Alamomin Cikawa Da Imani

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Shin wasu alamomi ne ke nuna cewa mamaci ya cika da imani kuma shin akwai waɗanda za su shiga aljanna Ranar alqiyama ba tare da an yi musu hisabi ba?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Daga cikin alamomin akwai:

    1. CIKAWA DA KALMAR SHAHADA: saboda faɗin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam "Duk Wanda maganarsa ta karshe ta zama La'ilaha illallahu zai Shiga aljanna".

    2. MUTUM YA MUTU YANA AIKIN ALHERI: kamar sallah ko Hajji, saboda faɗin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam "Ana tashin bawa akan abin da ya mutu yana yi".

    3. IDAN MUTUM YA RASU DAREN JUMA'A KO YININTA: saboda faɗin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam "Duk Wanda ya rasu Daren juma'a ko yininta Allah zai kare shi daga azabar Kabari"

    4. IDAN MUTUM YA RASU DA GUMI A GOSHISA: kamar yadda ya tabbata a hadisin Tirmizi.

    5. Idan mutum ya yi shahada kamar mace ta mutu wajan haihuwa ko ciwon ciki ko nutsewa a ruwa ko ya mutu a ciwon Kwalara ko kare kansa ko dukiyarsa da sauransu.

    Idan aka koma can cikin littafin Ahkamul Jana'iz Sheikh Albani yakawo alamomin a farko farkon littafin. Amma wannan ana kyautatawa mutum zatone ba'a yanke hukunci kai tsaye ace mutum ɗan aljanna ne ko ace kai tsaye ya cika da imani.

    Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi Wasallam) Ya ce: "Lalle za a samu masu shiga Aljanna a cikin al'umma ta mutum dubu Saba'in, babu Hisabi ko Azaba agare su, tare da kowani dubu ɗaya akwai mutum dubu saba'in da zasu shiga Aljanna.” [Saheeh Al-jami: 5366]

    Abin da hadisin yake nufi: mutum Biliyan Huɗu da miliyan ɗari Tara (4.9B ko 4,900,000,000) Za su Shiga Aljanna Babu Komai Salin Alin.

    Waɗanda suke shiga aljanna babu hisabi sune waɗanda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya faɗesu acikin hadisi Ukasha binu Mihsan wato waɗanda suke basa camfi basa neman magani da sauransu.

    ALLAH Yasa mu dace, Yasa muna daga cikin Al'ummar Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) waɗanda zasu shiga Aljanna ba tare da Hisabi ba (Aameen)

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.