TAMBAYA (86)❓
Aslm. Iftar mubaraq. Inada tambaya su wadanda suke kamar a norway ya zasuyi azumi, tunda kafin suga faduwar rana sai sunyi wata shida
AMSA❗
Alhamdulillah
Allah Subhanahu wata'ala yace
( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا
كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ
تَتَّقُونَ )
البقرة
(183) Al-Baqara
Yã ku waɗanda
suka yi ĩmãni! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke daga gabãninku,
tsammãninku, zã ku yi taƙawa,
Don haka su ma Norwegians hukuncin ya hau kansu duk da cewar
zasu share darare 180 (rabin shekara) a cikin dare ba tare da sunga ko da
kyallin hasken rana ba
"Allah daya gari ban-ban" karin maganar bahaushe
Nasha cin karo da tambayoyi daga dalibaina na secondary
school kamar: "To yan kasar Norway din zasu share wata 6 suna bacci ne, su
farka idan safiya tayi ?", yan anguwarmu sukan tambayeni "To a cikin
dare kenan suke gudanarda bukukuwan karamar sallarsu idan watan 1 ga Shawwal ya
kama ko kuma hakuri suke da bikin sallah tunda yazo musu a cikin dare ?"
Bari na amsa tambayar "Musulman da suke a kasar Norway
ta yaya zasuyi azumi tunda kafin suga faduwar rana sai sunyi wata 6 ?"
A shekarar 1980 babu musulmai sosai a yankin Arctic Circle
(doron duniya daga saman kudanci, domin gane bayanin: ka kaddara a hannunka
akwai kwai dafaffe to can saman tudunsa shine kamar yankin kasashen Arctic
kasar Norway tana cikinsu yayinda kasansa kuma shine arewacin Antarctic),
musulmai sun fara hijira ne daga kasashen Somalia, Iraq, Pakistan zuwa kasashen
Sweden, Norway dakuma Finland, wannan shine silar yawaitar al'ummar musulmai a
kasashen da ake share watanni a kalla 6 ba'aga hasken rana ba, haka watanni a
kalla 6 a cikin dare
Wani musulmi mai suna Hassan Ahmed, wanda aka yiwa irin
wannan tambayar a garin Tromsø, wanda gari ne a tsakiyar kasar Norway 350
kilometers daga Arctic Circle, mutanen garin yawancinsu yan gudun hijirane daga
kasar Somalia, da yawan musulmai bai wuce 1,000
ba, wanda Hassan yayi bayanin cewar rana bata faduwa har watan Ramadan
ya wuce
Ya ci gaba da cewa "Munada fatawowi guda 2 da malamai
suka bamu kodai mu dinga azuminmu da kasar musulmai dake makotaka damu ko kuma
mu dinga amfani da lokacin Makka"
An tambayi Sandra Maryam Moe, wadda ta bata dade da amsar
musulunci ba (revert) wadda ta kasance manager ce a Tromsø community center
tace "Tunda a cikin dare zamu dinga rayuwa har watan Ramadan dinnan ya
kare, sai muka zabi amfani da lokacin Makka"
Hakan yana nufin idan rana ta fito karfe 5:00 am (na asuba)
a Makka to mutanen Tromsø sai su fara azuminsu daga karfe 5:00 am irin na kasar
Norway (Norwegian time)
"Dadin dadawa hakan yafi kwanciyar hankali da nutsuwa
garemu saboda Makka suna da kayyadadden lokacin (timetable) na fitowar rana da
kuma faduwarta hakan yasa da sallar da azumi suka daidaitu" inji Sandra
Maryam Moe
A daren karfe 7:07 pm na Tromsø musulmai sukan tarune a
masallachin Alnor suyi iftar dinsu alhalin suna shan ruwa amman suna ci gabada
ganin hasken rana ta cikin windunan masallachin
Moe ta ci gaba da cewa "Kullum da daddare mukan cika
anan musha ruwa tare muyi sallah tare, lokaci ne na annashuwa a garemu a gaba
daya watan Ramadan din"
Wani zaice to meyasa su wadannan kasashen suke samun irin
wadannan lokatai, sai muce ai saboda karkacewar da duniya tayi na 23.5° shine
yasa ake samun yanayi guda 4: Summer: zafi, sai Winter: sanyi, da kuma Autumn:
rani, sai kuma Spring: damina. A shekara kusan gaba daya sassan duniya guda 4
(banda Arctic da Antarctic) suna karban hasken rana kai tsaye ta yanda idan
hasken rana ya hasko yankin arewa, su kuma kudancin duniya zasu ji sanyi haka
kuma idan ta haske kudu, su kuma yankin arewa zasu ji zafi, wannan shine
dalilin da yasa kasar Norway take share watanni 6 kafin rana ta haskota hakama
watanni 6 kafin dare ya gushe. Allahu Akbar ! Dukkan godiya ta tabbata ga Allah
Ubangijin mafadan rana 2 da mahudanta 2
To a takaice dai wannan shine amsar lokacin da yan kasar
Norway suke shan ruwa bayan sun kammala azumi alhalin basa ganin fitowar rana
sai an share watanni 6 haka kuma idan rana tayi basa kara ganin faduwarta sai
wasu watanni 6 din sunyi
Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.