Za a iya hasashen cewa, soyayyiyar miya ba gadajjiya ba ce ga Bahaushe. A maimakon haka, ya same ta ne a sama sakamakon cuɗanyarsa da baƙin al’ummu. Wannan ne ya sa, ko cikin gari ba a faye samun wannan nau’in miya ba. A ƙauyuka kuwa, sai dai abin da ba a rasawa.
Mahaɗin
Miya Soyayyiya ko Dafaffiya da Babu Ruwa a Ciki
Kayan haɗin
wannan nau’in miya sun haɗa da:
i. Albasa
ii. Gishiri
iii. Kayan yaji
iv. Kifi ko Nama (idan
akwai)
v. Kori
vi. Magi
vii. Ruwa
viii. Tafarnuwa
ix. Tarugu
x. Tattasai
xi. Thyme
xii. Tumatur
xiii. Zogale ko Alayyafu
Yadda
Ake Soyayyiya Ko
Dafaffiyar Miyar Da Babu Ruwa A Ciki
Da farko za a iya amfani da zogale ko alayyafu domin samar da wannan miya. Duk wanda ya samu akan wanke shi da gishiri sosai. Idan alayyafu ne sai an
yanka shi manya-manya,
sannan za a saka shi
a cikin tukunya a dafa. Kada a bari ya dafu sosai in alayyafu
ne. Idan kuma zogale ne, a zuba zuma da ’yar kanwa a dafa sosai. Daga nan sai a cire ganyen a saka shi cikin
kwando a tace sannan a bar shi ya tsane, sai a aje gefe ɗaya. Za a ɗauko kifi ko nama a haɗa
da albasa sannan a tafasa.
Daga wannan ya samu, za a yi jajjage sannan a zuba cikin tukunya a haɗa da wannan kifi ko nama tare da mai, kamar yadda ake na sauran miya. Bayan ya soyu, za a sanya kayan ƙamshi da na ɗanɗano. Da zarar sun soyu, za a zuba ganyen, a yi ta juyawa har sai ganyen ya soyu daidai yadda ake buƙata. Akan yi amfani da wannan nau’in miya wajen cin kuskus ko shinkafa ko dambu da dai makamantansu.
Tsokaci
Irin wannan miya takan daɗe ba tare da ta ɓaci ba. Wannan na faruwa ne sakamakon ba a sanya ruwa
cikinta. Wani lokaci ma akan sanya miyar a firijin. A irin wannan lokuta, takan
ɗauki kwana da kwanaki ba tare da ta ɓaci ba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.