Masar Gero
Kayan haɗin masar gero:
i. Albasa
ii. Gero
iii.
Kanwa
iv. Mai
v.
Ruwa
Da farko, za a surfe gero a bushe, sai kuma a ɗebi wani adadi na geron a matsayin ƙullu; ragowar za a daka ya yi laushi sosai, sannan a tankaɗe. A gefe guda kuwa, za a sanya ƙullun da aka keɓe a tukunya a aza bisa wuta, a dafa. Bayan ya dafu sosai, za a sauke a bar shi har sai ya yi sanyi. Garin da aka tankaɗe, za a baza shi a ƙwarya. Daga nan ne kuma za a baza wannan dafaffen ƙullun a gauraya.
Da zarar wannan ya samu, za a zuba
gaba ɗaya a turmi sannan a kirɓa tamkar dawo/fura. Ana yanka albasa ciki kafin a fara
kirɓawa. Bayan ya kirɓu tsaf, sai a juye a tukunya ko ƙwarya a rufe. Za a
ajiye shi ya kwana. Yayin da gari ya waye, za a
tarar da ya hau.[1] Za a jiƙa kanwa a gefe
guda, sannan a dama wannan kullu da ruwan kanwar. Da zarar wannan ya samu, sai
batun soyawa a tanda.
Za a hasa (hura)wuta sannan a wanke tanda a ɗora. Za a riƙa sanya mai a gurabun tandar sannan a riƙa zuba ƙullun daidai
gwargwado. Yayin da ɓari guda ta soyu,
sai a juya ta zuwa ɗayan ɓarin sannan a ƙara yaryaɗa mai. Da zarar ta
soyu, masa ta samu ke nan. Ana cin masa da yajin ƙuli ko maɗi ko miya. Wani lokaci kuma akan ci haka ba tare da yajin ƙuli ko miya ba.
Masar Masara
Kayan haɗin masar masara:
i. Albasa
ii. Mai
iii. Masara
iv.
Ruwa
Yayin samar da
masar masara, masara ake
surfewa a bushe. Za a jiƙa wannan masara a bar ta har sai ta kwana, ta jiƙa sosai. Washe gari za a tsame wannan masara a shanyata. Bayan ta
tsane, za a sanya a turmi a daka. Za a rinƙa dakawa ana tankaɗewa tare da fitar da tsaki gefe. Wannan tsaki shi ake dafawa a matsayin ƙullu.
Kamar yadda ake
masar gero (wanda aka yi bayani a 13.1 da ke sama), ana
zuba ƙullun kan garin bayan an sauke ya yi sanyi. Za a yayyanka
albasa ciki sannan a zuba a turmi a kirɓa. Za kuma a rufe
a tukunya ko ƙwarya a
bar shi ya kwana. Da safe za a tarar da ya hau, sai kuma a jiƙa da ruwan kanwa. Ana soya masar masara kamar yadda ake soya ta gero.
Masar Shinkafa
Kayan haɗin masar shinkafa:
i. Albasa
ii. Kanwa
iii. Mai
iv. Ruwa
v. Shinkafa
[1]Kumbura
[2]Ɗanyar shinkafa ita ce wacce ba a
turara/guma ta ba kafin a sussuke.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.