Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
Wasanni
a Ƙasar
Hausa
Sadaukarwa
Wannan aiki sadaukarwa ce ga
masu tunani na gari da karɓar shawarwari na gari da
kuma aikata aiki na gari. Babban goron da marubutan ke buƙata shi ne addu’ar alkairi, suna raye da
bayan ransu.
ƘUMSHIYA
Sadaukarwa 3
Godiya 17
Muƙaddima 18
Tsokaci 19
Ta’aliƙi 20
Allah San Barka 21
Jinjina 22
Gabatarwa 23
Kalmomin Fannu
Babi Na Ɗaya
Gabatarwa
1.0 Shimfiɗa
1.3 Muhimmancin Bincike
1.4 Waiwaye Adon Tafiya
1.5 Ma’anar Wasannin
Gargajiya
1.6 Muhimmancin Wasannin
Gargajiya
1.6.1 Horo da Gyaran Hali
1.6.2 Hannunka-Mai-Sanda
1.6.3 Jarunta Da Bajinta
1.6.4 Motsa Jiki
1.6.5 Hikima Da Dabara
1.6.6 Bin Doka Da Ƙa’ida
1.6.7 Tunani da Zurfafa Shi
1.6.8 Ilimantarwa Da
Taskance Harshe
1.6.9 Nishaɗi
1.6.10 Hana Yawon Banza
1.6.11 Ƙarfafa Danƙon
Zumunci
1.6.12 Wayewa Da Iya Magana
Cikin Jama’a
1.6.13 Bayyana Muradin Zuci
1.7 Naɗewa
Babi Na Biyu
Tsarin Rayuwar Hausawa
2.0 Shimfiɗa
2.1 Tsarin Zamantakewar
Hausawa
2.2 Tsarin Shugabancin
Hausawa
2.3 Addinin Hausawa
2.4 Hausawa A Duniyar
Zamaninmu
2.5 Naɗewa
Babi Na Uku
Rabe-Raben Wasannin Ƙasar Hausa
3.0 Shimfiɗa
3.1 Iren-iren Wasanni Ta
Fuskar Yanayin Aiwatar Da Su
3.1.1 Wasan Magana
3.1.2 Wasan Kurma
3.2 Rabe-Raben Wasanni Ta
Fuskar Masu Gudanarwa
3.2.1 Wasannin Yara
3.2.1.1 Wasannin Yara Maza
3.2.1.2 Wasannin Yara Mata
3.2.1.3 Wasannin Yara Maza
Da Mata
3.2.2 Wasannin Manya
3.2.2.1 Wasannin Manya Maza
3.2.2.2 Wasannin Manya Mata
3.2.3 Wasanni Gama-gari
3.3 Rabe-RabenWasanni Ta
Fuskar Lokacin Gudanarwa
3.3.1 Wasannin Rana
3.3.2 Wasannin Dare
3.3.3 Wasanni Marasa Ƙayyadadden Lokaci
3.4 Rabe-raben Wasanni Ta
Fuskar Yanayin Gudanarwa
3.4.1 Wasannin Tsaye
3.4.2 Wasannin Zaune
3.5 Rabe-Raben Wasanni Ta
Fuskar Sakamako
3.5.1 Wasanni Masu Sakamakon
Duka
3.5.2 Wasanni Masu Sakamakon
Ele/Zolaya
3.5.3 Wasanni Marasa
Sakamako
3.6 Wasannin Masu Waƙa Da Marasa Waƙa
3.7 Wasanni Masu Jagora Da
Marasa Jagora
3.8 Wasanni Masu Kayan Aiki
Da Marasa Kayan Aiki
3.9 Naɗewa
Babi Na Huɗu
Tasirin Zamani a Kan
Wasannin Hausawa
4.0 Shimfiɗa
4.1 Dalilan Dusashewar
Wasannin Gargajiya
4.1.1 Ilimin Addini
4.1.2 Ilimin Boko
4.1.3 Samuwar Fina-finan
Hausa
4.1.4 Samuwar Yanar Gizo
4.1.5 Samuwar Kafafen Sada
Zumunta Na Yanar Gizo
4.1.6 Lalaci/Ganda
4.1.7 Hani Daga Iyaye
4.1.8 Rashin Ƙarfafawa Daga Shugabanni
4.1.9 Dushewar Ƙungiyoyin Samari
4.2 Sauye-Sauye A Wasannin
Gargajiya na Hausa
4.3 Sababbin Wasanni A Ƙasar Hausa
4.4 Naɗewa
Babi Na Biyar
Wasannin Yara Maza
5.0 Shimfiɗa
5.1 Taɓaɓɓe
5.2 Goga
5.3 Gori/Koɗi 1
(Na Gargajiya)
5.4 Gori/Koɗi 2
(Na Zamani)
5.5 Langa
5.6 Sabis
5.7 Guro/’yar Guro
5.8 A Sha RuwanTsuntsaye
5.9 Jini Da Jini
5.10 Ba Mu Kuɗinmu
5.11 Ga Zabo Zai Mutu
5.12 Ɓelunge
5.13 Allazi Wahidun
5.14 Cincin Sakatum
5.15 Balbela-balbela
5.16 Noti-Noti
5.17 Damo Riya Damo
5.18 Allah Reni
5.19 Dokin Almajirai
5.20 Ƙwanƙwalati
5.21Ɗanduƙunini/Ɗanduƙununu
5.22 Jirgi 2
5.23 Yaƙi
5.24 Babana Ya Saya Min Ƙwallo
5.2 5 Rijiya
5.26 Taka Ɓurme
5.27 ‘Yar Ganel
5.28 Mai Dawa
5.29 Ɓigo
5.30 Dokin Kara
5.31 ‘Yar Cille
5.32 Wur-Wur
5.33 Fanka
5.34 Kofi
5.35 ‘Yar Ɗille
5.36 Baba Mai Gadi
5.37 Bindiga
5.38 Jirgi 1
5.39 Karan Tsallake
5.40 Sallar Kwaɗi
5.41 Dirƙe-Dirƙe
5.42 Tarkon Horon Wawa
5.43 Gwanjo-Gwanjo
5.44. Motar Kara
5.45 Motar Langa-langa
5.46 Afajana
5.47 Danda Dokin Kara
5.48 Alhajin Ƙauye
5.49 Maiƙiriniya
5.50 Tashi Mai Kwaɗayi
5.51 Baran Baji
5.52 Zule-Zuleyya
5.53 Ni Chadi Zan Tafi
5.54 Ɗanɓera
5.55 Ɗantsoho Mai Cin Bashi
5.56 Tsoho Da Gemu
5.57 Taya
5.58 Garere/Gare/Gare-gare
5.59 Baban Dudu
5.60 Tashi Wali
5.61 Robali/Kyauro - ‘Yar
Jifa
5.62 Robali/Kyauro‘Yar Taru
5.63 Ka Yi Rawa
5.64 Na Ci Na Kasa Tashi
5.65 Malam Ka Ci Kusa
Babi Na Shida
Wasannin Yara Mata
6.0 Shimfiɗa
6.1 Carman-Dudu
6.2 A Sha Ruwa
6.3 Samodara
6.4 Basha
6.5 Ɓakutu Mai Babban Ɗuwawu
6.6 Matar Nakarofi
6.7 Maimuna Ta Yi Ciki Ga
Goyo
6.8 Ina Da ‘Yata
6.9 Salamatu
6.10 Wasar Gora-Gora
6.11 Hajiyar Ƙauye
6.12 Mai Ciki
6.13 Ruwa Mai Malale
6.14 ‘Yar Ramel
3.15 Carafke
6.16 Digi-Digi
6.17 Ɗan Balum-balum
6.18 Babunna
6.19 A Fim-Fim-Fim
6.20 Bena
6.21 Kis-Kis-Kis An
Kas-Kas-Kas
6.22 ‘Yar Gala-Gala
6.23 Ladidin Baba
6.24 Na Ɗaura Kallabi
6.25 Laula Amarya
6.26 Ɓarawo Me Ka Sata?
6.27 Kin Zama
6.28 Rana Ta Fito Gabas
6.29 Nayaya?
6.30 O Aliyo
6.31 Tafa-Tafa
6.32 Jallu Wa Jallu
6.33Gabana Gaba Nawa
6.34 Ina Da Cikin Ɗan Fari
6.34 Kwalba-Kwalba Dire
6.35 Rurujina
6.36 Ruwan Ƙauye
6.37 Daƙu Fara
6.38 A Fiffigi Zogale
6.39 Ɗanlele
6.40 Gamuna
6.41 Ragadada
6.42 Kande Mahaukaciya
6.43 Kallo Da Ido
6.44 Ni Kura-Kura
6.45 ‘YarƘwado
6.46 Dinga-Dinga
6.47 Cin Dawo
6.48 Ba Dela Ba Kande
6.49 Odada
6.50 Ni Madara Ni Zuma
6.51 Ni Mota Nake So
6.52 Amali Kande
6.53 Ayye Rashidalle
6.54 Mai Naƙiye
6.55 ‘Yar Ato
6.56 Ayye Mama
6.57 Carmama
6.58 A CikinWannan Rana
6.59 Inna Leliya
6.60 Kaɗa
6.61 Karya Gaɗiɗi
6.62 Salo-Salo
6.63 Alo NaTaro Na Tattaro
6.64 Tattaba-Tattaba
6.65 Yaraye Dije
6.66 Ke Kika Je Gidansu Direba
6.67 Jar Miya
6.68 Afurka-Afurka
6.69 Kwalliyar La’asar
6.70 Sama Indo
6.71 Son Makaru
6.72 Iye Nanaye
6.73 Ruwaye
6.74 Gyara Zamanki Kamar Ba
Ke Ba
6.75 Cillo-Cillo
6.76 Lokos
6.77 Mama Ta Ƙi Shillona
6.78 Farin Zoben Azurfa
6.79 Ɗura-Ɗura
6.80 Mamin Jatau
6.81 Soyayya Iri-Iri Ce
6.82 Goɗiyallare
6.83 Gariye
6.84 Sadam
6.85 Tambo
6.86 Shanyar Kuluri
6.87 Goye-Goye
6.88 Goyon Kura
6.89 Goyon Baya
6.90 Kifi-Kifi
6.91 Faɗi
Mana
6.92 Tsakiyata Ta Tsinke
6.93 Ga Mairama Ga Dauda
6.94 TamaYakiTama
6.95 Rabi Da Audu
6.96 Ga KuɗinToshinki
Na Bara
6.97 Ɗan Mutumi-Mutumi
6.98 Ɗanmaliyo-Maliyo
6.99 Yau Na Zama Baran Mata
6.100 To Iya
6.101 Ni Karkashi
6.102 Sillen Kara
6.103 Taɓarya
Babi Na Bakwai
Wasannin Tarayya
7.0 Shimfiɗa
7.1 ‘Yartsana
7.2 Na Ɗiba
7.3 Tuwon Ƙasa
7.4 Biyar Ko Goma
7.5 Lakkuma-Lakkuma Lale
7.6 Kasko-Kasko
7.7 Cankuloto-Kuloto
7.8 Talili Tali Yambo
7.8 Ɗan Kurege
7.9 Efa-Efa
7.10 Dundunge
7.11 Sai Ka Yi Rawa A Nan
7.12 Tserel
7.13 Ba Za Ku Ga Tafiyar
‘yata Ba
7.14 Ɓoyel
7.15 O Maciji
7.16 GidanKurciya
7.17 Waran Warash
7.18 Za Ni
Za Ni Ye
7.19 ‘Yar Sarki
7.20 Ƙwaƙwale
7.21 Kumbukululu
7.22 Zuciyar Mai Tsumma
7.23 Ɗakin Tsuntsu
7.24 ‘Yar Canka
7.25 Caccayya
7.26 Allah Koro Ruwa
7.27 Hajijiya
7.28 ‘Yar Akuyata
7.29 Dunguren Kule
7.30 ‘Yar Cake
7.31 Lasko
7.32. Sunkuya Dundu
7.34 Na Ƙale
7.35 Na Jej Je
7.36 Odi-Odi
Babi Na Takwas
Wasannin Manya
8.0 Shimfiɗa
8.1 Girjim
8.2 Uku Saɓi
8.3 Gwauro
8.4 Boka Kake Ko Malami?
8.5 Jatau Mai Magani
8.6 Wandara A Sha Maganin Ƙaba
8.7 Macukule
Babi Na Tara
Kammalawa
9.0 Shimfiɗa
9.1 Sakamakon Bincike
9.2 Kammalawa
Manazarta
Fihirisan Kalmomi
Godiya
Da sunan Allah Mai Rahama
Mai Jin ƙai. Tsira da amincinSa su ƙara tabbata ga mafificin halittu Manzon
tsira Annabi Muhammadu (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi). Samun ƙwarin guiwa da jajircewar kammala wannan
ɗan ƙwarya-ƙwaryar
Littafi na nuni ga ikon Allah da taimakonSa dangane da aikin. Muna ƙara maSa godiya dangane da lafiya da
juriya da Ya ba mu har Littafin ya zama abin da yake a yau.
Ba za mu taɓa
mantawa da taimakon Farfesa Aliyu Muhammad Bunza da Dr. Musa Fadama Gummi da
Dr. Alamuna Nuhu da Dr. Mu’azu Sa’adu Muhammad da Malam Ibrahim Ɗalha ba. Sun sadaukar da lokacinsu domin
sanya albarka ga littafin. Da fatan Allah Ya saka musu da mafificin alkairi.
Bayan haka, muna miƙa
godiya ga dukkanin waɗanda suka taimaka da
addu’o’i da kuma Allah san barka har dai aikin wannan littafi ya kammala.
Mun gode.
Dr. Yakubu Aliyu GOBIR
Abu-Ubaida SANI
12-06-2019
Muƙaddima
Da sunan Allah Mai Rahma Mai
jin ƙai. Tsira da aminci su tabbata ga
Annabin Rahama Muhammadu ɗan Abdullahi da iyalan
gidansa da sahabbansa da waɗanda suka yi koyi da su da
kyautatawa ya zuwa ranar sakamako.
Na daɗe
ina tunanin yadda za a samu wani gawurtaccen aiki da zai harari wasannin
yaranmu maza da mata da idon basira ta yadda duniyar ilmi za ta amfana da shi.
Cikin ikon Allah, sai ga wasu masana da ban taɓa
tattaunawa da su ba kan haka, sun yi canjaras da tunanina sai na ji an yi mini
susa gurbin ƙaiƙai. Da na karanta wannan littafi na
gamsu da cewa, ruwa na ƙasa
sai ga wanda bai tona ba. Babu wai, ƙasar
Hausa zuriya ɗaya ce, nisantar wurin zama ya haifar da
bambance-bambancen al’adu da karin harshe. Dr. Yakubu Aliyu Gobir, ko ba a faɗa ba
mutumin Gobir ne, Abu-Ubaida Sani daga Bauchin Yakubu sai ga shi sun kalli
wasannin yara na ƙasar
Hausa da tunani ɗaya, ka ce gari ɗaya
ake wasannin. Wannan wata manuniya ce ga buƙatar
irin wannan aiki a duniyar karatun Hausa. Wannan giɓin
da manazartan suka cike ya cancanci ya shiga hannun ɗalibai
da malamai da manazarta Hausa domin su amfana da shi. Haƙiƙa
aikin ya aikatu, ba a yi kasala ba, ba a zure ba, ba a yi azarɓaɓi
ba, an shimfiɗa rubutun bisa ga ladabi da biyayyar karɓar
ilmi da bayar da shi. A tunaninmu na ɗaliban
al’ada da adabi wannan aiki ya cancanci babban yabo domin ba ya jin kunyar ido
huɗu da
ɗaliban
fanninsa da masu sha’awar karatunsa. Fatana shi ne, Allah Ya sa albarka, Allah
Ya yi mana jagora.
Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Harsuna da Al’adu
Jami’ar Tarayya, Gusau.
Tsokaci
Dukkan yabo da godiya sun
tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki. Tsira da
aminci su daɗa tabbata ga fiyayyen halitta, manzon
rahama, Annabi Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa, da dukkan masu koyi da
shi har ya zuwa ranar sakamako. A
matsayina na ɗalibi mai bincike da nazarin al’adun
Hausawa, na duba wannan muhimmin littafi mai suna Wasanni a Ƙasar Hausa wanda Dr Yakubu Aliyu Gobir da malam
Abu-Ubaida Sani suka wallafa. Haƙiƙa wannan wani gagarumin aiki ne mai ɗimbin
fa’ida, musamman idan aka yi la’akari da cewa littattafan da aka wallafa waɗanda
suka gabaci wannan aiki ba su yi
bakandamen tattara wasanni na maza da na mata, na yara da na manya ba a
wuri ɗaya.
Haƙiƙa
littafin bai bar wata kafa ta susar akaifa ba domin ya tattaro kusan duk
wasanni na da da kuma na yanzu.
Fatar da nake yi ita ce Allah ya albarkaci wannan gagarumin
aiki nasu, ya kuma saka masu da mafificin alheri. Amin!
Dr. Musa Fadama Gummi
Department of Languages and
Cultures
Federal University Gusau
Ta’aliƙi
Littafin ‘Wasanni a Ƙasar Hausa’ ƙari
ne cikin jerin littattafan da malamai da manazarta suka samar domin taskace
wani ɓangare
na rayuwar Hausawa jiya da yau. Bisa dukkan alamu, an gudanar da ƙwaƙƙwaran
bincike musamman ziyarar gani da ido domin neman waɗannan
wasanni game da yadda suke da yadda ake aiwatar da su. Wani abin ban sha’awa da
littafin shi ne, an fasalta wasannin ƙasar
Hausa bakin gwargwado ta fuskar jinsi da shekaru da yanayin aiwatarwa da lokaci
da yanayin wasannin. Hakan ya sa aka sami bambanci tsakaninsu da sauran
takwarorinsu littattafan wasannin Hausawa da suka gabaci wannan. Babu shakka
littafin zai taimaki malamai da masu nazarin wasannin Hausawa da matani a
kammale na nau’o’in wasanni waɗanda
suke daga ɓangarori daban-daban na ƙasar Hausa.
Hausawa suna cewa: “Wasa ba
faɗa
ba”. Tabbasa marubutan wannan littafi sun yi ƙoƙari wurin samar da aiki wanda zai ƙara bunƙasa
bincike a fannonin nazarin harshen Hausa, musamman a wannan zamani da wasannin
gargajiya na Hausawa suke ɗaukar fasali irin na
wasannin zamani. A gaishe da Malam Dakta Yakubu Aliyu Gobir da Malam Abu-Ubaida
Sani da ƙoƙari.
Allah ya sa littafin ya zama mai amfani ga masu karatu da nazari, ya kuma zama
abin yin madogara a fagen nazarin ilimi a matakai daban-daban.
Dakta Alamuna Nuhu
Tsangayar Fasaha,
Sashen Nazarin Harsunan
Nijeriya da Kimiyyar Harshe,
Jami’ar Jihar Kaduna,
Kaduna.
Allah San Barka
Wasanni a Ƙasar Hausa, wani littafi ne kandamin a
sha a yi wanka, wanda aka rubuta shi tare da tsara shi bisa kyakkyawan bincike
da nazarce-nazarcen bayanai masu tarin yawa. Ya shafi wani muhimmin fanni na
bayyananniyar al’adar
Bahaushe. Dalili kuwa, kusan ana iya cewa an tattaro wasanni na zamanin da, da
kuma na zamanin yanzu tare da hasko waɗansu
sauye-sauye waɗanda zamanin ya kawo. Babu shakka
littafin ya fito da wasu abubuwa tare da ƙara
haske dangane da abin da ya shafi wasannin Bahaushe. Marubutan sun yi bayanai
da suka shafi wasanni a ƙasar
Hausa ta hanyar rarraba su bisa la’akari
da adadin shekaru ko jinsin waɗanda ke gudanar da wasannin.
Littafin na ɗauke da kammalallen bayanai game da
wasannin. Ya faro tun daga bayyana ma’anar wasanni da amfaninsu har zuwa
bayanin yadda ake gudanar da su dalla-dalla.
Bayan haka, marubutan sun
binciko wasu abubuwa masu nuna alaƙa ko
dangantaka da ke tsakakanin wasanni da rayuwar Bahaushe. Bayyana waɗansu
abubuwan azanci da hikima na Bahaushe da suka shafi wasanninsa sun ƙawata littafin. Babu shakka wannan
Littafi zai taimaka ga fagen ilmi. Zai kuma taimaka wa ɗalibai
na kowane mataki daga sakandare zuwa jami’o’i, malamai da sauran al’umma da ke
sha’awar nazarin al’adun Bahaushe. Na yaba tare da jinjina wa marubutan da
fatan Allah ya ƙara
taimako da ƙarfin guiwa. Amin.
Dr. Mu’azu Sa’adu Muhammad
Department of Nigerian
Languages
Faculty of Humanities
Sule Lamido University Kafin
Hausa
Jigawa State.
Jinjina
Gaskiyar Hausawa da suka
aminta da cewa: “Sanin wurin bugu shi ne ƙira.” Samar da wannan littafi mai
suna Wasanni a Ƙasar
Hausa da Dr. Yakubu Aliyu Gobir da Malam Abu-Ubaida Sani suka yi, bai zo mana
da mamaki ba, duba da irin saninsu game da abubuwan da suka shafi al’adun Hausawa da kuma irin
yadda suka goge wajen karantar da al’adun na Hausawa. Nau’o’in wasannin da littafin ya
tattaro, shi ya nuna gagarumin aikin zai
taimaka wa malamai da ɗalibai a matakan ilimi
daban-daban (firamare zuwa jami’a). Don haka, samun wannan littafi a wannan
lokaci abu ne da ya zo daidai lokacin da ake buƙata.
Wato dai, tamkar wani kaya ne da ya tsinke a gindin kaba.
Allah Ya ƙara wa marubuta wannan littafi basira da
juriya. Muna roƙon
Allah Ya sa littafin ya zama mai amfani ga al’umma baki ɗaya;
Ya kuma ci gaba da ɗaukaka Hausawa da karatun
Hausa. Amin.
Malam Ibrahim Ɗalha,
GDSSS, Birnin Kudu,
Ministry of Education
Science & Technology, Dutse,
Jigawa State.
Gabatarwa
Haƙiƙa
wasanni sun kasance wani ɓangare na rayuwar ɗan
Adam. Wannan kuwa bai tsaya ga kan Hausawa ba kawai, ya shafi dukkanin al’ummun
duniya da ke ƙasashe daban-daban.
Sai dai akan sami bambance-bambancen salo da siga na waɗannan
wasanni, wanda hakan ya danganta ga al’ada da yanayin wurin zama na masu wannan
wasa. Kai! Ba ma ‘yan Adam ba kaɗai,
akwai halittu da dama da ke wasanni iri-iri a tsakanin junansu. Sun haɗa da
birrai da karnuka da shanu da ma wasu dabbobin na daban. Baya ga haka, akan
samu wasa tsakanin jinsin halittu mabambanta. A irin haka ne ma akan samu ɗan
Adam na wasa da dabbobi irin su karnuka ko birrai ko dawaki da dai sauransu.
Salailan wasannin da Hausawa
suka gada tun iyaye da kakanni na fuskantar dusashewa, tamkar dai sauran
al’adun Hausawan. Wannan na faruwa ne sakamakon dalilai masu dama waɗanda
za a iya taƙaita su da furucin
Tasirin zamani. Lura da wannan ƙoƙarin ɓacewa
da mafi yawan wasannin Gargajiya ke yi, akwai buƙatar
killace su wuri guda a matsayin wani kundin da zai kasance abin waiwaita a
kodayaushe. Yin hakan zai sanya ko da wasannin sun gushe a zamani, za su
kasance a killace har Mahadi.
Wannan Littafi ya yi nasarar
tattaro nau’ukan wasannin gargajiya har guda ɗari
biyu da goma sha huɗu (214). An raba aikin zuwa
babuka har guda tara. Babi na farko ya kasance shimfiɗa ga
aikin. A ciki ne kuma aka kawo amfanin wasannin gargajiya. Daga ciki akwai:
horo da gyaran hali, da koyar da jarumta, da koyar da hikima da dabara, da
motsa jiki da dai makamantansu.
Babi na biyu ya waiwaici
tsarin rayuwar Hausawa a jiya da kuma yau. Wannan ya haɗa da
addininsu da kuma tsarin zamantakewa da auratayya. Hakan ya kasance ƙarin haske game da al’ummar da aka yi rubutun
kansu. Wato dai tamkar fitila ce ta haska al’ummun
da ake magana kansu domin a ji daɗin ɗaukar
hoton zuci yayin da ake bayanin ire-iren wasanninsu.
A cikin babi na uku, an yi ƙoƙarin
kawo nau’ukan wasannin gargajiyan
Bahaushe. An yi hakan ne ta hanyar la’akari
da alƙalumma daban-daban wurin raba wasannin.
Waɗannan
matakai sun haɗa da yanayin gudanar da wasannin, da
lokacin gudanar da su, da masu gudanar da su da dai makamantansu. A ƙarƙashin
kowane rukuni an kawo taƙaitaccen
bayani mai gamsarwa tare da misalai domin ƙarin
haske.
Kamar dai yadda aka nuna a
baya, zamani ya yi tasiri sannan yana ci gaba da yin tasiri kan wasannin
gargajiya. Babi na huɗu ya waiwaici irin tasirin
da zamanin ya yi kan wasannin. A cikin babin an nazarci dalilan da suka haifar
da dusashewar wasannin gargajiyar Bahaushe. Sun haɗa da
samuwar ilimin addini da na boko da samuwar yanar gizo da kafafen sadarwa na
yanar gizo da dai sauransu. Sannan babin ya dubi irin sauye-sauye da aka samu
ga wasu wasannin gargajiyar ta fuskar yadda ake gudanar da su. Daga ƙarshe kuma sai babin ya nazarci wasu
sabbin wasannin gargajiya da Bahaushe ya tsinta a sakamakon Tasirin zamani a
kan al’adunsa.
Daga babi na biyar kuwa, har
zuwa na takwas, an kawo jerin wasanni ne tare da bayanin yadda ake gudanar da
su. Babi na biyar na ɗauke da wasannin yara maza
guda sittin da biyar (65) tare da bayanin kowanne. Babi na shida kuwa wasannin
yara mata ya ƙunsa, guda ɗari
da uku (103). Babi na bakwai kuwa ya ƙunshi
wasanni ne na tarayya tsakanin yara maza da mata. Adadinsu ya kai talatin da
shida (36). Sai kuma babi na takwas da ya ƙunshi
wasannin manya, waɗanda adadinsu ya kasance
bakwai (7) kacal.
Babi na ƙarshe kuwa, wato na tara, yana ƙunshe ne da jawaban kammalawa. Bayan an
kawo jerin manazarta, sai kuma aka biyo baya da ratayen waɗannan
wasannin Gargajiya guda ɗari biyu da goma sha huɗu
(214) cikin tsararran jadawali. An yi hakan ne domin samar da haske ga mai
karatu ko bincike, yadda zai samu bayanai masu muhimmanci kan kowane wasa kai
tsaye. Ga kowane wasa, an bayyana abubuwa da suka haɗa
da:
i. Sunan wasa
ii. Masu wasa
iii. Rukunin wasa
iv. Kayan aiki
v. Amfanin wasa
vi. Sakamakon wasa (Sakamako mai kyau yayin da aka yi abin ƙwarai, ko kuma mummunan sakamako yayin
da aka ci karo da ƙa’idojin wasa)
Dr. Yakubu Aliyu GOBIR
Abu-Ubaida SANI
15-06-2019
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.