Abubuwan da za a tanada yayin dafa tuwon masara su ne:
i. Masara
ii. Ruwa
iii. Rogo
Wannan nau’i ne na tuwo mai kama da tuwon dawa da na gero. Sai dai a nan, ana amfani ne da masara a maimakon dawa ko geron. Za a gyara masarar sannan a surfe ta a daka. Wani lokaci ana jiƙa masarar ba tare da an surfa ba. Bayan ta jiƙu sai a kai ta niƙa haka nan. Akan iya samin lokutan da ake kai masara niƙa ba tare da an surfa ko kuma an jiƙa ba.
Bayan an dawo da garin masara, za a tankaɗe. A gefe guda kuwa za a ɗora
tukunya saman wuta. Bayan ruwan nan ya yi zafi, za a yi talge kamar dai yada aka yi
bayanin talge a nau’o’in tuwon da ke sama. Ana iya yin wannan talge da tsaki ko gari. Masu buƙata na iya jefa kanwa cikin talgen.
Bayan talgen
ya nuna, sai maganar tuƙawa.
Tsokaci
Za a iya cewa tuwon masara ya game ko’ina a ƙasar Hausa. Kusan babu wani wuri, birni ko ƙauye da ba a cin tuwon masara. Ana cin sa da nau’o’in miya daban-daban, tun daga kan kuka da ma sauran
nau’o’in miyoyi na ganye da Bahaushe ke da su.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.