Ticker

Awon Maganin Gargajiya A Littafin Ruwan Bagaja

Cite this article as: Abdullahi, I. S. S. (2011) “Awon Maganin Gargajiya A Littafin Ruwan Bagaja” Algaita Vol. 2 No1. Journal of Current Research in Hausa Studies Department of Nigerian Languages, Bayero University, Kano. Pages 234 -240. ISSN: 2141-9434

Awon Maganin Gargajiya A Littafin Ruwan Bagaja

Daga:

Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
E-main: kontago2003@yahoo.co.uk
Lambar Waya: 0803 6153 050

1.0 Gabatarwa

Magani a yawancin al’ummu na duniya abu ne da ake ba muhimmanci Ƙwarai da gaske ta yadda ake ganin cewa, rayuwa ba ta gudana ba tare da an yi mu’amala da shi ba. Wannan yana faruwa ne idan aka yi la’akari da cewa, yanayin jikin ɗan’adam ya al’adanci ya wayi gari yana cikin rashin lafiya ko kuma wata Ƙaddara ta rauni ta faɗa masa. Baya ga wannan kuma, rayuwa takan bukaci kariya daga abin da take ganin zai cuta mata a gaba, da ƘoƘarin cutar da wanda ba a natsu da shi ba. Haka kuma, fafutikar neman biyan wata buƘata ta rayuwa wadda ake ganin dabarar mutum ba za ta iya samar masa da ita ba, to akan nemi magani don a sami nasara. Waɗannan dalilai guda huɗu su suka tabbatar da wajibcin mu’amala da magani a rayuwar ɗan’adam.

MaƘasudin wannan nazari shi ne ƘoƘarin tabbatar da wannan hasashe da ke nuna cewa, dangantakar Bahaushe da magani daidai take da irin wadda ke tsakanin tsoka da jini. Ta yaya za a iya gaskata haka? Da yake magabata sun nuna Adabi shi ne ‘hoton rayuwa na al’uma (Ɗangambo, 1984), akwai bukatar yin amfani da wani reshe na hoton rayuwar Hausawa a matsayin wani mizanin awon dangantakar magani da rayuwar ta Hausawa. Amfani da adabi a wannan nazari ba zai rasa nasaba da tunanin cewa, ba abin da za a rasa na rayuwar Hausawa a idan an kalli adabinsu muddin dai an yarda da fassara da masana suka yi wa Kalmar ta adabi. 

2.0 Fashin BaƘin Tubalan Take

Wannan fasalin tamkar wata ’yar shimfiɗa ce da za ta bayar da haske kan ainihin muhimman tubalan da suka gina taken wannan nazari. Ko ba komai, Hausawa na cewa, ‘Waiwaye adon tafiya.’ Waɗannan tubalai kuwa su ne littafin Ruwan Bagaja da marubucinsa, da kuma ma’anar Kalmar magani.

2.1 Zakaran Gwajin Dafi

Ruwan Bagaja littafi ne da Alhaji Abubakar Imam ya wallafa. Shi kuma Abubakar Imam ba baƘo ba ne idan ana maganar rubutaccen adabi Hausa. Yana daga cikin haziƘan da Allah ya huwace wa Ƙasar Hausa musamman idan ana maganar ilimin boko. HaƘiƘa ya amsa sunansa (na Imam) domin mánàzàrtá sun tabbatar da cewa, shi ne limamin rubutaccen Ƙagaggen labarin Hausa (Mora 1989, Malumfashi 2009). Babu shakka ayyukan da wannan taliki ya yi su suka samar wa rubutaccen Ƙagaggen labarin Hausa martabar da yake da shi a yanzu. Wannan ne ya sa harshen Hausa ya yi wa duk sauran harsunan Ƙasar nan fintinkau musamman a wannan nau’i na adabi. Littattafan da Imam ya samar sun jawo hankalin ɗalibai da malamai da dama wajen ƘoƘarin fito wa jama’a irin hazaƘar da ya yi a zamaninsa.

Littafin Ruwan Bagaja shi ne littafin Abubakar Imam na farko kuma littafin da ya lashe gasar rubuta Ƙagaggun labaran Hausa na farko da Hukumar Talifi ta shirya a shekarar 1933 (Yahaya 1988). Duk da yake ba a wannan zamani ya rubuta littafin ba, har yanzu littafin yana cin kasuwa a duniyar mákàràntá da mánàzàrtá rubutattun Ƙagaggun labaran Hausa. Rubuce-rubucen da aka yi a kan nazarin wannan littafi a matakai daban-daban na ilimi ba su da iyaka. Kaɗan daga cikin su akwai na Ingawa (1969) da Yunusa (1985) da Kudan (1987) da Bunza (1991) da Malumfashi (1996, 2009) da dai sauran su. Matsayin wannan littafi da marubucinsa da kuma Ƙumshiyarsa, shi ya sa yake taka muhimmiyar rawa a dandalin nazarin Ƙagaggen labarin Hausa a duniya. HaƘiƘa wannan ne kuma ya sa ya zama zakaran gwajin dafi a wannan nazarin.

2.2          Magani

Kalmar magani ita ma ba baƘuwa ba ce a fagen nazarin al’adun Hausawa. Ayyukan Ahmad (1984) da Tukur (1988), da Bunza (1990 da 1995) sun fayyace matsayin magani, yadda ake samar da shi, mahaɗinsa, hanyoyin sarrafa shi, nau’o’insa, ma’abuta bayar da shi da dai duk abin da ya shafe shi musamman a gargajiyar Bahaushe. Duk da haka, a Ƙarin tabbatar da dugadugan wannan nazari, akwai bukatar a waiwayi abin da manazarta falsafar magani suka ce dangane da ainihin ma’anar kalmar.

Bunza (1990) ya bayyana ma’anar kalmar magani da:

 “….. wata hanya ce ta warkar da ko kwantar da ko rage wata cuta ta ciki ko ta waje ko wadda aka samu ta haɗari. Ko kuma neman kariya ga cuta ko abokan hamayya ko neman ɗaukaka da daraja ko buwaya ta hanyar siddabaru da sihirce-sihirce na ban al’ajabi.”

Tabbas! ya fito muna da ma’anar ta magani da ma dalilai uku daga cikin huɗu da aka ambata a baya na wajibcin samar da magani ga ɗan’adam. To sai dai ba lallai ba ne hanyoyin samun waɗannan magunguna su kasance siddabaru ko sihirce-sihice kawai, kamar yadda malamin ya ambata. Nazarze-nazarcen da suka biyo bayan sun tabbatar da sahihancin samar da magani musamman ga Bahaushe ta hanyar tsirrai ko itatuwa, da Ƙwari, da dabbobi, da addu’o’’i da surkulle, da dai sauran su da yawa.

3.0 Ga Wuta Ga Masara

Wannan fasali shi zai dubi waɗannan rassa na magani (huɗu) a cikin littafin Ruwan Bagaja domin tabbatar da hasashen da aka yi.

2.2.1      Magungunan Warkarawa

Wannan rukuni ya danganci maganin da ake tanada na warkar da cututtuka da ake iya gani a jikin mutum dangin Ƙurji, ko gyambo ko kumburi da kuma wani rauni da aka iya samu a jiki. Haka kuma, ya danganci cututtukan cikin jiki waɗanda ba a iya gani sai dai a ji raɗaɗinsu ko a ga alamun kamuwarsu ta hanyar kumburi ko ràmá ko hana sukunin gudanar da al’amurra yadda aka saba.

A littafin na Ruwan Bagaja, ana iya hango misalan wannan nau’i na magani tun daga ainihin maƘasudin samar da labarin. An nuna cewa, Yarima (ɗan Sarki) ba ya da lafiya. Sai a kwantar a tayar. Liman ya bayar da shawarar neman maganin da zai warkar da wannan cutar da ma na jama’ar Ƙasa baki ɗaya.

“Ni kuwa na ce na ji an ce da za a sami ruwan Bagaja a wani gari da mutanen garin nan duk sun huta.” (shafi na 5)

Gwada maganin da aka yi ya tabbatar da lallai rayuwa ba ta inganta sai da shi.

“Na ɗauki tsinke na tsoma cikin kwalabar Ruwan Bagaja, na jefa tsinken cikin wani ruwa a kwano, aka ba yaron ya sha. Da haɗewarsa sau ɗaya sai ya yi farat ya tashi. Nan take ya warke saura Ƙarfi kawai.’’ (shafi na 43)

Makanta ciwo ne da ke muzguna wa rayuwa ainun. Muddin dai akwai magani, to mai cutar ba zai ɗebe tsammanin gani ba. Imam, ya ci karo da irin wannan Ƙaddara ya kuma dace da magani a lokacin da ya haɗu da wasu bayin Allah.

“Bayan na huta suka tambaye ni labarina, duk na kwashe na faɗa musu. Da suka ji haka, sai suka ji tausayina suka ba ni magani, idona ya warke.” (Shafi na 16)

A lokacin da Imam ya kuskure shiga ɗakin da Ruwan Bagaja yake, aljanu sun yi masa raunin da dole ya nemi magani.

“Da Sarkin Aljannu ya gan ni jina-jina, rotse ko’ina, ya ce ‘Ka kuru, da sun kashe ka. Na gaya maka ka lura, na gaya maka, ka lura, ai ga shi ka gani. Allah Ya sa ba su halaka ka ba.’ Ya ce, ‘Zauna sai ka warke ka koma.’ Suka yi mini magani na warke.” (Shafi na 39)

Bayan da Imam ya sami Ruwan Bagaja, ya kama hanyar zuwa gida ta cikin teku ya ɓullo ta wata rijiya mai suna Maiburgami a birnin Kano, ya nuna ya fuskanci barazanar kamuwa da ciwon kurumta a sakamakon kwaramniyar da ya sha. Nan ma dole ya nemi maganin warkarwa.

“Sarki ya sa aka kawo mini abinci na ci. Motsin teku ya tashi kurunta ni, sai da na sha magani kwana bakwai, sa’an nan na warke.”(Shafi na 41)

2.2.2      Magungunan Kare Kai

Waɗannan magunguna su ne akan tanada a ƘoƘarin kauce wa ɓacin rana ko wasu bala’o’i ko Ƙaddarori da ake ganin za su iya aukuwa a kowane lokaci. Hausawa na cewa, ‘don gobe ake wankan dare.’ Misalin irin waɗannan magunguna sun haɗa da na hana ɓarawo sata, da maganin kamun maye, da na tauri, da sagau/Ƙago, da harbin kunama ko dafin maciji da dai sauran su.

A littafin na Ruwan Bagaja an sami wanzuwar irin waɗannan magunguna na kare kai. Misali, bayan da SaƘimu (agolan Malam Na-Bakin Kogi) ya kashe malamin, sai ya yi mugun mafarki. Maganin farko da ya yi tunani don kare kansa daga sakamakon mafarkin shi ne ya tara malamai su fassara masa gaskiyar al’amari.

“Dukan malamai, kowa ya duƘufa ya zana ya shafe. Daga nan sai babbansu ya ce, ‘za a haifi wani yaro a gidan nan, cikin matan tsohon nan da ya rasu shi zai kashe ka.’” (Shafi na 4)

Baya ga Imam, a wannan littafi, wani tauraron da ya yi fice shi ne Malam ZurƘe. Gwagwarmayar da ya sha, ya sa dole ya nemi maganin kare kai don gudun ɓacin rana. A lokacin da Imam ya sauka wani Ƙauye ya tarar da ba sana’ar da Malam ZurƘe ke yi illa sata. Ganin haka ya sa ya yi tunanin Ƙulla masa sharri. Da dare ya yi, ZurƘe ya sallami matarsa ya fita. Sai Imam ya ɓatar da kama ya miko mata gawar mutum a ɗaure cikin duhu. Shi kuma ZurƘe da ya dawo, bai musanta cewa, ba shi ya miƘo gawar ba, sai bayan da suka kwance. Wannan gawar ita ta saka ZurƘe cikin rikicin da ya ga ba mafita in ba ta hanyar magani ba.

“Gari na wayewa Sarki na jin labarin. Nan da nan ya aiko aka ɗunguma da su. Da dare na sami labari ZurƘe ya yi layar zana ya tsere.”(Shafi na 25)

Addu’a tana ɗaya daga cikin hanyoyin da ake amfani da su a matsayin maganin kare kai daga aikata saɓo ko kuma kariya daga miyagun Ƙaddarori. A cikin wannan littafi, bayan da Imam da ZurƘe suka jima suna cutar juna, a haɗuwar da suka yi a Ƙauyen Yalwa suka zarce Birnin Ƙudus, har Baitul MuƘaddas, sun yi amfani da wannan dabarar don neman kariya.

“A wannan gari mai albarka Malam ZurƘe ya ce mu tuba da irin ayyukammu na saɓo hakanan. Na yarda da magana tasa, muka tara malamai aka yi mana addu’a don kada sheɗan ya sake wasa da zukatanmu.”(Shafi na 12)

Bayan da haƘar Imam ta fara cim ma ruwa, Sarkin aljannu ya gaya masa inda zai sami Ruwan Bagaja, kafin su rabu sai da aka ba shi wata waƘa da zai rinƘa rerawa a matsayin kariya daga sharrin aljannu da kuma tsoron da zai ji a sakamakon ganin abubawan al’ajabi.

“Da ka shiga garin ka yi ta rera wannan waƘa: ‘Wa yaf’alu fi hukumi ma yasha’u. Ta’alal ilahu wa jallal hakam,’ har ka ɗebo rowan ka fito …. Don za ka ga abubuwan da ba ka saba gani ba.” (Shafi na 38)

2.2.3      Magungunan Cutarwa

Wannan reshe na magunguna ya Ƙunshi waɗanda ake yi don a cutar da wani mahaluki a bisa wani dalili da mu’amala ta yau da kullum take haifarwa. Akan yi wa irin waɗannan magunguna laƘabi da magungunan sharri. Misalin irin waɗannan magunguna sun haɗa da yin sihiri a kashe mutum, da kurciya, da ɗaure bakin mutum, da kashe azzakarin namiji, da nakasa wata gaɓa ko sashe na jiki kamar makantar da mutum, da cusa wata mummunar ɗabi’a a rayuwa kamar fitsarin kwance, ko a haukatar da mutum da dai sauransu.

A littafin Ruwan Bagaja, wuri na farko da aka yi amfani da magani don cutarwa shi ne lokacin da Imam ya shiga neman aure, ya kuma kasa abokan hamayya. Ba kowane namiji kan jure wa irin wannan Ƙalubale ba musamman daga baƘo irin Imam.

“Da sun hange ni sun shiga zagina ke nan. Mai tsina na yi, mai zagi na yi. To, ni da nake baƘo lalle sai in kame bakina, gama fa shi ya fi. Abu dai ya tsananta, har suka yi makircin da suka Ƙwace mini matar. Suka yi mini magani na makance.” (Shafi na 14)

2.2.4      Magungunan Biyan Bukatocin Rayuwa

Wannan rukuni yana Ƙunshe da magungunan da akan tanada don biyan bukatar rayuwa ko taimaka wa rayuwa ta gudana yadda ake bukata. Misalin irin waɗannan magunguna akwai asirran nasarar neman aure, da na farin jini, na na sauƘin samun bashi, da na kiran kasuwa, da na neman mulki ko shugabanci ko ɗaukaka da na neman ilimi da sauransu ba iyaka.

A littafin na Ruwan Bagaja, lokacin da Imam ya bar gida, a kan hanyarsa ta neman Ruwan Bagaja, ya fara ya da zango ne a wani dutse da ke cikin Ƙungurmin daji. A nan ne ya haɗu da wani tsoho a cikin kogo, ya kwana biyu. Da zai tafi, ya nemi a buga masa Ƙasa.

“bayan mun saba da juna na ce masa ya buga mini Ƙasa, ya gaya mini labarina da labarin niyyata. Ya buga Ƙasa ya ce, ‘Ruwan Bagaja dai akwai shi a duniya, amma yana hannun aljannu. Ƙarewa ma ba shi a bisa Ƙasan nan da muke takawa.’ ” (Shafi na 6)

Bugun Ƙasa, wani nau’in magani ne da Malaman tsibbu suka laƘanta. Neman Ruwan Bagaja kuwa ga Imam wata bukata ce da yake son biya wa zuciyarsa. Sakamakon da ya samu daga bugun Ƙasar da Malamin ya yi, shi ya Ƙara masa Ƙwarin guiwa na ci gaba da tafiya don ya biya wannan bukata tasa.

4.0 Naɗewa

HaƘiƘa ruwa na Ƙasa sai ga wanda bai tona ba. Wannan nazari ya tabbatar muna da cewa, magani abu ne da yake tafiya da rayuwa. Duk da kasancewar wannan littafi na Ruwan Bagaja an samar da shi ne saboda gasa, bai hana marubucin ya bayyana abin da ya zama tilas a ambata na magani ba. Hasali ma dai, buƘatar magani ita ce Ƙashin bayan labarin. Fafutikar neman magani shi ya gina duk wasu rassa na labarin, waɗanda a cikin su kuma aka ta samun tsarmin sauran nau’o’in magani. Idan da daga cikin dokokin gasar an nuna ba a bukatar magani ya fito, da watakila an kasa samun littafin da zai yi armashi ko farin jinni irin wannan. Kasancewar magani abin da ya wajaba ne a rayuwa, ba ma a wannan littafin ba, haka ake tsammanin lamarin ya kasance a duk wani nau’in adabi, muddin dai ya amsa sunansa na hoton rayuwa.

5.0 Manazarta

Ahmad, I. A. (1984) “Cututtukan Ciki da Magungunansu.” Kudin Digiri na Farko, (B. A.

 Hausa) Jami’ar Bayero, Kano.

Ɗangambo, A. (1984) Rabe-Raben Adabin Hausa Da Muhimmacinsa Ga Rayuwar Hausawa. Kano, Triumph Publishing Company.

Bunza, A.M. (1990), “HayaƘi Fid Da Na Kogo: (Nazarin Siddabaru Da Sihirin Hausawa)”, Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa), Jami’ar Bayero, Kano.

Bunza, A. M. (1991) “Sharhin Ciki da Wajen Littafin Ruwan Bagaja.” MaƘalar da aka gabatar a taron Makon Hausa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Bunza, A. M. (1995) “Magungunan Hausa a Rubuce: (Nazari Ayyukan Malaman Tsibbu),” Kundin digiri na uku (Ph.D Hausa) Jami’ar Bayero, Kano.

Bunza, A. M. (2006) Gadon Feɗe Al’ada Tiwal Nig. Ltd Lagos.

Gusau, S. M. (2008) Dabarun Nazarin Adabin Hausa, Kano, Benchmark Publishers Limited.

Imam, A. A. (1999) Ruwan Bagaja, Zaria, Nothern Nigeria Publishing Company.

Ingawa, A. (1969) Ruwan Bagaja. The Water of Cure. Fassarar Hausa zuwa Ingilishi, Zaria,

Nothern Nigeria Publishing Company.

Kudan, M. B. T. (1987) “Kwatanta Jigon Ƙagaggun Labaran Gasa.” Kundin Digiri na Ɗaya,

Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya

Malumfashi, I. (1996) “The Making of Abubakar Imam’s Ruwan Bagaja: A preliminary

 Investigation.” MaƘalar da aka gabatar a taron ANA Arewa House, Kaduna.

 

Malumfashi, I. (2009) Adabin Abubakar Imam, Sokoto, Garkuwa Media Services LTD.

Mora, A. A. (1989) Abubaka Imam Memoirs, Northern Nigerian Publishing Company, Zaria.

Mukhtar, I. (2004) Jagoran Nazarin Ƙagaggun Labarai, Kano, Benchmark Publishers Limited.

Tremearne, A. J. N. (1913) Hausa Superstitions And Customs, Oxford, John Bale, Sons and Danielsson, LTD.

Tukur, A. (1988) “Nazari a kan Cututtukan da suka shafi Fatar Jiki da Magungunansu a

Bahaushiyar Al’ada.” Kudin Digiri na Farko, (B. A. Hausa) Jami’ar Bayero, Kano.

Yahaya, I. Y. (1988) Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa, Zaria, Nothern

Nigeria Publishing Company.

Yunusa, M. M. (1985) “Kasancewar Tatsuniyar Ruwan Bagaja tushen littafin Ruwan Bagaja

na Abubakar Imam” Kundin Digiri na Ɗaya, Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Sakkwato.

Post a Comment

0 Comments