Shin Aljanu Suna Mutuwa Kuma Za Su Shiga Aljannah?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum Malam da fatan Allah shi Qara maka lafiya da tsawon kwana cikin hidimar addinin Allah. Malam tambaya nake da ita kamar haka : Shin da gaske ne Aljanu suna mutuwa? Ko kuwa basu mutuwa ne kamar yadda yawancin mutane suke faɗa?. Shin Aljanu ma zasu shiga Aljannah a lahira? Naga zaluncin da suke yiwa mutane yayi yawa ne.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

    Aljanu suna mutuwa kamar yadda Allah Maɗaukakin Sarki ya faɗa acikin Alqur'ani cewa

    كُلُّ نَفْسٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ...

    Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne... (Suratul Ankabut Aya ta 57)

    To su dinma rai ne dasu kuma Allah ya ajiye musu ajalinsu wato ranar mutuwarsu. Sai dai malamai awannan fannin sun ce su kansu Aljanun nau'i uku ne. Nau'i biyu daga ciki suna mutuwa ta dalilin tsufa ko jinya ko kuma wani tsatsayi kamar dai yadda Bil Adama keyi. Amma akwai nau'i guda waɗanda sune dangin shaiɗan waɗanda Allah ya jinkirta musu sai ranar tashin Alqiyamah.

    Game da shigar Aljanu Aljannah ko wuta, lallai suma Allah zai tashesu aranar Alqiyamah kuma zai yi musu hisabin ayyukansu bayan mutuwarsu. Domin acikinsu akwai muminai mutanen kirki, kuma akwai fasikai da kafirai. Kamar yadda yazo acikin suratul jinni

    وَأَنَّا مِنَّا الصَّالِحُونَ وَمِنَّا دُونَ ذَٰلِكَ ۖ كُنَّا طَرَائِقَ قِدَدًا

    Kuma lalle ne mũ, akwai sãlaihai a cikinmu, kuma akwai a cikinmu waɗanda ba haka bã mun kasance ƙungiyõyi dabam-dabam. (Suratul Jinn Aya ta 11)

    وَأَنَّا مِنَّا الْمُسْلِمُونَ وَمِنَّا الْقَاسِطُونَ ۖ فَمَنْ أَسْلَمَ فَأُولَٰئِكَ تَحَرَّوْا رَشَدًا

    'Kuma lalle ne mũ akwai a cikinmu, waɗanda suka mĩƙa wuya, kuma akwai a cikinmu karkatattu. to, wanda ya mĩƙa wuya waɗancan kam sun nufi shiryuwa.' (suratul Jinn Aya ta 14)

    وَأَمَّا الْقَاسِطُونَ فَكَانُوا لِجَهَنَّمَ حَطَبًا

    'Kuma amma karkatattu sai suka kasance makãmashi ga Jahannama.' (suratul Jinn Aya ta 15)

    Alhafiz Ahmad bn Hajr Al Asqalani ya faɗa acikin littafinsa mai suna "FAT'HUL BAREE" juzu'i na 6 shafi na 346 cewa: "Malaman farko (tabi'ai da tabi'ut tabi'eena) da kuma waɗanda suka biyo bayansu sunyi ittifaqi akan cewa lallai kafiran cikin Aljanu zasu shiga wuta amma sunyi saɓani game da shin Muminan cikin Aljanu zasu shiga Aljannah ne ko ba zasu shiga ba?.

    Ra'ayoyin Malaman sun kasu ne zuwa gida huɗu kamar haka

    1. Ra'ayi na farko: Kwarai kuwa zasu shiga kamar yadda muminan Bil Adama zasu yi. - wannan ita ce fatawar mafiya yawan Malamai.

    2. Ra'ayi na biyu: Zasu kasance ne acikin birbishin aljannah (ba chan cikinta ba) wannan shine fatawar Imamu Malik da wasu malammai da dama.

    3. Ra'ayi na uku: Sune Ma'abotan zama bisa tozon nan na "A'ARAF" wato tsakanin wuta da Aljannah.

    4. Ra'ayi na huɗu: sune maluman da basu ce komai ba game da mas'alar.

    Al Imam Ibnu Katheer acikin littafinsa mai suna "TAFSEERUL QUR'AN (juzu'i na 4 shafi na 141) Yace "zance dai na gaskiya shine muminan cikinsu (su aljanu) kamar muminan Bil Adama ne, zasu shiga Aljannah kamar yadda Mazhabin magabata na kwarai ya nuna. Kuma wasunsu suna kafa hujjah ne da ayar nan ta 56 acikin Suratur Rahman

    فِيهِنَّ قَاصِرَاتُ الطَّرْفِ لَمْ يَطْمِثْهُنَّ إِنسٌ قَبْلَهُمْ وَلَا جَانٌّ

    A cikinsu akwai mãtã mãsu taƙaita ganinsu, wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba kuma haka wani aljani.

    Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya amsa shigen irin wannan fatawar acikin Majmu'ul Fatawa nasa, juzu'i na 19 shafi na 38. Ga abinda yake cewa: "Hakika kafiran cikinsu ababen azabtarwa ne a lahira, bisa ittifaqin malamai. Amma muminan cikinsu to mafiya yawan maluma suna bisa fatawar cewa suna cikin aljannah.

    Amma an ruwaito daga wasu maluman cewa muminan Aljanu zasu kasance ne a Qasan Aljannah, 'Yan Adam zasu rika ganinsu amma su basu ganin 'yan Adam ɗin. Wannan Qaulin an ruwaitoshi daga Imamu Malik da Imam Abu Hanifah da Imamush Shafi'iy da Imam Ahmad bn Hanbal (rahimahumullah).

    Da fatan mai tambayar ya gamsu.

    WALLAHU A'ALAM.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.