Kayan haɗin tuwon shikafa su ne:
i. Man Gyaɗa
ii. Ruwa
iii. Shinkafa
Tuwon shinkafa ya ɗan bambanta da sauran nau’o’in tuwo da aka yi bayani a sama. Domin ita shinkafa ba niƙanta ake kaiwa ba. Sannan ba a surfe shinkafa kamar sauran nau’o’in hatsi. Yayin samar da tuwon shinkafa, ana gyara shinkafar ne kawai. Wato dai za a tsince ta sannan a wanke. Akwai nau’in shinkafar da ake kira shinkafar tuwo. Ita ce kuma ake kira Bahaushiyar shinkafa ko shinkafar Hausa. An fi amfani da wannan shinkafa yayin samar da tuwon shinkafa. Sai dai ana iya yin amafani shinkafar da ba nau’inta ba ma yayin yin tuwon.
A gefe guda kuma, za a ɗora
tukunya tare da ruwa kan wuta. Bayan ruwan ya tafasa, za a rage kaɗan sannan a kawo wannan shinkafa a zuba ciki. Daga nan za a rufe
tukunyar a bar ta tai ta dafuwa har sai ta yi laushi sosai, ta narke. Daga nan
za a sanya muciya a fara tuƙawa.
Yayin da ake wannan tuƙi,
idan aka lura tana buƙatar
a ƙara mata ruwa, za a yi amfani da
wannan ruwan da aka rage domin a ƙara.
Bayan ta tuƙu za a rufe
domin ya ƙara sulala. Bayan ya sulala za a sake tuƙawa. Daga nan kuwa sai maganar
kwashewa.
Tsokaci
Wannan nau’i ne na abinci da bai taƙaita ga dare ba kawai. Wato dai koma
bayan sauran nau’o’in tuwo da aka fi yi da dare domin a ci (a kuma ci ɗumame da safe), shi wannan tuwo har abincin rana ana yi da shi. Shi ma
wannan nau’in tuwo ana cin sa da nau’o’in miya da dama, har ma da miyar kuka.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.