Yadda Ake Miyar Tumatur

Tumatur shi ma yana ɗaya daga cikin ’ya’yan itatuwa da ake amfani da su tun lokaci mai tsawo kusan birni da ƙauye. Shi ma yaɗo yake yi, sai dai yana da ɗiya ne madaidaita. Launin ɗiyan kore ne kafin su nuna, amma sukan koma jajaye bayan sun nuna. Akan yi amfani da tumatur a matsayin kayan miya a mafi yawan nau’o’in miyoyi a ƙasar Hausa (kamar yadda aka yi bayani a sama). Sai dai a miyar tumatur, shi tumatur ɗin ne ya kasance babban abin haɗi. Ma’ana dai akan sanya adadin tumatur mai yawa.

Mahaɗin Miyar Tumatur

Yayin samar da miyar tumatur, ana buƙatar kayan haɗi kamar haka:

i. Albasa                     

ii. Gishiri                     

iii. Kanwa/bakin foda

iv. Kayan yaji             

v. Kori                         

vi. Lawashi

vii. Magi                      

viii. Mai                       

ix. Nama ko kaza

x. Ruwa                      

xi. Tarugu                  

xii. Tattasai                 

xiii. Tumatur

Yadda Ake Miyar Tumatur 

Za a tafasa nama (idan akwai) tare da kori (da sauran kayan ƙamshi irin waɗannan) da ɗan gishiri, a sauke in ya ya nuna. Daga nan sai a niƙa tumatur da tattasai da tarugu da albasa. Kar a saka tarugu da yawa a wurin niƙa. Haka kuma, kar a niƙa tumatur luƙui-luƙui, a maimakon haka, za niƙa shi ne tsaka-tsaki. Yayin kai markaɗen yana da kyau a sanya ’yar kanwa ko bakin foda.

Bayan an dawo da shi daga markaɗe, za a aza bisa wuta domin ya tsane. Daga nan kuma sai maganar soyawa tare da kayan yaji. A lokacin saka kayan yaji, kada a saka su da sauri. A maimakon haka, a bari sai tumatur ya fitar da wata kumfa ɗorowa ita ake kira (yami). Daga nan ne za a zuba kayan yaji. Idan aka yi haka, to an fi jin ƙamshin miyar sosai. A lokacin da jajjagen ya soyu, za a sake kwashe nama daga cikin ruwa a haɗe da tumatur a ci gaba da soya su tare. Idan tumatur ya ƙara soyuwa za a yi sanwa da ruwan nama a saka magi. A lokacin za a yanka lawashin albasa wanda da ma an riga an wanke shi, a saka ciki. Idan miyar ta dafu ta yi kauri sosai, za a iya saukar da tukunya. Akan ci nau’o’in tuwo daban-daban da wannan miyar. Daga cikin nau’o’in tuwon da ake ci da ita sun haɗa da tuwon masara, da taiba da tuwon shinkafa da sakwara da semo da makamantansu.

Tsokaci

Kusan za a iya cewa, babu wani ɓangare daga ƙasar Hausa da ba a amfani da miyar tumatur. Za kuma a iya hasashen cewa, an fi samun irin wannan nau’in miya a bira ne, duk kuwa da yake ƙauyukan sun fi birane yawaitar tumatur. 

The book “Cimakar Bahaushe” (Diets of the Hausa People) is a collection of 293 traditional and modern diets of the Hausa people. Detailed explanations of the recipes and ingredients are provided. Comments are provided on the areas of the Hausa land where specific diets are mostly found, the age categories of people that usually use it, as well as the scientific impact of some of the diets to human biology.  Data is collected from interviews with different categories of people including:  i.                    Food sellers within the Hausa land: Mainly to have an idea of recipes on the diets.  ii.                  People of older age: Mainly to have insights on traditional diets of the Hausas.  iii.               Hausa scholars: Mainly to verify and justify the validity of the information obtained as well as provide further expert explanations on the diets.  Moreover, over two hundred (200) pieces of literature were reviewed to have better insight on the topic in question as well as get scientific and professional clarifications on some key concepts relevant to the research. The pieces of literature cover major relevant phenomena such as diet and hunger. Others are on the Hausa land and the Hausas.  The book contains thirty-three (33) chapters. Chapter one is the main introduction in which a concise explanation is provided on the Hausas, their history, their land, social life, and transformations due to globalization, acculturation, and modernity. Chapter two detailly discusses the concepts of diet and food from the Hausa point of view. That includes the meaning and the usage of diets in some Hausa works of literature both verbal and written (i.e. prose, poetry, proverbs, etc.).  Chapters three and four discuss the sources of Hausa diets and their forms accordingly. Chapters five to seventeen discuss some traditional Hausa diets including hard and soft ones. Chapter eighteen concentrates on the influence of modernity and globalization on Hausa diets. It has been discovered that there have been some significant changes in the Hausa diets ranging from recipes to kitchenettes.  Chapters nineteen to thirty-two discuss modern Hausa diets. Some traditional diets are still retained with little modifications, while on the other hand, there are a lot of new ones. Chapter thirty-three discusses “hunger” from the Hausa point of view. The relationship between hunger and food is examined. Additionally, the use of hunger in various Hausa literary works is studied. It is concluded that hunger is like a disease whereby its cure is food.  7th November 2022
Citation (Manazartar Littafin): Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments