Miyar Albasa Da Miyar Karas

    Miyar Albasa

    Albasa na É—aya daga cikin ganyayen Bahaushe wanda yake nomawa. Tana matuÆ™ar kama da gadali. A saman albasa akwai lawashi (ganye). A Æ™asa kuwa, akwai asalin Æ™wallon albasar wanda ke ruÉ“anye, wani saman wani. Shi ya sa ma Bahaushe ke da kacici-kacicin da ke cewa: “Cikin ma da cikin cikin, cikin ma da cikin, “wato albasa.

    MahaÉ—in Miyar Albasa

    Akwai abubuwan da za a tanada idan za a haÉ—a miyar albasa. Abubuwan sun haÉ—a da:

    i. Albasa

    ii. Attarugu

    iii. Gishiri

    iv. Kayan yaji

    v. Kori

    vi. Magi

    vii. Mai

    viii. Ruwa

    ix. Nama ko kifi (idan da hali)

    Yaddda Ake Miyar Albasa

    Ana É—ora tukunya ne sannan a zuba albasa a soya a jajjaga albasa mai yawa tare da tarugu. Sannan sai a yanka nama Æ™annan a soya su tare. Idan an yanka naman za a zuba a cikin tukunya ya soyu sosai. Za a saka magi da gishiri da kori da kayan yaji. Ruwan da ake sanyawa yayin sanwa kaÉ—an ne. Bayan sanwa ta tafasa, za a zuba albasa mai yawa da aka yayyanka kuma aka wanke. Akan ci wannan miya da shinkafa ko kuskus ko tuwon semo da sauransu.

    Tsokaci

    Kusan birni da ƙauye ana miyar albasa, duk da cewa an fi samunta a birane. Babu garin da ba a samun albasa a cikin garuruwan ƙasar Hausa. Duk da haka, ba kowa ke shan miyar albasa ba, a dalilin warinta da wasu mutane ke ji musamman maza.

    Miyar Karas

    Karas na É—aya daga cikin kayan marmarin Bahaushe. Akan ci shi haka nan ko da ba a haÉ—a shi da komai ba. Kamar dai yadda aka gani a sama (cikin bayanan wasu nau’o’in abinci), karas na iya kasancewa mahaÉ—in wasu nau’o’in abinci na daban. Amma a wannan gaÉ“a, za a yi maganar karas ne a matsayin babban mahaÉ—in miya.

    MahaÉ—in Miyar Karas

    Akwai wasu kayan haɗin da ake buƙata yayin samar da miyar karas. Abubuwan sun haɗa da:

    i. Albasa

    ii. Albasa

    iii. Gishiri

    iv. Karas

    v. Kayan yaji

    vi. Magi

    vii. Mai

    viii. Nama (idan da hali)

    ix. Ruwa

    x. Tafarnuwa

    xi. Tarugu

    xii. Tattasai

    Yadda Ake Miyar Karas

    Akan samar da miyar karas ne kamar yadda ake samar da ta kabeji. Wurin da suka bambanta shi ne, a maimakon a sanya kabeji, a nan akan zuba karas ne. Akan wanke karas sosai sannan a yayyanka shi sala-sala kafin a zuba. A yayin sanwarta, ba a zuba ruwa sosai. Akan ci wannan miyar da shinkafa ko kuskus ko tuwon shinkafa ko sakwara da dai makamantansu. 

    The book “Cimakar Bahaushe” (Diets of the Hausa People) is a collection of 293 traditional and modern diets of the Hausa people. Detailed explanations of the recipes and ingredients are provided. Comments are provided on the areas of the Hausa land where specific diets are mostly found, the age categories of people that usually use it, as well as the scientific impact of some of the diets to human biology.  Data is collected from interviews with different categories of people including:  i.                    Food sellers within the Hausa land: Mainly to have an idea of recipes on the diets.  ii.                  People of older age: Mainly to have insights on traditional diets of the Hausas.  iii.               Hausa scholars: Mainly to verify and justify the validity of the information obtained as well as provide further expert explanations on the diets.  Moreover, over two hundred (200) pieces of literature were reviewed to have better insight on the topic in question as well as get scientific and professional clarifications on some key concepts relevant to the research. The pieces of literature cover major relevant phenomena such as diet and hunger. Others are on the Hausa land and the Hausas.  The book contains thirty-three (33) chapters. Chapter one is the main introduction in which a concise explanation is provided on the Hausas, their history, their land, social life, and transformations due to globalization, acculturation, and modernity. Chapter two detailly discusses the concepts of diet and food from the Hausa point of view. That includes the meaning and the usage of diets in some Hausa works of literature both verbal and written (i.e. prose, poetry, proverbs, etc.).  Chapters three and four discuss the sources of Hausa diets and their forms accordingly. Chapters five to seventeen discuss some traditional Hausa diets including hard and soft ones. Chapter eighteen concentrates on the influence of modernity and globalization on Hausa diets. It has been discovered that there have been some significant changes in the Hausa diets ranging from recipes to kitchenettes.  Chapters nineteen to thirty-two discuss modern Hausa diets. Some traditional diets are still retained with little modifications, while on the other hand, there are a lot of new ones. Chapter thirty-three discusses “hunger” from the Hausa point of view. The relationship between hunger and food is examined. Additionally, the use of hunger in various Hausa literary works is studied. It is concluded that hunger is like a disease whereby its cure is food.  7th November 2022
    Citation (Manazartar Littafin): Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

    Get a copy:
    To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
    +2348133529736

    You can also write an email to:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.