An Gano Wata Rana Mai Haske A Sararin Samaniya

    TAMBAYA (122)

    Mene ne gaskiyar binciken da masana sukai akan cewar an gano wata Rana mai haske ta daban a sararin samaniya. Hakan na nufin ba iya wannan ranar bace a saman duniya ba kenan?

    ✍️AMSA A TAQAICE:

    (Akwai ayoyin Allah a sammai da kassai wadanda Shi kadai ya barwa kanSa sanin adadinsu. Rana daya daga cikin taurari ce dake sararin sama'ud dunya, nisan nisan dake tsakaninmu da sama ne ya sa ba ma iya ganin sauran ranakun. Imani da Allah shi ne yafi muhimmanci fiye da yawan tambaya akan ayoyinSa)

    Bismillahir Rahmaanir Raheem

    Tabbas, Rana (Ash-shams) ba guda 1 ba ce a sararin samaniya kamar yanda wasu mutanen suke tunani. A binciken da Astronomers (masana kimiyyar sararin samaniya) suka gano ta hanyar amfanida na'urar Hubble Telescope, akwai Miliyoyin ranaku a iya birnin taurarinmu wato Galaxy dinmu (da ake kira da Milky Way Galaxy) kuma an gano cewar da akwai Galaxy sama da miliyan dari a sararin sama. Ranarmu da muke iya gani a sararin samaniya tanada nisan shekarun haske (light years) na kusan shekaru 27,000 (Dubu ashirin da bakwai) daga tsakiyar Galaxy dinmu. Amman wani ikon Allah hasken nata yana karasowa duniyarmu ne a cikin mintuna 8 kacal

    Kafin na gindayar da mai tambaya yakamata nayi bayani dalla dalla akan batun mene ne shekarun gudun haske (light years). A cikin 1 second (sekon 1) na agogo, haske yana gudun 300,000km (kilometer dubu dari 300). Misali: ka qaddara kana aiki a company NEPA, wutar lantarkin da ka kunna daga Nigeria zata isa kasar Niger a kasada 1 second (ma'ana kafin ka qifta ido har yan Niger sunga ankawo wutar)

    Kenan a cikin second 1 kacal haske zai iya zagaye duniya sau 7 (300,000km arabata gida 22 zai zamo 13,636km, wanda fadin duniyarmu a diameter shine 13,500km). A lissafin circumference kuma, duniyarmu takai 40,075km, wanda ahakan kana kunno haske zai zagayata sau 7 a cikin second 1 kacal. A taqaicedai gudun haske ya zarce na bindiga, jirgin sama, da kuma rocket. Wannan lissafin second 1 muke, ita kuma rana tanada tazarar shekaru 27,000 na gudun wancan hasken, bawai seconds, mintuna, kwanaki ko watanni ake magana ba, shekaru 27,000 ake magana anan. Allahu Akbar!

    A wannan matsanancin gudun da takeyi kuma bata cin karo da wata tauraruwar a sararin samaniya (Alhamdulillah), kuma a hakan wasu taurarin suna daukeda cincirindon duniyoyi wadanda suke daukeda watanni a tattaredasu. Kuma ko wannensu dawafi (bautar Allah) suke a kewayen duniyarsu. Solar system dinmu tana jujjuyawane a salon juyawar helix/spiral (helix motion) ma'ana katantanwa take tana juyawa a duk awanni 24 (24 hours da muke kira da kwana daya). Misali: ka samu ranwa, ka garata a kas, zakaga tana juyawa, kamar hakane duniyarmu take juyawa

    Wani zaice "Yanaji bana juyawa kuma alhalin ance duniyar tana katantanwa?" Amsar shine "Gravity kokuma kace maganadisu ne yasa baka jin juyawar" Astronomers sungano cewar Rana (Ash-shams) tana ninqaya a sararin samaniya kamar yanda mai iyo yake ninqaya a cikin ruwa. Samada shekaru 2,000 da suka gabata lokacinda mutane irinsu Aristotle suke tunanin Duniya ba ta da farko kuma ba ta da karshe, Rana kuma a tsaye take qiqam, Allah SWT ya fada a cikin Qur'ani mai girma, cewar Rana tana ninqayane a sararin samaniya. Allahu Akbar!

    Hujjar hakan tana a cikin Suratu Yasin ayata 38:

    ( وَالشَّمْسُ تَجْرِي لِمُسْتَقَرٍّ لَّهَا ۚ ذَٰلِكَ تَقْدِيرُ الْعَزِيزِ الْعَلِيمِ )

    يس (38) Yaseen

    "Kuma rãnã tanã gudãna zuwa ga wani matabbaci nãta. Wannan ƙaddarãwar Mabuwãyi ne, Masani"

    Ayata 39 kuma yace:

    ( وَالْقَمَرَ قَدَّرْنَاهُ مَنَازِلَ حَتَّىٰ عَادَ كَالْعُرْجُونِ الْقَدِيمِ )

    يس (39) Yaseen

    "Kuma da watã Mun ƙaddara masa manzilõli, har ya kõma kamar tsumagiyar murlin dabĩno wadda ta tsũfa"

    ( لَا الشَّمْسُ يَنبَغِي لَهَا أَن تُدْرِكَ الْقَمَرَ وَلَا اللَّيْلُ سَابِقُ النَّهَارِ ۚ وَكُلٌّ فِي فَلَكٍ يَسْبَحُونَ )

    يس (40) Yaseen

    "Rãnã bã ya kamãta a gare ta, ta riski watã. Kuma dare bã ya kamãta a gare shi ya zama mai tsre wa yini, kuma dukansua cikin sarari guda suke yin iyo"

    Allah SWT wanda shine ya halicci sammai 7 da kassai 7 da abunda ke cikinsu da tsakaninsu, ShiNe ya fada a cikin Littafin (Qur'anin) da aka saukar dashi qarni 14 (shekaru 1,400) da suka gabata. Gashi kuma Astronomers sun gano hakan kwanannan ta hanyar amfanida Hubble Telescope. Wannan ayar ta 40 da tayi magana akan iyo (swimming) kadai ta isa ta tabbatar maka da mu'ujizar Al-Qur'ani mai girma

    Ba ma gano wata rana ne abin mamaki ba. Kwanannan Professor Michau Kaku (malami a wata jami'a dake kasar Amurka) ya ce sun yi amfani da na'urar JWST (James Webb Space Telescope) sun gano wata Rana a sararin sama, duniyoyi guda 5,000 (dubu biyar) suna zagayeta kamar dai yanda duniyarmu take zagaye ranarmu (ash-Shams). Wannan duk ikon Allah ne jibge a sararin saman duniyarmu. Duk don su zame mana ayoyi akan samuwarSa (Subhanahu wata'ala) kuma don su tuna mana dalilin da yasa ya halicce mu wato mu bauta masa Shi kadai ba tare da yin shirka ba

    A kowanne hali muka tsinci kanmu kada mu sake mu manta aya ta 2 dake cikin Suratu Mulk:

    ( الَّذِي خَلَقَ الْمَوْتَ وَالْحَيَاةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْغَفُورُ )

    الملك (2) Al-Mulk

    "Shi ne Wanda Ya halitta mutuwa da rãyuwa domin Ya jarraba ku, Ya nũna wãye daga cikinku ya fi kyãwon aiki, Shi ne Mabuwãyi, Mai gafara"

    Ya Allah ka bamu ikon bauta maka ka rabamu da shirka da bidi'a ka tabbatar damu akan musulunci kan tafarkin Sunnah bisa fahimtar Salaf

    Wallahu ta'ala a'alam

    Amsawa:

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.