Ganyen Ka-fi-likita ganye ne da ake samu a wasu garuruwa na ƙasar Hausa. Ba a kowane gari ake samun sa ba. Ana kiran sa da ka-fi-likita ne saboda yana maganin cututtuka da yawa na jikin ɗan Adam. Gane hakan ne ya sa wannan miyar ke ƙara yawaita tsakanin Hausawa.
Mahaɗin
Miyar Ka-fi-likita
Akwai abubuwan da za a tanada idan za
a haɗa miyar ka-fi-likita.
i. Albasa
ii. Daddawa
iii. Gishiri
iv.
Ka-fi-likita
v. Kayan yaji
vi. Magi
vii. Mai
viii. Ruwa
ix. Tarugu
x. Tattasai
Yaddda
Ake Miyar Ka-fi-likita
Ana sarrafa wannan miyar ne tamkar yadda ake samar da miyar alayyafu.
Bambancin kawai shi ne, bayan sanya ta tafasa, a maimakon a sanya alayyafu, sai
a saka ganyen ka-fi-likita. Shi ma wannan ganye akan wanke shi da gishiri sannan a yanka kafin a zuba shi
cikin sanwa. Akan yi amfani da wannan miyar yayin cin kusan kowane irin nau’in
tuwo, tun daga tuwon shinkafa da semo da tuwon masara da dai sauransu.
Tsokaci
Amfani da wannan miyar na ƙara yawaita birni da ƙauye. A yanzu haka, akan samu wannan bishiya a cikin gidajen Hausawa. Shukarsa na da sauƙi, domin karyar sa kawai ake yi sannan a dasa tamkar shuwaka ko lalle. Wato ba sai an nemi ’ya’yansa ba yayin da aka buƙaci shukawa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.