Yadda Ake Sarrafa Nama (Soyayyen Nama, Tsire, Dambun Nama, Nama Da Karas, Nama Da Kabeji)

    Gabatarwa

    Babi na goma sha hu É— u (14) an gina shi ne sukutum kan bayanin nama da yadda ake sarrafa shi a Æ™ asar Hausa . Kamar dai sauran nau’ukan abinci, yadda ake sarrafa nama a gargajiyance ba shi da wani bambanci mai tazara tsakaninsa da yadda ake sarrafa shi a zamanance. Bambancin ya fi shafar kayan ha É— i da kuma kayayyakin amfanin gida da ake amfani da su a lokacin aikin sarrafawar. Misali , yadda ake farfesun nama a gargajiyance, haka ake yi a zamanance. Kodayake, kayan ha É— in sun É— an bambanta. Zamani ya zo da nau’ukan kayan É— an É— ano da na Æ™ amshi wa É— anda babu su a tsarin gargajiya. Za a iya lura cewa, a wannan  babi an tsallake wasu daga cikin nau’o’in dabarun sarrafa nama da ake da su na gargajiya. An yi hakan ne saboda ba su da bambancin a-zo-a-gani tsakaninsu da na zamani.

    Soyayyen Nama

    a. Albasa

    b. Gishiri

    c. Kayan yaji

    d. Magi

    e. Mai

    f. Nama

    g. Ruwa

    h. Tafarnuwa

    i. Tarugu

    j. Tattasai

    A yayin samar da soyayyen nama, za a tafasa naman bayan an wanke . Yayin wannan  tafasawar, za a sanya kayan yaji tare da albasa . A Æ™ a’ida, ba za a sanya ruwa da yawa ba, za dai a sa shi ne daidai gwargado yadda naman zai iya shanyewa. Bayan an tafasa shi, sai a soya shi sama-sama.

    A gefe guda kuwa, za a jajjaga tarugu da tattasai da albasa  sannan a sanya sauran kayan Æ™amshi da na É—anÉ—ado da ba a a sanya ba. Daga nan za a É—an soya su sama-sama. Sai kuma a haÉ—e su da wannan  nama da aka soya. Bayan an haÉ—a, za a iya Æ™ara soya su tare ko kuma a ma bar su haka nan.

    Tsiren Nama  Cikin Tukunya

    i. Albasa

    ii. Attarugu

    iii. Gishiri

    iv. Kori

    v. Magi

    vi. Mai

    vii. Nama

    viii. Ƙuli-ƙuli

    ix. Ruwa

    x. Tumatur

    Za a wanke  naman, sannan a tafasa shi kamar dai yadda aka yi bayani a sama (haÉ—e da kayan É—anÉ—ano da na Æ™amshi). Daga nan sai a jajjaga tarugu da tattasai a soya sama-sama. Sai kuma a daka Æ™arago/Æ™uli tare da kori a zuba saman naman. Wannan dakakken Æ™arago za a zuba kan naman sannan a soye su tare.

    Tsiren Nama

    i. Albasa

    ii. Citta

    iii. Koren tattasai

    iv. Kori

    v. Magi

    vi. Nama

    vii. Ƙwai

    viii. Ruwa

    ix. Tafarnuwa

    x. Tarugu

    xi. Tumatur

    A nan kuma, za a yi maganar tsire nau’i biyu. Nau’i na farko, bayan an wanke  naman za a tafasa shi da magi da albasa . Bayan ya tafasa, sai a É—auko tattasai da tarugu da albasa waÉ—anda aka yanka Æ™anana-Æ™anana a haÉ—e wuri guda. Za a kawo tsinkaye a riÆ™a sossoka wannan  nama da kuma kayan lambu da aka yayyanka. Za su kasance a jere reras. Daga nan sai a barbaÉ—a  musu kayan yajin da aka tanada.

    Nau’in tsire na biyu kuwa, ya bambanta da wannan  nau’i na farko. Yawanci mahauta ne suka fi yin sa. Kuma  irinsa ne ake sayarwa ko’ina kan hanya. Wannan nau’i na tsire ba ya buÆ™atar a tafasa shi. Za a yanka naman ne Æ™anana sannan lafe-lafe. Sai a sanya su da yajin Æ™arago, daga nan sai a jera su jikin tsinke. Za a caccaka waÉ—annan tsinkaye a gewaye da wutan da aka tanada. Yawanci akan yi hakan ne bisa abin da ake kira tukubar tsire. Za a riÆ™a juya su lokaci zuwa lokaci har sai kowane É“ angare a jikinsu ya gasu.

    Tsinken Nama

    a. Albasa

    b. Dankalin turawa

    c. Gishiri

    d. Magi

    e. Mai

    f. Nama

    g. Ruwa

    h. Thyme

    i. Tumatur

    Za a wanke  nama a yi masa yankan Æ™wallo (wato Æ™walolo-Æ™walolo) sannan a sulala. A gefe guda kuwa za a yanka dankalin Turawa shi ma yankan Æ™wallo, sai a sulala. Sannan sai a yanka albasa  da tumatur. Za a haÉ—e naman da aka sulala da dankali wuri guda, sannan a sanya kayan Æ™amshi da kayan yaji, sai kuma a riÆ™a sokawa a tsinke. Misalin yadda ake sokawa kuwa, idan an saka nama yanka guda, sai a sanya dankali, sai tumatur da kuma albasa. Bayan an kammala, sai a sanya cikin mai domin suya.

    Dambun Nama

    i. Albasa

    ii. Attarugu

    iii. Gishiri

    iv. Kayan ƙamshi

    v. Magi

    vi. Nama

    vii. Ruwa

    Za a tafasa nama da kayan Æ™amshi da kuma kayan É—anÉ—ano tare da ruwa kaÉ—an. Idan naman yana da yawa, ba a fiye Æ™ara ruwa ko kaÉ—an ba, domin É—an sauran ruwan da aka wanke  naman da shi ya isa ya tafasa shi. Akan sanya albasa  a ciki domin Æ™ara masa Æ™amshi da kuma kawar da Æ™arnin da ke tattare da shi.

    Da zarar naman ya tafasa yadda ake buÆ™ata, sai a jajjaga tarugu da albasa  a soya sama-sama. Naman kuwa da aka tafasa, za a sanya shi cikin turmi  a É—an daddaka har sai ya É—an fara watsewa. Akan iya saka shi a bilander a maimakon turmi. Daga nan za a haÉ—e naman da jajjagen kayan miyar da aka yi, sannan a sanya cikin tukunya , a É—an Æ™ara mai kaÉ—an a ci gaba da juyawa. Haka za a ci gaba da yi har sai ya nuna sarai.

    Nama  da Karas

    i. Alayyafu

    ii. Albasa

    iii. Gishiri

    iv. Karas

    v. Kayan Yaji

    vi. Magi

    vii. Mai

    viii. Nama

    ix. Ruwa.

    x. Tafarnuwa

    Za a wanke  nama a tafasa tare da albasa  da kayan É—anÉ—ano. Gefe guda kuwa za a goge karas. Daga nan sai a É—auko wannan  tafasasshen nama a sanya a tukunya  tare da mai kaÉ—an domin suya irin ta dambu. Ana cikin wanan suya ne za a sanya tanadajjen karas É— in da aka yanka tare da wannan alayyafun da aka yanka Æ™ anana, za kuma a sanya kayan yaji a ciki.

    Kabeji Da Nama

    i. Albasa

    ii. Dankali

    iii. Gishiri

    iv. Kabeji

    v. Karas

    vi. Kori

    vii. Magi

    viii. Mai

    ix. Nama

    x. Ƙwai

    xi. Ruwa

    Za a yanka kabeji manya-manyan yanka, sai a sanya shi a cikin tukunyar da ke bisan wuta  domin ya yi tafasa guda. A gefe guda kuma, za a yanka karas da dankali Æ™ananan yanka, sai a soya su sama-sama cikin mai. Daga nan sai a tafasa nama tare da kayan É—anÉ—ano. Za a yayyanka wannan  tafasasshen nama Æ™anana-Æ™anana sannan a soya shi a ajiye gefe guda. Daga nan za a kaÉ—a Æ™wai cikin wata roba ko kwano sannan a haÉ—e naman da kabeji da kuma karas. Za a zuba zuba su cikin mai a soya gaba É—aya.

    Kammalawa

    Ha Æ™ i Æ™ a , Ubangiji Y a wadata É— an Adam da nau’o’in nama iri-iri. Wannan babin ya kawo wasu nau’o’i ne k a É— an daga cikin wa É— anda ake da su. Sai dai za a iya ha sa shen cewa, hanyoyin sarrafa nama a Æ™ asar Hausa  ba su wuce wa É— anda aka bayyana a sama ba. Sai dai akan samu wasu ‘yan bambance-bambancen da ba za a rasa ba. 

    Citation (Manazartar Littafin):  Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

    Get a copy:
    To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
    +2348133529736

    You can also write an email to:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.