi. Za a iya cin sa da mai da gishiri da Barkono (tonka). Haka kuma, shi ma za a iya saka ganye da ƙuli-ƙuli a yi kwaɗo da shi, kuma za a iya saka masa miya idan ana buƙata a ci da shi.

    Wasa-Wasar Burabusko

    i. Barkono       

    ii. Burabusko (Ɓarzazziyar masara

    iii. Gishsiri

    iv. Mai             

    v. Ruwa

    Shi ma wannan nau’in dambu akan yi shi ne kamar yadda aka yi bayanin sauran da ke sama. Akan yi shi da ɓarzazziyar masara. Bayan ya kammala, akan sanya masa mai da yaji domin a ci. Wani lokaci akan ci da miya.

    Wasa-Wasar Wake

    i. Barkono       

    ii. Gishiri         

    iii. Kanwa

    iv. Mai             

    v. Ruwa          

    vi. Wake

    Ita ma wasa-wasar wake duk lokacin da aka buƙaci yin ta ana wanke waken ne sannan a tsince wanda ba shi da kyau. Idan ruwan da aka ɗora a saman wuta ya tafasa, sai a zuba shi a saka ’yar kanwa da gishiri a ciki, sai kuma a saurara har sai ya dafu sosai. Akan ci da mai da yaji, ko kuma a sanya miya idan da hali.

    Kammalawa

    Nau’in abincin wasa-wasa, abinci ne mai sauƙin dafuwa ba tare da an saka kayayakin lambu a wajen dafuwa ko cinsa ba. Duk da haka, akan samu waɗanda ke amfani da kayan lambun yayin cin wasa-wasa. Mafi yawanci abinci ne da ake cin sa da mai da yaji. Wani lokaci kuwa akan sanya miya, musamman a zamanin yau.

    The book “Cimakar Bahaushe” (Diets of the Hausa People) is a collection of 293 traditional and modern diets of the Hausa people. Detailed explanations of the recipes and ingredients are provided. Comments are provided on the areas of the Hausa land where specific diets are mostly found, the age categories of people that usually use it, as well as the scientific impact of some of the diets to human biology.  Data is collected from interviews with different categories of people including:  i.                    Food sellers within the Hausa land: Mainly to have an idea of recipes on the diets.  ii.                  People of older age: Mainly to have insights on traditional diets of the Hausas.  iii.               Hausa scholars: Mainly to verify and justify the validity of the information obtained as well as provide further expert explanations on the diets.  Moreover, over two hundred (200) pieces of literature were reviewed to have better insight on the topic in question as well as get scientific and professional clarifications on some key concepts relevant to the research. The pieces of literature cover major relevant phenomena such as diet and hunger. Others are on the Hausa land and the Hausas.  The book contains thirty-three (33) chapters. Chapter one is the main introduction in which a concise explanation is provided on the Hausas, their history, their land, social life, and transformations due to globalization, acculturation, and modernity. Chapter two detailly discusses the concepts of diet and food from the Hausa point of view. That includes the meaning and the usage of diets in some Hausa works of literature both verbal and written (i.e. prose, poetry, proverbs, etc.).  Chapters three and four discuss the sources of Hausa diets and their forms accordingly. Chapters five to seventeen discuss some traditional Hausa diets including hard and soft ones. Chapter eighteen concentrates on the influence of modernity and globalization on Hausa diets. It has been discovered that there have been some significant changes in the Hausa diets ranging from recipes to kitchenettes.  Chapters nineteen to thirty-two discuss modern Hausa diets. Some traditional diets are still retained with little modifications, while on the other hand, there are a lot of new ones. Chapter thirty-three discusses “hunger” from the Hausa point of view. The relationship between hunger and food is examined. Additionally, the use of hunger in various Hausa literary works is studied. It is concluded that hunger is like a disease whereby its cure is food.  7th November 2022
    Citation (Manazartar Littafin): Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

    Get a copy:
    To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
    +2348133529736

    You can also write an email to:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.