Ashe Kwalayen Digiri Na Da 'Expiry Date’?

    Kuma fa haka ne. Ka ga ban ma taɓa sani ko kula da haka ba sai da abokina Ahmad Sulaiman ya faƙa mun. Digirin boko a mafi yawancin lokuta in ya kai wasu shekaru kana raye to ya kan daina aiki ko yin tasiri a rayuwa.

    Ya ce gaskiyar magana ita ce da zarar mutum ya kai wasu shekaru a duniya duk ƙwarewarsa ko tulin kwalayensa da wuya ka ga an ƙauke shi aiki a ma'aikata ko masana'anta don 'age' shekarunsa sun zarce wato matasa ake so.

    Iyaka dai in mutum ya ci sa'a a ba shi wani ƙwaryaƙwaryar political appointment in abokinsa dake gwamnati yana son a yi da shi in ba haka ba sai dai ya koma wani mai ba da shawarwari wato ya kama yin consultancy,

    Ahmadun ya kara da cewa wasu daga kwalayenmu idan suka kai wani lokaci sai su daina aiki a yi musu ritayan dole su zama wasu abin nune abin tarihi abin ado idan ma za su yiwa mutum kyan adon ke nan ko kuwa ya dinga tiritiri da su.

    Amma sana'a ko aikin hannu wanda mutane ke dogaro da kansu (skills) to mutu ka raba ne tsakanin mai su da su. Sai dai in ba ka da lafiya ko kuma tsufa ya hana ka fita ko yin su amma ba dai a ce ba a son ka a bakin yin su ba.

    Don haka kowa ya kama wata sana'ar yi komai ƙanƙantar ta. Wata rana za ta bawa mai ita abin yi abin dogaro da kai abin alfahari da ma kariya daga wulakanci yayin da duniya ta yi watsi da shi saboda ya manyanta.

    Balle ma ace yana da yaran aiki da ya ƙora su akan taya shi yin sana'ar. A hankali in suka koya su goge suka ƙware to a cikin sauƙi zai tsinci kansa ko da ya yi ritaya. Kuma dai na rufin asiri ba zai taɓa yanke masa ba

    Wato dai kiran da muke yi ga al'uma shi ne ko kana aikin albashi ko ba ka yi cewa a haƙa shaidar samun ilimi (digiri) da ƙwarewar a iya sarrafa abubuwa (skills) musamman ma da yanzu zamani ya zo da hanyoyin masu sauƙi na neman kuɗi ta intanet.

    From the Archive of:

    Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
    Imel: mmtijjani@gmail.com
    Lambar Waya: +2348067062960

    ©2024 Tijjani M. M.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.