Sakwara
i. Doya
ii. Man Gyaɗa
iii. Ruwa
Wannan nau’in abinci da doya ake yin sa. Ya sha bamban da sauran nau’o’in tuwo da aka yi bayani a sama. Za a fere doya ne sannan a dafa ta. Bayan ta dafu sai a wanke turmi sannan a riƙa sanya doyar ciki a riƙa kirɓawa. Za a riƙa ƙara ruwan zafin da aka dafa doyar da shi yayin da ake wannan kirɓi. Haka za a ci gaba har sai ta haɗe gaba ɗaya ta yi danƙo. Da zarar haka ya samu, to an kammala sakwara kenan. An fi cin sakwara da jar miya ko ganye. Duk da haka, ana iya cin ta da wasu nau’o’in miya na daban.
Amala
i. Kwalfar Doya
ii. Kanwa
iii. Ruwa
Citation (Manazartar Littafin): Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.
Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736
You can also write an email to:
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.