An yi tsokaci dangane da tuwo a babi na biyar (5.0). Ire-iren tuwon da aka yi bayani a wancan babin sun kasance na gargajiya ne. Ko bayan zuwan zamani, Bahaushe ya ci gaba da amfani da tuwo. Zamani ya samar da dabarun sauye-sauye ga nau’o’in tuwon gargajiya da ake da su. A ɓangare guda kuwa, akwai nau’o’in tuwo da Bahaushe ya samu a zamanance. Ya same su daga baƙin al’ummu na kusa da na nesa.
Wannan babi na goma sha tara na ɗauke da bayanai dangane da ire-iren tuwon Bahaushe na zamani da yadda
ake sarrafa su. Za a tarar da cewa, wasu daga cikin nau’o’in tuwon da ma
Bahaushe yana da su tun gargajiya. Idan haka ta kasance, ana bayyana ‘yan
sauye-sauye ne kawai da ake samu yayin sarrafa tuwon (ba tare da maimaita
bayanin tuwon ba, kasancewar bayani ya gabata cikin babi na biyar).[1]
Tuwon Ƙasari
Wannan nau’in
tuwo daidai yake da tuwon ƙasari na gargajiya kamar yadda aka yi bayani a babi
na biyar (ƙarƙashin 5.1). Bambanci
da ake samu kawai shi ne, akan niƙa gero ne a inji a maimakon niƙan dutse na gargajiya, ko dakawa a turmi. Bayan nan sai
‘yan bambance-bambance da ake samu waɗanda suka shafi
kayayyakin dafa abincin, wato kamar murhunan zamani ko gas kuka ko risho da sauransu.
Tuwon Tsaki
Tuwon tsaki na zamani ba shi da wani bambanci na
a-zo-a-gani da tuwon tsaki na gargajiya. ‘Yan bambance-bambancen da
ake samu ba su wuce amfanin da ake yi da inji wurin niƙa ba a maimakon dutse ko daka a turmi (kamar yadda yake a gargajiyance). A yau akan
kai hatsi niƙan
barzo/barza/datsa[2]
kai tsaye. Wannan ya kasance saɓanin a gargajiyance inda bayan an daka hatsi ko an niƙa a dutse, sai an tankaɗe kafin a
yi amfani da tsakin a matsayin mahaɗin tuwon tsaki.
Tuwon Bado
A babi na goma
sha bakwai ƙarƙashin 17.3 an yi
bayanin bado. Tuwon bado kuwa, an kawo bayani kan yadda ake samar
da shi a ƙarƙashin 5.14 da ke
babi na biyar. Babu wani bambanci tsakanin yadda ake tuwon bado na gargajiya da kuma na zamani.
Tuwon Ƙullu
An yi bayanin
tuwon ƙullu a ƙarƙashin 5.4. Kayan
haɗin tuwon ƙullu a gargajiyance
su ne dai ake amfani da su a zamanance.Bambancin da ake samu kawai shi ne wanda
ya shafi nau’in sarrafa hatsin, wanda a nan ana yin sa ne a zamanance (misali,
amfani da inji). Bayan an sauƙe tuwo kuwa, akan naɗe ne
cikin leda a sanya a kuloli ko wasu mazubai na zamani a maimakon yadda abin
yake a gargajiyance.[3]
Tuwon Gero
Yadda ake
sarrafawa da samar da tuwon gero a zamanance ba shi da bambanci da yadda abin
yake a gargajiyance. An yi bayanin tuwon gero a ƙarƙashin 5.5 da ke babi na biyar.
Tuwon Dawa
A babi na biyar,
an yi bayanin tuwon dawa a ƙarƙashin 5.6. Babu wani bambanci na a-zo-a-gani da yadda ake
samar da tuwon a zamanance. Duk da haka, wannan bincike ya ci karo da bayanan da ke nuna cewa
a yanzu amfani da kanwa na raguwa matuƙa.
Tuwon Maiwa
An yi bayanin
tuwon maiwa a ƙarƙashin 5.7 na babi na biyar. Hanyoyin da ake bi wajen sarrafa tuwon maiwa a gargajiyance daidai yake da
yadda ake yinsa a zamanance.
Tuwon Masara
An yi bayani game
da tuwon masara a 5.8 da ke babi na biyar. Hanyoyin sarrafa
tuwon a gargajiyance daidai yake da yadda ake sarrafa shi a zamanance.
Naɗewa
Akwai nau’o’in tuwo da dama na gargajiya da ba su da bambanci da yadda ake samar da su a zamanance. Waɗannan nau’o’in tuwo sun haɗa da tuwon masara da na dawa da na maiwa da na bado da sauransu. Duk da haka, zamani ya zo da wasu nau’o’in tuwo daban da waɗanda ba a san su a gargajiyance ba. Yawanci an same su ne a sakamakon tasirin zamani da kuma na baƙin al’ummu.
[3]Naɗe tuwo cikin leda bai zama dole ba, sai dai ya kasance hanyar tattalin tuwo da ajiyewa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.