Limanci Da Kananan Kaya Mai Hoton Tsuntsu

    TAMBAYA (109)

    السلام عليكم ورحمه وبركاته

    Allah ya temaki malan yakara lafiya da Nisan kwana, malan inada tanbayah

    1 Minene hukuncin limanci?

    2 Minene hukuncin limanci da kananan kaya

    3 malan Minene hukuncin limanci da kananan kayah Wanda akwai hoton tsuntsu a jiki koh Kuma rubutu?

    Allah yakara lpia da Kuma Nisan kwana ngd Allah yasaka da alkhairi ameen🙏

    AMSA

    Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuh

    ✍️(Amsa a taqaice: yin limanci ya halatta, makaruhi ne ayi limanci da kananan kaya, haramun ne liman yayi limanci da riga mai zanen hoto)

    Alhamdulillah

    1) Limanci ma'anar sa shine "shugabanci", abune mai matuqar muhammanci a musulunce kuma abune wanda ya halatta a shari'ance. Kuma anfi son ko da tafiya kuke (in har kunkai ku 3) to a tsakaninku ku fitar da shugaba. Kamar hakane a babin Sallah, liman (da larabci Imam) shine jagoran masallata (wato mamu)

    2) Idan mutum yayi limanci da kananan kaya baza'ace ya aikata haramun ba saidai hakan makaruhi ne domin kuwa sutura tana bayyana kamalar mutum a zahirance kuma ko da mutum zai je gidan surukansa zaka ga sai ya kure adakarsa (ta hanyar saka kayansa sababbi) don ganin sirikansa ko kuma wadda zai aura to ina kuma ga wanda zai gana ne da wanda ya halicce sa, Allah (Subhanahu wata'ala)

    Don haka saka sutura mai kyau shine yafi don koyi da maganar Annabi Sallallahu alaihi wasallam da ya ce: "Innallaha jamilun yu hibbul jamal"

    Ma'ana: "Haqiqa Allah kyakkyawane kuma yana son abu mai kyau"

    (Sahihul Bukhari)

    Kuma ita tsafta tana daga cikin imani kamar yanda hadisi sahihi ya tabbatar da hakan

    3) Haramun ne mutum yayi sallah da kayan da suke dauke da hoton abu mai rai (animate objects) domin kuwa zasu dinga daukewa mamu hankali yayin da suke gabatar da Ibadah to ballanta kuma ace liman ne da kansa zai saka irin wannan kayan. Kaga ai idan wadanda ba musulmai ba suka zo shigewa zasu ce ga mamu dai sunyi shigar kamala amman limaminnasu da sauransa

    Ko a jikin bangon masallachi baya halatta a liqa hoto ballantana kuma mutum ya saka a rigarsa har ma ya shigo da ita cikin dakin Allah don aiwatar da Ibadah

    Ko da riga ce mai zanen ko rubutun da zai dauki hankalin mutane bai halatta a shiga da ita masallachi ba saboda gudun daukar alhakin mamu ballantana kuma hoton tsuntsu, kamar hakane Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya umarci Ummul Muminun, Nana Aisha (R.A) akan ta cire labulen da yake a dakinta bayan ya kammala sallah, yace mata ta cire labulen domin kuwa zanen tsuntsayen da suke a jikinsa yana bijiro masa a lokacin da yake sallah

    (Duba littafin: Sifatu Salatin Naby na Shaikh Nasiriddin al-Albany, Rahimahullah)

    Haka kuma Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace mala'ikun rahama ba sa shiga gida wanda akwai sura (zane) ko kare

    (Bukhari da Muslim)

    Indai har mala'ikun rahama bazasu shiga daki ko gida wanda akwai hoto ba to bai kamata wani kuma ya saka hoton a rigar sa ba ya shiga dakin Allah (masallachi) harma ya ja mutane sallah

    Wallahu ta'ala a'alam

    Amsawa

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.