Yadda Ake Miyar Egushi

    Egushi yana daga cikin ’ya’yan itace da Hausawa suka samu a yankin kudancin ƙasar nan. Saboda haka ne ma, egushi bai yawaita sosai a ƙasar Hausa ba. Sannan yawanci ba Hausawa ne ke sayar da shi a ƙasar Hausa ba. A dalilin haka, miyar egushi ba ta yawaita a ƙasar Hausa ba.

    Mahaɗin Miyar Egushi

    Kayan haɗin miyar egushi sun haɗa da:

    i. Albasa                      

    ii. Egushi                    

    iii. gishiri

    iv. Kayan ciki ko nama ko kifi (idan akwai)  

    v. Kayan yaji

    vi. Kori                        

    vii. Magi                      

    viii. Manja ko mangyaɗa

    ix. Ruwa[1]                    

    x. Tafarnuwa              

    xi. Tarugu

    xii. Tattasai                 

    xiii. Thyme                 

     xiv. Tumatur

    Yadda Ake Miyar Egushi

    Da farko za a wanke kayan ciki (idan za a yi amfani da su). Za a sanya musu nau’o’in kayan ɗanɗano sannan a bar shi har sai ya tsane. Daga nan, za a jajjaga tarugu da tattasai kar a saka tattasai ya yi yawa sosai. Sannan za a saka ɗan tumatur kaɗan shi ma a jajjaga sama-sama sai a saka ’yar kanwa kaɗan a ciki a aje. Bayan nan, za a soya mai tare da albasa a soya jajjaagen. Bayan sun soyu, za a saka kayan yaji dangin su citta da kanamfari.

    Bayan wannan ya samu, za a yi sanwa a saka magi da gishiri kaɗan. A wannan gaɓa ne kuma za a sanya kayan cikin da aka tanada. Daga nan za a ɗauko agushi a fece shi tare da cire dattin da ke tare da shi a kuma daka. Bayan an kammala daka, sai a kwaɓa shi. Idan a na buƙata ana iya saka karas a cikin. Sai dai dole sai an goge karas an yanka kafin a sanya. Bayan haka, akan sanya koren tattasai.

    Tsokaci 

    Wannan nau’in miya an fi samun ta a gidajen masu hannu da shuni. Sannan an fi yin miyar a cikin birane sama da ƙauyuka. Hasali ma, ba kasafai ake samun egusi a kasuwannin ƙauyuka ba.



    [1] Idan an lura, akwai nau’in kayan ɗanɗano na musamman da ake amfani da su yayin samar da wannan miyar.

    The book “Cimakar Bahaushe” (Diets of the Hausa People) is a collection of 293 traditional and modern diets of the Hausa people. Detailed explanations of the recipes and ingredients are provided. Comments are provided on the areas of the Hausa land where specific diets are mostly found, the age categories of people that usually use it, as well as the scientific impact of some of the diets to human biology.  Data is collected from interviews with different categories of people including:  i.                    Food sellers within the Hausa land: Mainly to have an idea of recipes on the diets.  ii.                  People of older age: Mainly to have insights on traditional diets of the Hausas.  iii.               Hausa scholars: Mainly to verify and justify the validity of the information obtained as well as provide further expert explanations on the diets.  Moreover, over two hundred (200) pieces of literature were reviewed to have better insight on the topic in question as well as get scientific and professional clarifications on some key concepts relevant to the research. The pieces of literature cover major relevant phenomena such as diet and hunger. Others are on the Hausa land and the Hausas.  The book contains thirty-three (33) chapters. Chapter one is the main introduction in which a concise explanation is provided on the Hausas, their history, their land, social life, and transformations due to globalization, acculturation, and modernity. Chapter two detailly discusses the concepts of diet and food from the Hausa point of view. That includes the meaning and the usage of diets in some Hausa works of literature both verbal and written (i.e. prose, poetry, proverbs, etc.).  Chapters three and four discuss the sources of Hausa diets and their forms accordingly. Chapters five to seventeen discuss some traditional Hausa diets including hard and soft ones. Chapter eighteen concentrates on the influence of modernity and globalization on Hausa diets. It has been discovered that there have been some significant changes in the Hausa diets ranging from recipes to kitchenettes.  Chapters nineteen to thirty-two discuss modern Hausa diets. Some traditional diets are still retained with little modifications, while on the other hand, there are a lot of new ones. Chapter thirty-three discusses “hunger” from the Hausa point of view. The relationship between hunger and food is examined. Additionally, the use of hunger in various Hausa literary works is studied. It is concluded that hunger is like a disease whereby its cure is food.  7th November 2022
    Citation (Manazartar Littafin): Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

    Get a copy:
    To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
    +2348133529736

    You can also write an email to:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.