Cite this article as: Abdullahi, I. S. S. (2012) “Muhallin Magani a Adabin Bakan Bahaushe” Ɗundaye Journal of Hausa Studies Vol. 1, No 4. Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto. December, Pages 187-198
Muhallin Magani
A Adabin Bakan Bahaushe
Daga:
Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
E-mail: kontago2003@yahoo.co.uk
Lambar Waya: 0803 6153 050
Tsakure
Ƙokarin da aka yi na
samar da wannan nazari yana da dangantaka da tunanin cewa a duk inda adabin
Bahaushe yake akwai tasirin magani a ciki. Wannan fahimta ta tuzgo ne bisa
la’akari da cewa, rayuwa ba ta gudana ba tare da magani ba. Don haka dole ne
adabin ya ɗauko
hoton magani muddin yana son ya amsa sunansa. Wannan nazari ya yi ƘoƘarin tabbatar da
hakan ta hanyar duban ɓangarorin
adabin baka daban-daban.
1.0 GARATARWA
Masana
Hausa sun yi ittifaƘi
da cewa,
2.0
ADABI A TUNANIN MASANA HAUSA
Kawowa
yanzu, babu wasu saɓanin ra’ayoyi a tsakanin
masana adabin Hausa a
3.0
MAGANI
DA RASSANSA A GARGAJIYAR BAHAUSHE
Idan
Bahaushe ya ambaci
3.1
RASSAN MAGANI TA FUSKAR BUKATUN MUTANE
Manazarta
al’adun Hausawa, musamman ma waɗanda suka mayar da
hankali ga magungunan gargajiya, sun yi la’akari da bukatocin mutane na magani
wajen karkasa magungunan Hausawa.
(i)
Magungunan warkarwa, waɗanda
suka Ƙunshi
duk wani magani da ake amfani da shi don warkar da cuta ta zahiri ko ta cikin
jiki ko rauni da dai makamantan su.
(ii)
Magungunan kariya, su kuma sun Ƙunshi
magungunan da Hausawa suke sarrafawa ko amfani da su don kare kai daga cuta ko
cutarwar mutum ko aljani ko wata dabba ko Ƙwaro.
(iii)
Magungunan cutarwa, akan
tanade su ne da tunanin cutar da wasu mutane bisa wasu dalilai na Ƙiyayya ko hukunci
ko ramuwar gayya ko gyara wa wani zama.
(iv)
Magungunan biyan bukatocin rayuwa, sun Ƙunshi duk wani
magani da zai Ƙara
wa rayuwa kwarjini da ado da jin daɗi. Magunguna ne da
ake amfani da su domin su samar wa zuciya abubuwan da take so waɗanda
ba ta iya samar wa kanta su kai tsaye.
3.2
RASSAN
MAGANI TA FUSKAR ABIN DA AKE SARRAFAWA
ƘoƘarin gano
magugunan da Hausawa suke mu’amala da su a gargajiyance shi ya ba manazarta
damar karkasa su ta la’akari da ainihin abin da ake sarrafawa wajen aiwatar da
maganin. A al’adance, an fi amfani da abubuwan da al’uma ta samu a muhallin da
take zaune a matsayin magani. Tunanin wannan ya sa aka rarrabe magungunan
gargajiya na Hausawa zuwa ga dangoginsu. Akwai magungunan da aka samo daga
itace ko tsirrai. Wasu kuma daga dabbobi da Ƙwari, ko sassan
jikin mutane ko wani abu da ya fito daga jikin nasu kamar Ƙumba da gumi da
dai sauran su. Haka kuma akwai magungunan da suka shafi ruwa da Ƙasa. Wasu kuma
addu’o’i ne da surkulle ko karance-karance da yanka ko zubar da jini da dai
sauran su.
3.3
RASSAN
MAGANI TA FUSKAR YADDA AKE SARRAFA SU
Kowane
irin magani da nau’insa. Wannan ya kasance haka ne da yake bukatocin mutane ba ɗaya
ba, abin da ya sa hanyoyin sarrafa magungunan suka bambanta. Wannan bambancin
shi ya ba da damar karkasa magunguna zuwa rukunai daban-daban. Daga cikin waɗannan
kashe-kashe akwai magungunan gargajiyar da ake sha, akwai na shafawa a jiki.
Wasu a shaƘa
a hanci, wasu a sa cikin wuta a turara, wasu kuma a dafa su a yi suraci da
turirin. Wasu magungunan binnewa ake yi a cikin Ƙasa, a yayin da
ake ɓoye
wasu a cikin wani abu a doron Ƙasa
da sauran dabaru na sarrafa magani.
4.0
MAGANI
A ADABIN BAKAN BAHAUSHE
Wannan
fasali zai mayar da hankali ne wajen zaƘulo irin rawar da
magani ke takawa wajen ginuwar adabin bakan Bahaushe. A ƘoƘarin yi wa nazarin
adalci, za a ɗora magani a rassan bishiyar li’irabin Gusau
(1984) na rabe-raben adabin baka.
4.1
ZUBE
Rukunin
zube a adabin bakan Bahaushe rukuni ne da ya Ƙunshi duk wani
labari da za a bayar da baki. Misalan zube na baka sun haɗa
da tatsuniya da hikaya da Ƙissa
da labarai da tarihi da barkwanci da almara. Ga misalin yadda lamarin magani
yake watayawa a biyu daga cikin su.
4.1.1
Tatsuniya
Tatsuniya
a taƘaice,
Ƙagaggen
labari ne da al’adar Hausawa ta tanada domin ba da nishaɗi
da kuma cusa tarbiyya ga yara (Yahya 1994). Da yawa daga cikin tatsuniyoyin
Hausawa suna ɗauke da lamarin magani ta hanyar nuna cewa, ba
lafiya an nemi magani, ko kuma wata bukata ta taso wadda ba makawa sai an nemi
magani sannan a kawar da ita. Irin wannan bukata tana iya kasancewa wani ne ake
son cutarwa ko wata kariya ce ake son yi daga cuta. Haka kuma yana iya
kasancewa wata bukata ce ta rayuwa kawai ake son biya. Misali:
A tatsuniyar “Maraya da saniya mai Magana,”
kishiyar uwar Janniya ta yi ta zuwa wajen malamai da ‘yan bori tana karɓo
maganin da za ta halaka shi ta mallake dukiyar da uwarsa ta bar masa. Duk
maganin da aka yi amfani da shi don cuta masa sai saniyarsa mai magana ta
Wannan
tatsuniyar ta ɗauko muna hoton yadda Ƙiyayya ke sa a yi
ta faɗi-tashi
wajen neman maganin cutar da wanda ba a so. To haka irin waɗannan
misalai suke da ɗimbin yawa a tatsuniyoyin
Hausawa.
4.1.2
Almara
Almara
wani gajeren Ƙagaggen
labari ne da ake bayarwa sannan a bukaci mutum ya faɗi amsa ko ya yi zaɓi
tsakanin abubuwan da aka ambata. Galibi almara
Wani
magidanci ne mai mata biyu da ‘ya’ya da yawa ya kwanta rashin lafiya shekara da
shekaru ciwo ya Ƙi
ci, ya Ƙi
cinyewa. An yi maganin duniyar nan amma Allah bai sa an dace ba. Uwargidansa
ita aka
A
wannan almarar an kawo matsala, aka nuna magani ya kasa samuwa cikin sauƘi. Wannan da ma
al’ada ce ta ciwo. Bahaushe ya yarda da cewa, magani sai dace. Bayan da aka
sami maganin kuma, sai almarar ta Ƙara fito da wata al’adar
bayar da magani a rayuwar Hausawa, wato kafa sharaɗin amfani da
magani. HaƘiƘa wannan misali ya
tabbatar muna da nason magani a adabin bakan Bahaushe.
4.2 MAGANGANUN AZANCI
Rukunin
maganganun azanci a adabin bakan Bahaushe rukuni ne da yake da rassa da yawa
wanda ke nuna irin hikima ko fasahar Hausawa wajen sarrafa harshen su a lokacin
da suke magana. Wannan rukuni ya Ƙunshi fasahohi irin su: Salon
magana da Karin magana da Habaici da Ba’a da BaƘar magana da
Kirari da Take. Ga misalin yadda magani ke rausayawa a ɗaya daga cikin su.
4.2.1 Karin Magana
Karin magana
kamar yadda magabata suka nuna, dabara ce ta dunƘule magana mai
yawa a cikin zance ko ‘yan kalmomi kaɗan cikin hikima (Ɗangambo 1984:38).
Fasaha ce da kan Ƙara
wa zance armashi da bayyana halayen rayuwar Bahaushe na haƘiƘani. Hausawa sun
yi fice ainun wajen amfani da Karin magana a zantuttukansu na yau da kullum.
Kamar yadda sha’anin magani ya yi ta watayawa a tatsuniya da almara, haka ya
sami ranar shanya a Karin magana. Fitowar magani a Karin maganar Hausawa yakan ɗauki
fuska biyu:
(i)
Magani ya fito muraran a
cikin Karin magana. Misali:
-
Da tsohuwar zuma ake magani.
-
Abin majinyaci na mai magani
ne.
-
Da kura na da maganin zawo da
ta yi wa kanta.
-
Idan magani ya Ƙi ci ba ya Ƙi zubarwa ba.
-
Idan ka ci maganin Ƙarfe, ka ci na Ƙarfi?
-
Magani a sha ka ba don yunwa
ba.
-
Da haka ake yi a ce ba a sha?
An sa wa majinyaci zuma a magani.
(ii) Amfani
da
-
Haihuwa da yawa maganin
annoba.
-
Maganin biri, Karen Maguzawa.
-
Gobara daga kogi maganinta
Ubangiji.
-
Hadarin Ƙasa maganin mai
kabido.
-
Idan so cuta ne, haƘuri magani ne.
-
Tuwon salla maganin mai haɗama.
-
Barin kashi a ciki ba ya
maganin yunwa.
-
Haukar ba ni, maganinta ungo.
-
Haske maganin duhu.
-
Hannu da yawa maganin Ƙazamar miya.
-
HaƘuri maganin zaman
duniya.
-
Arha maganin mai wayo.
-
Waiwaye maganin mantuwa.
-
Gudu da mari ba ya maganin
bauta.
4.3
RAHA
Raha
wani babban reshe ne daga rassan adabin bakan Bahaushe. Shi ne reshen da yake ɗauke
da duk nau’o’in rabe-raben waƘoƘin Hausawa kamar
waƘoƘin aiki, da na gaɗa
da na yara da waƘoƘin fada da na
sha’awa da na maza da waƘoƘin jama’a da dai
sauran su. A kowane ɗaya daga cikin waɗannan
rukunai na waƘa
akwai mutanen da suka yi fice, kuma akwai waƘoƘi masu armashi da
ke fito da hoton rayuwar Hausawa musamman dangane da al’amurran da ke faruwa
yau da kullum. ƘoƘarin da wannan
fasali zai yi shi ne, fito da lamarin magani a wasu daga cikin rassa na waɗannan
waƘoƘin don tabbatar da
dugadugan wannan nazarin.
4.3.1 WaƘoƘin gaɗa
A
al’adar Hausawa, yara ’yan mata sukan fita wasan gaɗa a dandali da
dare. A irin wannan lokacin sukan yi wasannin da suke Ƙunshe da waƘoƘin waɗanda
suke bayyana ra’ayoyi ko abin da suka hango, musamman a rayuwar aure ko ma
rayuwar mace gaba ɗaya. Wasu daga cikin waɗannan
woƘoƘin sukan fito da
hoton magani. Ga misali:
“Ayye yaraye,
Ayye yaraye,
Ayye yaraye iye nanaye.
Ni ba kishiya,
Ni ba kishiya,
Ni ba kishiya nake tsoro ba.
Tai maka magani,
Tai maka magani,
Tai maka magani ka faɗa daji,
Hanyar gidanku ta ɓarɓace
maka.”
Wannan
misalin ya fito da wata al’ada ta Ƙiyayya da ke dasuwa a zukatan
kishiyoyi na neman magungunan sharri a Ƙuntata wa juna. Su
kansu ‘yamatan da ba su
4.3.2 WaƘoƘin Jama’a
WaƘoƘin Jama’a su ne waƘoƘin da makaɗan
Hausa ke rera wa kowane irin mutum. Wannan ya Ƙunshi waƘoƘin attajirai da na
mutanen da suka yi fice a wani sha’ani na duniya da dai duk wanda ya ja
hankalinsu. Wasu daga cikin irin waɗannan waƘoƘi kai tsaye a
“Malam Babba na Ƙofar Gabas,
Na ga dai yai shirin ya duba mani,
Ya dai haka, sai na ga nai yai haka,
Ya kimtsa sai na ga ya yo haka,
Ya sake shiryawa sai na ga ya yo haka,
Ya fid da uku ya ɗauke
shida,
Sannan ya ɗauke
huɗu ya ɗauke
Na ga yai gum da ni yana al’ajab,
Ya ce mani, ‘kai makaɗi
mai kiɗa,
Sha shagalinka cikin duniya,
Duk ba abin da zai tam maka,
Gidan tara kake, gani kuma nike,
Maganan kau duk haka tat tabbata,
A nan na yarda da Babba na Ƙofar gabas. ”
A
wannan misalin, duk da yake Shata bai ambaci cewa, magani aka ba shi ya sha ko
ya shafa ba, duban da aka yi masa, Malamai sun lissafa shi a matsayin wani babban
rukuni na magani, (Bunza 1995). A waƘar Gagarabadau kuma Shata ya
kawo misalin wani magani na kariya inda yake cewa:
Aradu
na sha magani Nadadale ne ni
yanzu
wuqa ba ta tava ni,
sai
ya na faxin, Kushegere,
yanka
kushegere, Tsii!
4.3.3 WaƘoƙin Maza
Wannan
rukuni ya Ƙunshi
waƘoƘin da wasu makaɗan
Hausa suke yi don wasa gwarzayen da suka yi fice a wasanni kamar dambe ko
kokawa ko tauri da dai sauran su. Jigon magani yana taka muhimmiyar rawa a irin
waɗannan
waƘoƘi domin duk wata
bajinta da namiji zai nuna za a fahimci yana tinƘaho ne da maganin Ƙarfi ko na juriya
ko na buwaya. Shi kuma wanda za a kushe, akan nuna duk da maganin da ya mallaka
bai kai gwarzon makaɗin ba. Ana iya ganin irin
wannan misalin a waƘar
Jikan Bagwariya (makaɗin Tauri) ta Mamman Ɗanturwa.
“Gamon da mukai
a cikin Zarumawa, xan Turwa
Rannan abun ya
ba mu tausai
Na ga abun
tausai a dawa
Rannan na ga
abun kunya
Uban wani ya
sheqa da gudu
Wani na gudu da
kayan layu
Ya kwance kambuna
ya watsar
Ca!
Mamman, xan Turwa.
Layu
da kambu wasu hanyoyi ne na sarrafa magani a al’adar Hausawa. Kai tsaye da zarar
an gan su to an san magunguna ne da Hausawa ke mu’amala da su. Ba abin mamaki
ba ne hoton su ko amfani da su a matsayin magani ya fito a irin waɗannan
waƘoƘi.
4.3.4
Fanɗararrun WaƘoƘi
Malaman
adabin Hausa musamman masana waƘoƘin baka sun keɓe
wani rukunin waƘoƘi da suka kira fanɗararru.
An laƘaba
musu wannan suna ne bisa la’akari da irin mutanen da ake yi wa waƘa da kuma Ƙyamar da al’uma ke
yi na irin abin da ya sa ake yi musu waƘar. Misalin irin
waɗannan waƘoƘi sun haɗa da na ɓarayi da ‘yan caca. Gwarzayen
da ake yi wa irin waɗannan
waƘoƘi ba su kan yi
fice ta yadda har za a yi musu waƘa
sai sun haɗa da magani. Don
haka dole ne yabo ta fuskar maganin ya yi tasiri a waƘoƘin nasu. Misali,
Gambu mai waƘar
ɓarayi yana yaba
wani gwarzonsa Arzika da cewa:
“Wata rana an tashe shi Lolo
Naj ji Zabarmawa na ta Zaino! Zaino!,
Zaino kowa ka cewa,
Ban san da Zabarmanci sannan,
Naj ji Nuhwawa na ebeci!
Ban san da Nuhwanci ko kwabo ba,
Naj ji Hulani na hwaɗin
gujjo!
Ba jin Hillanci nikai ba,
Sai ga Hausawa irin mu
Naj ji suna eho! Ɓarawo!
Nac ce ‘an yi ɓarna’
Wancen bawa ba kai shikai ba.
Na dubi dut rutsun kasuwan nan,
Sai shina tahiya tai yanga-yanga!
Hay yas shiga jirgi lahiya lau,
Wane jihwa ko bugawa!
Sai dai nuni ɗan
gaton uwa,
Nac ce biya mallanmanka Arzika
Sun cika aiki babu wasa.”
A
wannan ɗan waƘa Gambu ya umurci Arzika da
ya biya malaman da suka ba shi maganin ɓacin rana domin
aikin nasu ya yi kyau, an ga sakamako. Ya yi sata cikin kasuwa, aka tayar da
shi amma aka kasa yi masa komai har ya ɓace.
Waɗannan
kaɗan
kenan daga cikin ɗimbin misalan da za a iya
hangowa na tasirin da magani yake da shi a wannan rukuni na adabin bakan Bahaushe.
5.0
KAMMALAWA
HaƘiƘi wannan nazari ya
tabbatar muna da cewa, dangantakar da ke tsakanin adabin baka na Bahaushe da
magani tamkar ta tsoka da jini ce. A taƘaice, ba a iya
raba su. Idan Bahaushe bai tanadi magani don kare kai ko cutarwa ko kuma biyan
wasu bukatocin rayuwa ba, to dole ya nema saboda ciwo wanda yake ɗauka
a matsayin babban maƘiyi.
Haka kuma idan har adabin zai amsa sunansa na hoton rayuwar al’uma, (wanda ya
amsa ɗin)
to dole ne ya ɗauko maganin Bahaushe domin
rayuwar Hausawa ba ta taɓa gudana ba tare da magani
ba. An tabbatar da haka ne a wannan nazari, ta ɗaukan adabin baka
Bahaushe a matsayin mizanin awo. Nazarin ya leƘa rassan adabin
bakan guda uku, wato Zube, da Maganganun azanci da kuma Raha. A kowane ɓangare
an sami misalai da suka nuna yadda sha’anin magani yake watayawa. A rukunin
zube a an leƘe
tasuniya da almara. A maganganun azanci aka zaƘulo magani a Karin
magana. Ta ɓangaren raha kuma, an kawo misalai daga waƘoƘin jama’a da na
maza da kuma cikin fanɗararrun waƘoƘi. Kenan, idan da
za a auna duk wani ginshiƘin
rayuwar Bahaushe kamar magani a adabi, ana ɗammahar haka za a
ga ya wataya, domin ya ba adabin dama ya amsa sunansa.
6.0
MANAZARTA
Ahmad,
I. A. (1984) “Cututtukan Ciki da Magungunansu.” Kundin Digiri na Farko,
(B. A. Hausa) Jami’ar Bayero,
Bunza,
A.M. (1990), “HayaƘi Fid Da
Na Kogo: (Nazarin Siddabaru Da Sihirin Hausawa)”, Kundin Digiri na Biyu (M.A.
Hausa), Jami’ar Bayero, Kano.
Bunza, A. M. (1991) “Sharhin
Ciki da Wajen Littafin Ruwan Bagaja.”
MaƘalar
da aka gabatar a taron Makon Hausa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Bunza, A.
M. (1995) “Magungunan Hausa a Rubuce: (Nazarin Ayyukan Malaman Tsibbu),” Kundin
digiri na uku (Ph.D Hausa) Jami’ar Bayero, Kano.
Bunza, A. M. (2008) “Asirran Sata a Riwayar Gambu” Takardar da aka gabatar a
taron
Ƙara
wa juna sani na Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo
Sakkwato.
Ɗangambo,
A. (1984) Rabe-Raben Adabin Hausa Da Muhimmacinsa Ga Rayuwar Hausawa. Kano,
Triumph Publishing Company.
Gusau, S. M.
(1984) “Adabin Hausa na Gargajiya: ma’anarsa da Yanaye-yanayensa.” MaƘalar
da aka gabatar a taron raya Harshen Hausa wanda Ƙungiyar
Hausa ta Makarantar Tarbiyyar Malamai Mata ta Arabiyya ta Gusau ta shirya.
Gusau,
S. M. (2008) Dabarun Nazarin Adabin Hausa,
Kano, Benchmark Publishers Limited.
Sayaya, A. S. (2009) “Wasan
Tauri a Ƙasar
Katsina” Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa), Jami’ar Usmanu Danfodiyo,
Sakkwato
Tremearne,
A. J. N. (1913) Hausa Superstitions And Customs,
Tukur,
A. (1988) “Nazari a
a
Bahaushiyar Al’ada.” Kundin Digiri na Farko, (B. A. Hausa) Jami’ar Bayero,
Umar,
M. B. (1987) Dangantakar Adabi da Al’adun
Gargajiya. Triumph Publishing
Company,
Yahya,
A. B. (1994) “
Aka gabatar a taron Ƙara wa juna sani
wanda Ƙungiyar
marubuta da manazarta
waƘoƘin Hausa ta
gudanar a Sakkwato.
Yahya,
A. B. (1997) Jigon Nazarin WaƘa. Fisbas Media
Services,
Yahaya, I. Y.
(1977) Tatsuniyoyi da Wasanni, (littafi na uku) Oxford University
Press,
Yahaya,
I. Y. (1988) Hausa A Rubuce: Tarihin
Rubuce-Rubuce Cikin Hausa,
Northern Nigeria Publishing
Company.
[1] Adabin gargajiya shi aka yi bayani da Adabin da Hausawa suka gada
kaka da kakanni. Shi kuwa
adabin zamani, shi ne wanda ya zo a rubuce
bayan da Hausawa suka sami hanyar rubutu.
[2] Don ganin cikakkiyar tatsuniyar dubi littafin Tatsuniyoyi da Wasanni, (littafi na uku) na Ibrahim Yaro Yahaya.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.