𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Ya salaf suka kasance suna shiri
domin fuskantar watan Ramadan Mai Albarka. Menene koyarwarsu, da matafiyarsu akan
hakan? Kuma ya shauqin su yake ga wañnan wata??
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Dabi'ar magabata Kamar yadda yake
a rubuce a cikin littafai' Wanda aka ruwaito da sanadinsu daga amintattu: cewa
lallai su sun kasance suna rokon Allah Mai girma da ɗaukaka da yakaisu wañnan wata (Ramadan)
kafin isowarsa. Domin abunda suka sani dangane dashi na Alkhairi da daraja dake
cikinsa. Sannan bayan shigar watan: suna rokon Allah ya taimake su akan ayyukan
Alkhairi, bayan Kuma Ramadan ya fita suna rokon Allah ya karɓa musu ayyukan dasuka gabatar
acikin wañnan wata. Kamar yadda Allah Mai girma yake fada
وَالَّذِينَ يُؤْتُونَ مَا آتَوْا وَقُلُوبُهُمْ
وَجِلَةٌ أَنَّهُمْ إِلَىٰ رَبِّهِمْ رَاجِعُونَ
Da waɗanda ke bãyar da abin da suka bãyar, alhãli
kuwa zukãtansu sunã tsõrace dõmin sunã kõmãwa zuwa ga Ubangijinsu. (Suratul
Muminun 60)
أُولَٰئِكَ يُسَارِعُونَ فِي الْخَيْرَاتِ وَهُمْ
لَهَا سَابِقُونَ
Waɗancan
sunã gaggãwar tsere a cikin ayyukan alheri, alhãli kuwa sunã mãsu tserewa zuwa
gare su (ayyukan alheri). (Suratul Muminun 61)
Sun kasance suna qoqari wurin yin
aiki, bayan sunyi aikin Kuma sai su dinga tunani shin Allah ya amsa ayyukan su
ko Bai Amsa ba! Wañnan Kuma Yana faruwa dasu ne sakamakon sanin girman Allah da
sukayi. Da sanin Allah baya amsan wani aiki sai Wanda akayishi da (iklasi) Kuma
akayi Shi yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yakoyar. (Mutaba'a) sun
kasance basa tsarkake kansu, Kuma suna tsoron abunda zai ɓata musu ayyukan su.
Samun Aikin su ya karɓu
yafi damun su fiye da wahalan yin aikin, domin fadin Allah Mai girma
إِنَّمَا يَتَقَبَّلُ اللهُ مِن المُتَّقِيْنَ
Allah Yana karɓã daga mãsu taƙawa
ne. (Suratul Ma'ida 27)
Sun kasance suna rage neman
duniya, suna kashe lokutansu a masallatai, suna kiyaye azumin su basa cutar da
kowa. Suna kiyaye lokutan su cikin karantu littafin Allah. Basa sake da lokacin
su ya tafi a asara, Kamar yadda mutane suke awannan lokacin. Suna raya dararen
su da salloli . Yinin su Kuma cike take da azumi, karatun Qur'ani, zikiri da
sauran ayyukan Alkhairi. Ba su kasance suna barin wa lokaci daidai da minti ɗaya ko second ɗaya ba face sun gabatar
da Aikin Alkhairi a cikin sa.
WALLAHU A’ALAM
Fatwa: Sheikh Salihul Fauzan.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.