Kabeji, nau’in ganye ne daga cikin ganyayen da Bahaushe ke amfani da shi. Yana kama da ganyen salat, sai dai shi yana dunƙulewa ne sannan ya fi ganyen salat ƙarfi. Za a iya hasashen cewa, kabeji ba asalin ganyen Bahaushe ba ne. Ya samu ne sakamakon cuɗanyarsa da baƙin al’ummu. Ko bayan miya, akan sarrafa kabeji a matsayin abinci ko mahaɗin abinci daban-daban.
Mahaɗin
Miyar Kabeji
Akwai abubuwan da ake tanada yayin
samar da miyar kabeji. Waɗannan abubuwa sun haɗa
da:
i. Albasa
ii. Gishiri
iii. Kabeji
iv. Karas
v. Kayan miya
vi. Nama
vii. Ruwa
viii. Thyme
Yadda
Ake Miyar Kabeji
Za a samu kabeji mai kyau na iya adadin da ake buƙata na miyar. Daga nan za a yanka
albasa wada ba ta da lawashi, za a yi yankan ne kamar ƙwallo. Haka ma za a yanka kayan miya a aje gefe guda. Daga nan sai batun ɗora tukunya da zuba mai tare da soya nama, wanda bayan nan
ne za a sanya kayan miya tare da kayan ɗanɗano
da na ƙamshi, a kuma
rufe tukunyar. Bayan sanwa ta tafasa, sai a kawo kabejin da aka yanka aka wanke domin a sanya
ciki tare da karas wanda shi ma aka yayyanka. Akan ci wannan miya da shinkafa ko kuskus ko kafa da ma
sakwara da makamantansu.
Tsokaci
Akasari ba ko’ina ake miyar kabeji ba.
Kusan za a iya cewa, an fi
yin ta a cikin birane,
ko a cikin biranen ma, ɗaiɗaikun gidaje ne ake samun ta.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.