Kayan haɗin miyar sure.
i. Albasa
ii. Daddawa
iii. Gishiri
iv. Kanyan yaji
v. Magi
vi. Mai
vii. Ruwa
viii. Tafarnuwa
ix. Tarugu
x. Tattasai
xi. Wake
Yadda
Ake Miyar Sure
Bambancin kayan haɗin da ake amfani da su a zamanance, shi ya samar da bambance-bambance tsakanin yadda ake miyar sure ta gargajiya da ta zamani. A zamanance, za a samu wake mai ɗan dama, gwargwadon yawan miyar da ake son yi. Za a surfa wannan wake sannan a wanke, a kuma cire hanci da ɓawon. A gefe guda kuma, za a tanadi kayan yaji a dake su tsaf. Baya ga haka, za a yi markaɗe ko jajjagen kayan miya, nau’o’in da aka lissafo a sama.
Yayin da kayan haɗi suka kammala, sai batun ɗora
tukunya bisa wuta. Cikin tukunyar nan za a sanya mai,
tare da albasa. Da zarar ya soyu, sai kuma a sanya
kayan miyan da aka tanada (markaɗe ko jajjage). Haka za a bar wannan kayan miya har sai sun soyu sarai, sai kuma a sanya kayan
yaji da aka tanada, ciki har da dakakkiyar daddawa. Daga nan sai a ɗan motsa shi na kimanin mintuna uku zuwa sama da haka,
har dai sai daddawar da aka sanya ta haɗe. Daga nan sai batun zuba ruwa,
gwargwadon yawan miyan da ake son samarwa.
Bayan an zuba ruwa, za a sanya kayan ɗanɗano nau’in magi da gishiri (ko dai
nau’in da aka fi amfani da shi a gida). Daga nan za a bar wannan tukunya ta yi ta tafasa. Idan miyar da nama za a yi,
to a wannan gaɓa ne za a sanya nama (da ma dai an
riga an tafasa nama an ajiye a gefe). Haka ma idan kifi ne, a wannan gaɓa za a sanya (yayin da za a yi amfani da ɗanyen kifi, to ya kamata a tafasa shi kaɗan tare da gishiri kafin a fara miyar).
Abu na gaba shi ne, sanya sure cikin miya. Za a ɗauko
suren da aka yanka aka
wanke tare da kanwa (domin a rage mata tsami) a sanya cikin tukunya. Haka ma idan dakakken sure ne
(busasshe) to za a barbaɗa shi tare da kaɗawa.
Bayan an sanya sure, za a rufe tukunya ta ɗauki kimanin mintuna talatin ko ma
sama da haka. Ana son ta ɗauki lokaci mai tsawo domin ta sami dahuwa mai kyau. Akwai wadda
ake barinta bisa wuta har na tsawon awa guda. Da zarar an kammala
wannan, to kuwa an samu miyar sure.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.