Miyar kwata miya ce da ke ɗaya daga cikin miyar Hausawa. Daɗaɗɗiya ce, wadda suka gada tun kaka da kakani. Kwata nau’in dutse ne daga cikin duwatsun da Allah ya halitta a doron ƙasa. Yana da laushin da ke ba da damar a niƙa shi ta hanyar amfani da dutsen niƙa. Akan yi amfani da wannan niƙaƙƙen garin kwata domin miya. An fi samun wannan nau’in miya a garuruwan Kabi da Zamfara da Sakkwato. Ba a cika samun ta a garuruwan Katsina da Kano da Kaduna da Bauchi ba. Al’ummun ƙauyuka ne suka fi amfani da wannan nau’in miya, sai kuma tsofaffi da ke zaune a cikin birane.
Mahaɗin Miyar Kwata
Kayan
haɗin da ake buƙata yayin samar da miyar kwata sun
haɗa da:
i. Barkwano
ii. Daddawa
iii. Kayan yaji
iv. Kwata
v. Ruwa
Yadda Ake Miyar Kwata
Ita miyar kwata ana yin ta ne ba da mai ba. Ma’ana dai, kwata
na iya kasancewa a matsayin mai, saboda maiƙon da take
da shi. Yayin da za a yi miyar kwata, za a aza sanwa tamkar dai yadda aka yi
bayani a nau’o’in miyoyin
da aka bayyana a baya.
Bayan sanwa ta daɗe da tafasa, sai a sanya kwata.
Yayin da wannan miya ta dahu, za a tarar tana da maiƙo, sannan za ta yi jawur. Akwai
lokutan da akan sanya kwata ga miyar sure ko miyar soɓorodo.
Tsokaci
Tun shekaru aru-aru ake amfani da kwata a matsayin mahaɗin
miya. Sai dai a yau, an rage amfani da
wannan nau’in miya ƙwarai da gaske. Wannan bai rasa nasaba da ci gaba da ake
samu a yanzu dangane da abincin Hausawa. Duk da haka, ana samun kwata a cikin kasuwannin
Hausawa kuma ana sayarwa ga
wasu ɗaiɗaikun
mutane da ke zaune a cikin ƙauyuka
da suke da tazara da birane.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.