Hukuncin Saka Tafarnuwa A Cikin Man Kitso

    TAMBAYA (118)

    Slm barka da warhak Dan allh Ina da tambaya Mainene hukunci saika tafarnuwa aka Misali kasakata acikin maikitso zaka iyayin Sallah ngd

    AMSA

    Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuhum

    Indai har saboda magani ne ya halatta a shafa amman ayi taka tsantsan da yawan shafawa a lokacin sallah

    Saboda Mala'iku suna cutuwa da abin da yan Adam ke cutuwa (kamar dai warin tafarnuwan)

    Tun da hadisi sahihi ya tabbata daga Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce

    "Duk wanda ya ci albasa ko tafarnuwa, to ya nesanta da masallachin mu ya zauna a gida. Tabbas, mala'iku suna cutuwa da abinda yake cutar da yayan Adam"

    (Al-Bukhari 855 & Muslim 564)

    "Hadisan da suke da alaqa da wannan suna da yawa. An rawaito cewar duk lokacin da wani ya zo da bakinsa yana warin tafarnuwa ko albasa Annabi (Sallallahu alaihi wasallam). Dalilin hakan kusa shine saboda mutanen da suke karatun Qur'ani, suke sallah da mala'ikun da suke tare dasu dukkansu suna cutuwa da wannan warin. Don haka duk wani abu wanda yake da wari, kamar irinsu cigarette dukkansu suna daukan hukunci daya ne da wadancan ta hanyar hana su shiga masallachi. Haka kuma warin dake fitowa daga hammata da dai sauransu, wannan hukunci ne gamamme dogaro da hujjar hadisin Annabi (Sallallahu alaihi wasallam). Allah ya taimake mu ya bamu ikon aiwatar da abinda yake so

    (Fatawa Islamiyya, Vol.3, p. 39,40 - Darussalam)

    Amman tunda ke macece kuma a gida kike sallarki, don kin shafa akanki ko kuma a jikinki daboda magani wannan ba matsala, in sha Allahu

    Saidai idan mijinki zai takura to anan bai kamata ki saka ba, sai ki bari idan ba ya nan sai ki saka

    Wallahu ta'ala a'alam

    Amsawa

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.