Auren 'Yammata Marayu A Jihar Neja

    Gaskiya ana yiwa Musulmi ‘yan Arewa abin da aka ga dama a 'Kasarmu Najeriya.

    Yanzu dai kowa yana da labarin auren ‘yammata marayu da aka ƙudiri niyya aka kuma shirya yi a jihar Neja yau 24 ga watan Mayu, 2024 da Rt. Hon. Abdulmalik Sarkin-Daji Kakakin Majalisar Jihar ya d'auki nauyin gudanarwa.

    Sannan kuma kun ji irin takaddamar da yanzu haka ta wanzu akan lamarin wacca Ministar Harkokin Mata ta Ƙasa Hon. Uju Kennedy-Ohanenye ta ƙalubalanta har ta kai zancen kotu. Dalilinta, wai auren dole za a yiwa marayun nan.

    Tambayoyin da zan yi anan su ne shin ko ministar nan ba ta shige gona da iri ba kuwa? Ta tuntuɓi Kakaki Sarkin-Daji don ta ji ya aka yi ake neman haihuwa a ragaya? Shin akwai wata doka ta Ƙasa da ta hana iyaye su aurar da ‘ya’yansu mata in sun kai munzalin yin aure?

    Ko da inda aka haramtawa wani d'an Najeriya taimakon wasu akan abin da ya dame su muddun abin nan bai saɓawa kundin tsarin mulkin ƙasa ba? Me zai sa a dinga katsalandan akan harkar da ta shafi addini, al'ada da gargajiyar mutane in har bai taɓa halaccin abun ba a Ƙasa?

    Ko kuma dai neman suna ne na a san da zaman ta tana aiki ko duniya su gan ta a fagen ƙwatarwa mata haƙƙinsu wato "feminism" ke nan a ɓangaren ministar? In ba haka ai da sai ta nemi masaniya, bayani, ba'asi da dai irinsu kafin ta bud'a baki ta ce ga zance ga magana.

    Kuma fa abin zai iya zuwa da ƙyashi da baƙin ciki tunda sau da yawa za ka iya samun manyan mata da ba sa fatan alkhairi ga ‘yammata wajen yin aure don suma ba su samu sun yi akan lokaci ba? Don haka duk inda suka ga wata za ta yi aure sai sun nemi su hure mata kunne ko ma su hana ta yi gaba d'aya in damar hakan ta samu.

    Ala ayya halin dai tamu ba irin tasu ba ce. Wai sai daga baya zance ke fitowa cewa za ta nemi zama da masu ruwa da tsaki wato malamai, manyan gari, iyayen marayun nan da za a aurar da ma su kansu ‘yammatan wanda wannan ba komai ba ne illa ihu bayan hari.

    Wani lokaci na kan tambayi kaina wai ina ƙungiyoyi masu kare haƙƙin bil Adama ne? Ina d'aid'aikun ‘yan ƙwatar haƙƙin mata ne? Ina fitattu, gogaggun masananmu Musulmi ne? Na dai ji Ƙungiyar Lauyoyi Musulmi ta Ƙasa (MULAN) ta shiga lamarin wanda abu ne da ya dace. Hakan sara ne a daidai kan gaɓa.

    Gaskiya ya kamata mu dinga yin magana da kakkausar murya game da irin wannan shiga sharo ba shanun da ake yiwa Musulmi ‘yan Arewa akan haƙƙoƙinsu wajen gudanar da rayuwarsu a ƙasar nan. Akwai rashin sanin darajar haƙƙinsu na cewa su ma fa ‘yan ƙasar nan ne masu cikakken iko kamar kowa.

    In fa muna bari kowa ya bushi iska sai ya zo ya tsoma bakinsa a abin da bai shafe shi ba ko ba shi da ilimi akai to a ko da yaushe mune zamu dinga zama wata al'uma mai kama da irin tabarmar nan ta share kazanta a ƙofar shiga d'aki.

    Amma a kullum da matsayinmu, iliminmu, wayewarmu da ƙololuwa addininmu kuma mu bar kanmu mu zama wulakantattu, gafalallu, wofaffu da ba su san ciwon kansu ba su san kishin Kai da Kare haƙƙinsu ba hakan a gaskiya samsam bai dace ba.

    From the Archive of:

    Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
    Imel: mmtijjani@gmail.com
    Lambar Waya: +2348067062960

    ©2024 Tijjani M. M.

    Marayu

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.