Gabatarwa
Wannan babi na goma sha ɗaya zai yi bayani ne game da yadda ake yin ɗanwake da tubani. An haɗe su wuri guda ne saboda makusanciyar kamanceceniyar da su ke da ita. Duk da haka, ɗanwake da tubani wasu nau’o’in abinci ne masu zaman kansu.
Yadda Ake Ɗanwake
i. Kanwa
ii. Kuka
iii. Kayan ɗanɗano
iv. Mai
v. Ruwa
vi.
Fulawa ko alabo da wake da dawa
Akwai ɗanwaken da ake yi ta hanyar haɗa wake da dawa da alabo,[1]
amfani da wake da ake
yi a matsayin babban sinadarin haɗi, ana
hasashen shi ne ya sa ake
ce masa ɗanwake. Bayan an haɗa waɗannan kayayyaki, sai a daka a
turmi ko kuma a niƙa su a
dutsen niƙa ko kuma a injin
niƙa (injimin rida). Idan dakawa za a yi, za a iya sanya kuka a daka su tare. Idan kuwa niƙa ne, akan niƙa ne haka nan bisa dutse ba tare da
kuka ba, amma idan
a inji ne akan sanya kukar.
Da zarar an kammala, sai a tankaɗe. Idan haka ta faru, to za a sanya
tankaɗaɗɗen garin kuka bayan an dawo daga niƙa. Daga nan kuma za a kwaɓa wannan gari tare da ruwan jiƙaƙƙiyar
kanwa ba mai yawa ba. Wannan ruwan jiƙaƙƙiyar kanwar, shi zai mayar da kwaɓaɓɓen garin mai danƙo.
A gefe guda kuwa, za a ɗora ruwa bisa wuta. Bayan ya tafasa, za a riƙa ɗiban
wannnan kwaɓaɓɓen garin ɗanwake da hannu ko da cokali ko kuma da wani abu makamancinsa ana sanyawa ƙanana-ƙanana cikin wannan tafasasshen ruwan da ke
bisan wuta. Bayan an saka
daidai adadin da tukunyar za ta iya ɗauka, sai a bar ta haka nan. Ɗanwaken zai riƙa samar da wani kumfa yayin da ruwan
ke tafasa. Za a riƙa amfani da
ludayi da ruwan sanyi kaɗan domin mayar da wannan kumfa da ke
tasowa.
Yadda ake gane ɗanwake ya nuna shi ne, idan aka ɗauka aka sanya cikin ruwan sanyi, zai koma ƙasan ruwan. Wanda bai nuna ba kuwa, zai zauna a saman ruwan. Ana cin ɗan wake da mai da da gishiri da yaji. Wani lokaci ma
akan ci shi da jar miya(miyar da
ake cin shinkafa) ko
miyar gyaɗa.
Yadda Ake Tubani
i. Rogo
ii. Ganyen rogo ko
na masara
iii. Kanwa
iv. Kuka
v.
Wake
A wannan nau’in abinci, za a niƙa
wake ne
ko a daka shi,
sannan a tankaɗe a saka garin kuka kaɗan a kwaɓa da ruwan kanwa. Ganyen rogo ko na masarar da aka samo, ana buƙatar a wanke shi domin ya samu
cikakkiyar tsafta. Idan
ganyen ya bushe, sai a riƙa
zuba wannan kwaɓin da aka yi bisa ganyen ana naɗewa. Bayan an kammala sai maganar sanyawa a cikin tukunyar da aka sanya bisa wuta.
Kammalawa
Ɗanwake da tubani nau’o’in abinci ne sanannu a ƙasar Hausa. Kamar yadda aka bayyana a sama, wake shi ne babban sinadarin haɗin waɗannan nau’o’in abinci. Sai dai zamani ya zo da hanyoyi daban-daban da ake sarrafa su.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.