Yadda Ake Yin Faten Dankalin Hausa Da Faten Kabewa

    Gabatarwa

    Fate, abinci ne mai sauÆ™i wanda ke É—aya daga cikin nau’o’in abincin Hausawa.Ana hasashen an raÉ—a masa wannan suna ne saboda yin sa ruwa-ruwa da ake yi. Saboda idan an zuba shi a wuri zai iya malale ko’ina, ba ya tsayawa wuri guda saboda ruwan da ke cikinsa. Hausawa na da tatsuniyar kacici-kacici dangane da fate, inda suke cewa: “Kogina ya kai ya kawo sai ta gefe-gefe nake wanka.” Akwai waÉ—anda ba su É—auki fate a matsayin abincin da za a ci a Æ™oshi ba, sai dai a matsayin abincin sauya É—anÉ—ano kawai, ma’ana sauyi daga abincin da aka daÉ—e ana ci yau da kullum.

    Kashe-Kashen Fate

    Fate ya kasu kashi-kashi, duba da nau’o’in kayan haÉ—in da aka yi faten da su, ko kuma hanyoyin da aka bi domin sarrafa su. A Æ™asa an kawo jerin wasu daga cikin nau’o’in fate kamar yadda ake samun su a wurare mabambanta a Æ™asar Hausa:

    Faten Dankalin Hausa

    Kayan haÉ—in faten dankalin Hausa:

    i. Albasa          

    ii. Dankali                  

    iii. Gishiri                    

    iv. Kayan yaji

    v. Mai              

    vi. Ruwa                    

    vii. Tafarnuwa            

    viii. Tarugu    

    ix. Tattasai      

    x. Tumatur                  

    xi. Zogale

    Za a fere dankalin na Hausa, sai a saka shi a cikin ruwa don kar ya bushe. Za a jajjaga tattasai da attarugu da albasa da tumatur da tafarnuwa a saka a tukunya a soya da mai. Idan ya soyu za a zuba ruwa kaÉ—an a saka magi da kayan Æ™anshi a juye dankalin a ciki. Bayan ya kusa dafuwa sai a watsa zogale da kifi a rufe. Idan ya dafu za a É—auko muciya a saka ana daddagawa har sai ya haÉ—e ko’ina. Za a bar shi da É—an ruwa-ruwa domin ya fi daÉ—in ci.

    Faten Kabewa

    Kayan haÉ—in faten kabewa:

    i. Alayyafu      

    ii. Gishiri         

    iii. Kabewa     

    iv. Kayan miya

    v. Mai             

    vi. Nama         

    vii. Ruwa

    A tafasa nama da kayan Æ™anshi, idan ya dafu a sauke a aje gefe guda. Daga nan za a jajjaga tattasai da tumatur da albasa da tarugu a sa mai a tukunya a soya kayan su soyu. Sanan a zuba ruwa tare da tafasasshen nama da sauran ruwan nama, idan ya tafasa, sai a yanka kabewar kamar yadda ake yankan dankali, a wanke a zuba a ciki. Idan kabewa ta nuna za a yanka alayyafu a zuba a ciki, za a rage wuta sosai har ya dafu da É—an ruwa-ruwansa.

    Tsokaci

    Fate wani nau’i ne na abinci daga cikin nau’o’in abincin Hausawa mai mutuÆ™ar muhimmanci. Wannan ya sa suka É—auke shi É—aya daga cikin abincin da ake yi musamman da rana. Baya ga wannan, abinci ne mai sauÆ™in aiwatarwa da bai cika É—aukar lokaci ba yayin dafa shi ; sannan ya kasance abin marmari ga mutane da dama. Wannan ya nuna Hausawa suna da dabaru a É“angaren sarrafa abincinsu na gargajiya har da na zamani. 

    The book “Cimakar Bahaushe” (Diets of the Hausa People) is a collection of 293 traditional and modern diets of the Hausa people. Detailed explanations of the recipes and ingredients are provided. Comments are provided on the areas of the Hausa land where specific diets are mostly found, the age categories of people that usually use it, as well as the scientific impact of some of the diets to human biology.  Data is collected from interviews with different categories of people including:  i.                    Food sellers within the Hausa land: Mainly to have an idea of recipes on the diets.  ii.                  People of older age: Mainly to have insights on traditional diets of the Hausas.  iii.               Hausa scholars: Mainly to verify and justify the validity of the information obtained as well as provide further expert explanations on the diets.  Moreover, over two hundred (200) pieces of literature were reviewed to have better insight on the topic in question as well as get scientific and professional clarifications on some key concepts relevant to the research. The pieces of literature cover major relevant phenomena such as diet and hunger. Others are on the Hausa land and the Hausas.  The book contains thirty-three (33) chapters. Chapter one is the main introduction in which a concise explanation is provided on the Hausas, their history, their land, social life, and transformations due to globalization, acculturation, and modernity. Chapter two detailly discusses the concepts of diet and food from the Hausa point of view. That includes the meaning and the usage of diets in some Hausa works of literature both verbal and written (i.e. prose, poetry, proverbs, etc.).  Chapters three and four discuss the sources of Hausa diets and their forms accordingly. Chapters five to seventeen discuss some traditional Hausa diets including hard and soft ones. Chapter eighteen concentrates on the influence of modernity and globalization on Hausa diets. It has been discovered that there have been some significant changes in the Hausa diets ranging from recipes to kitchenettes.  Chapters nineteen to thirty-two discuss modern Hausa diets. Some traditional diets are still retained with little modifications, while on the other hand, there are a lot of new ones. Chapter thirty-three discusses “hunger” from the Hausa point of view. The relationship between hunger and food is examined. Additionally, the use of hunger in various Hausa literary works is studied. It is concluded that hunger is like a disease whereby its cure is food.  7th November 2022
    Citation (Manazartar Littafin): Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

    Get a copy:
    To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
    +2348133529736

    You can also write an email to:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.