TAMBAYA (120)❓
Allah yasaka da alkairi pls tanbayata shine dajjal da yajuju
da majuju wanne ne zaifara bayyana sannan suratul al khaf tana kare mutun daga
fitinar dajjal
AMSA❗
Amin ya rabbal alamin
✍️AMSA A TAQAICE
(Dajjal ne zai fara bayyana. Ya'ajuj da Ma'ajuj daga baya zasu zo domin neman mafita daga wadannan fitin-tinu sai ki yawaita karanta: "Allahumma inni a'uzubika min azabil qabr, wamin azabi jahannam, wamin fitnatil mahya wal mamati, wamin fitnati sharril masihid dajjal" bayan kin gama Tahiyya kafin kiyi Sallama)
Bismillaahir Rahmaanir Raheem
Ingantaccen hadisi ya tabbata cewar Annabi (Sallallahu
alaihi wasallam) ya ce: Annabi Isah (AS) zai sauko daga sama ta 2, hannayensa
dafe da fuka-fukan mala'iku, zai sauka a saman (minaret) hasumiyar masallachin
Ummayad (Masjid Umayyad) dake Damascus, birnin kasar Syria
Lokacin ana gab da sallar Asubah, kowa yana ta tunanin
fitinar da Dajjal yazo da ita, a lokacin Imam Mahdi (Muhammad Bin Abdullahi) ya
bayyana, musulmai suna ganin Annabi Isah (AS) zasu gane shi, zasu ce ya ja su
sallah, sai ya koma wajen mamu yace ga shugabanku nan (ya nuna Imam Mahdi) yace
shi zai ja mu sallah
Ana fitowa za'a doshi kasar Palestine, lokacin Dajjal yana
qoqarin shiga Masjid al-Aqsa don ya kwace masallachin (wanda Aljanu ne suka
ginashi tun a zamanin Annabi Sulaiman AS), nan take sai ya ga Annabi Isah (AS),
ya fita a guje saboda daman yasan shine kadai zai zama sanadin ajalinsa, yana
gudu yana zagwanyewa kamar gishiri a ruwa, sai Annabi Isah dan Maryam (AS) yasa
takobi ya kashe shi a daidai wata kofa da ake kira da Baab Lud dake Palestine
(inada video din wajen yanzu haka, kwanakin baya na taba dora shi a status)
Bayan an kashe Dajjal ana tunanin komai ya lafa, sai kuma
Yajuj da Ma'ajuj su bayyana, suna da matuqar yawa kamar yanda Allah
Azzawajallah ya fada a Qurani mai girma
(حَتَّىٰ
إِذَا فُتِحَتْ يَأْجُوجُ وَمَأْجُوجُ وَهُم مِّن كُلِّ حَدَبٍ يَنسِلُونَ)
الأنبياء
(96) Al-Anbiyaa
"Har sa'ad da aka bũde Yãjũju da Mãjũju alhãli kuwa
sunã gaggãwa daga kõwane tudun ƙasa"
Wasu malaman tarihin sun ce katangar Ya'juj wa Ma'ajuj
itace: "The Great Wall of China" wato babbar katangar China, wasu
kuma sun ce a'a, Katangar dake tsakiyar Asia ce, dake maqotaka da garin Bukhara
da Tirmidh, sunan wajen Darband, wasu kuma suka ce: a Russia katangar take anan
Daghistan kuma ana kiranta da Darband da kuma Bab al-Abwab (Kofar kofofi).
Masana ilimin tarihi irinsu: Yaqut al-Hamawi a littafinsa Mu'jam al-Buldan,
Idrisi (wanda ya fitar da map din duniya) a littafinsa Geographiyah, al-Bustani
a littaginsa Da'irah al-Ma'arif duk sun tafi akan cewar katangar Ya'juj wa
Ma'juj itace Bab al-Abwab
Saidai a shekarar 2008 ne Geoarcheologists (masana ilimin
tarihin kasa) suka gano ainihin katangar Ya'juj da Ma'ajuj a wani waje da yake
yammacin Darband Pass dake maqotaka da yankin kasar Turkey da Iran zuwa
Arewacin Georgia gabashin dutsen Kazbek (tsayin 1,800 meters kusan kafa 5,900),
sunan wajen "The Valley of Daryal (Dariel)" wato kwarin Daryal, yana
tsakanin Qafqaz da Taflas, wannan shine ra'ayi manyan malamai irinsu Wahb, Abu
Hayyan, Ibn Khardad, Allamah Anwar Shah, da kuma Azad, a wajen da akwai wasu
manyan duwatsu guda biyu wanda binciken ya tabbatar da anan katangar take,
wajen da Zulkarnaini ya je ya tarar da wasu mutanen gari da basa jin yarensa
(حَتَّىٰ
إِذَا بَلَغَ بَيْنَ السَّدَّيْنِ وَجَدَ مِن دُونِهِمَا قَوْمًا لَّا يَكَادُونَ يَفْقَهُونَ
قَوْلًا)
الكهف
(93) Al-Kahf
"Har a lõkacin da ya isa a tsakãnin duwãtsu biyu, ya
sãmi waɗansu mutãne
daga gabãninsu. Ba su yi kusa su fahimci magana ba"
(قَالُوا
يَا ذَا الْقَرْنَيْنِ إِنَّ يَأْجُوجَ وَمَأْجُوجَ مُفْسِدُونَ فِي الْأَرْضِ فَهَلْ
نَجْعَلُ لَكَ خَرْجًا عَلَىٰ أَن تَجْعَلَ بَيْنَنَا وَبَيْنَهُمْ سَدًّا)
الكهف
(94) Al-Kahf
Suka ce: "Yã Zulƙarnaini! Lalle ne Yãjũja da Majũja
mãsu ɓarna ne a cikin ƙasa.
To, ko zã mu Sanya harãji sabõda kai, a kan ka sanya wani
danni a tsakãninmu da
tsakãninsu?"
(قَالَ
مَا مَكَّنِّي فِيهِ رَبِّي خَيْرٌ فَأَعِينُونِي بِقُوَّةٍ أَجْعَلْ بَيْنَكُمْ وَبَيْنَهُمْ
رَدْمًا)
الكهف
(95) Al-Kahf
Ya ce: "Abin da Ubangijĩna Ya mallaka mini, a cikinsa
yã fi zama alhẽri. Sai ku taimakeni da ƙarfi, in sanya babbar katanga a tsakãninku da tsakãninsu."
(آتُونِي
زُبَرَ الْحَدِيدِ ۖ حَتَّىٰ إِذَا سَاوَىٰ بَيْنَ الصَّدَفَيْنِ قَالَ انفُخُوا ۖ
حَتَّىٰ إِذَا جَعَلَهُ نَارًا قَالَ آتُونِي أُفْرِغْ عَلَيْهِ قِطْرًا)
الكهف
(96) Al-Kahf
"Ku kãwo mini guntãyen baƙin ƙarfe". (Suka kai masa) har a lõkacin da ya daidaita a tsakãnin duwãtsun biyu (ya sanya wutã a cikin ƙarfen)
ya ce: "Ku hũra
(da zugãzugai)."
Har a lõkacin da ya
mayar da shi wutã, ya
ce: "Ku kãwo mini
gaci (narkakke) in zuba a kansa"
(فَمَا
اسْطَاعُوا أَن يَظْهَرُوهُ وَمَا اسْتَطَاعُوا لَهُ نَقْبًا)
الكهف
(97) Al-Kahf
"Dõmin haka bã za su iya hawansa ba, kuma bã zã su iya
hujẽwa
gare shi ba"
(قَالَ
هَٰذَا رَحْمَةٌ مِّن رَّبِّي ۖ فَإِذَا جَاءَ وَعْدُ رَبِّي جَعَلَهُ دَكَّاءَ ۖ وَكَانَ
وَعْدُ رَبِّي حَقًّا)
الكهف
(98) Al-Kahf
Ya ce: "Wannan wata rahama ce daga Ubangijĩna. Sai idan
wa'adin Ubangijĩna ya zo, ya mayar da shi niƙaƙƙe. Kuma wa'adin Ubangijĩna ya kasance
tabbatacce."
Dangane da batun da mutane suke akan cewar Ya'juj wa Ma'juj
halittu ne masu fala falan kunnuwa, su kwanta da guda daya su rufa da guda
daya, duk wannan zancen mutane ne. Zancen gaskiya shine: su Ya'juj wa Ma'juj
mutane ne daga cikin bani Adam, kuma kakanninsu sune Tatars kuma suna daga
cikin qabilar Mongols. Sun kasance tsatson Yafith dan Annabi Nuhu (Alaihis
Salam) kamar yanda Ibn Khathir (Rahimahullah) yayi bayani a cikin shahararren
littafinsa: Albidaya wan Nihaya
ʿAllāmah
ibn Kathīr, ʿAllāmah Abū al-Layth as-Samarqandī, ʿAllāmah
Abū al-Ḥasan
al-Māwardī, da malamai da yawa duk sunyi bayani a cikin Tafsir dinsu cewar
Ya’jūj da
Ma’jūj sun fito ne daga Yāfith ibn Nūḥ
Idan suka bayyana, za su dinga kashe mutane, ba wanda zai
iya kashe ko da daya daga cikinsu, ko Annabi Isah (AS) ma guduwa zai yi tare da
sauran musulmai zuwa kan wani tsauni
A lokacin ne Allah Azzawajallah zai saka wasu qananan
halittu kamar tsutsotsi su fito a jikinsu su kashe kowannensu, daganan sai a
turo wasu halittu masu dogayen wuya su dauke gawarwakinsu daga kan doron kasa
(suna da matuqar yawa ne)
Bayan komai ya lafa, Annabi Isah (AS) zai koma ga Allah
bayan ya yi aure sannan za'a binne kabarinsa a kusa da na Annabi (Sallallahu
alaihi wasallam) da Abubakar (RA) da Umar (RA), daganan kuma sai addini ya fara
samun tasgaro a fara fasadi a bayyane, lokaci zai zo har a manta da Sallah da
Azumi. Saboda wadatar kudi babu wanda zai karbi Zakkah
A lokacin kuwa tuni an dade da rushe Kaabah, sunan wanda zai
rushe ta "Dhu As-siwaqatayn al-afhaj" ya kwashe zinaren da aka binne
a karkashinta, ya kasance dan kasar Yemen ne (kasar su daya da Sarki Abrahata
wanda yazo da manyan giwaye, yaso ya rushe Ka'abah duba cikin Suratu Fil), Dhu
As-Siwaiqatayn al-afhaj gajere ne, wada, kafarsa ta baude ma'ana gwame ne, kuma
kansa cibir cibir ne kamar yanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya fada a
cikin hadisi ingantacce
Za'a maida masallachin Annabi (Sallallahu alaihi wasallam)
wajen zubar da shara, za a mai da shi kamar gidan zoo, wani wajen ana kiwo,
lokacin Makka da Madina ta koma karkashin mulkin yahudawa (wanda a binciken da
nake yanzu, ya tabbata cewar manufarsu shine su kafa World Totalitarian
Government da sukewa laqabi da The Greater Israel wato babbar Israela)
Shi yasa yanzu suke ta kokarin korar Palestinians daga Gaza,
Rafah, Khan Yunus da sauransu don su mamaye ba iya Palestine ba har maqotansu
wato Misra (Egypt), Syria, Jordan da Jaziratil Arab gaba daya wanda kuma Saudi
Arabia tana ciki
Za'a tashi alqiyama ne ranar Juma'a akan fasiqan kafirai
wadanda basu taba tunanin duniya zata zo karshe ba, kamar daukewar ruwan sama
haka zasu ji, sai kuma karar busa kaho daga Mala'ika Israfil (AS), za'a fara
guje guje, yayin busa ta biyu kuma kowa zai mutu, a busa ta uku ne kowa zai
tashi daga kabarinsa. Allah zai zo (Zuwan da ya dace daShi) tare da mala'iku,
sahu sahu, za'a kawo Jahannama, a shimfida siradi akan Wutar tun daga filin
lahira har zuwa kofar shiga Aljannah. Kowa zai bi takai (Da ni: Usmannoor da
kai/ke mai karatu), gwargwadon ayyukanmu gwargwadon saurin wucewarmu. Sai mu
tsaya mu gyara halayenmu, muyiwa kanmu hisabi kafin ayi mana
Allah yasa mudace yasa muyi kyakkyawan karshe, mu mutu muna
musulmai kan tafarkin Salaf (Magabatan farko)
Sahihin hadisi ya tabbata daga Manzon tsira (Sallallahu
alaihi wasallam)
Yace karanta ayoyi 10 na farkon suratul kahfi suna maganin
fitinar Dajjal ne ba Yajuj wa Majuj ba
(Sahihul Bukhari)
Amman dangane da addu'ar neman tsari daga Ya'juj wa Ma'juj,
abinda yafi sauqi shine karanta "Allahumma inni a'uzubika min azabil qabr,
wamin azabu jahannam, wamin fitnatil mahya wal mamati, wamin fitnati sharril
masihid dajjal"
Ki dinga karantawa bayan kin kammala tahiyya kafin kiyi
sallama
Duba cikin littafin
(Hisnul Muslim)
Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.