Ticker

Shin Fuskar Mace Ita Ma Al'aura Ce

TAMBAYA (107)

Mene ne hukuncin bayyana fuskar mace, kamar matan da suke dora hotunansu a profile picture?

AMSA

Alhamdulillah

Dangane da fuskar mace, jamhurin malamai sun ce gaba daya jikin mace al'aurace, ban da hannun ta da fuskar ta. Dalilin hakan kuwa shine saboda mu'amular da zata iya yi da maza a bangaren cinikayyar siya da siyarwa da makamantansu. Abu Hanifa (Rh) yace mace zata iya bayyana tafin kafarta. Imam Ahmad (Rh) yace mace dole ne ta rufe jikinta gaba daya har farcen ta la'akari da bai halatta mutum yaci abinci da matarsa ba alhalin yayi baqo don kada baqon yaga hannunta

Alqadi, dan mazhabar Imam Ahmad Bin Hanbal ya ce: bai halatta ya hada ido da macen da ba muharramarsa ba face hannunta da fuskarta

Ibn Khathir (Rh) ya naqalto daga al-'Amash wanda ya ce: an karbo daga Sa'id Ibn Jabir (RA) ya rawaito daga Ibn 'Abbas (RA) ya ce: game da ayar da Allah yace su bayyana adonsu face ga abinda ya bayyana, hakan na nufin hannunsu (da zobensu) da kuma fuskarsu

An rawaito hakan daga: Ibn 'Umar, 'Ata, 'Ikrimma, Sa'id Ibn Jabeer, Abi Shasha', Dahak, Ibrahim al-Nakha'i da sauransu

An karbo daga Nana Aisha (RA) tace: "Asma bint Abi Bakr ta shigo wajen da Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace sanye da kaya marasa nauyi, sai ya kauda fuskarsa sannan ya ce: "Asma' idan mace ta kai minzalin balaga to bai halatta ta bayyana kanta ba, saidai iya nan da nan, sai ya nuna fuskar sa da hannunsa"

(Abu Dawud lambata 4104, Al-Albaany ya inganta hadisin a cikin Sahih Abu Dawud, kafin shi kuma akwai Imam Al-Bayhaqi a cikin sunan dinsa, da kuma Al-Mundhari a cikin Targheeb dinsa, da kuma Imam Adh-Dhahabi a cikin Tahdheeb dinsa da wasunsu)

Ibn Khalaf al-Baji (Rh) daga makarantar Imam Malik ya ce: "gaba daya jikin mace al'aura ne ban da fuska da hannaye"

Ibn Hajar al-Haytami (Rh) dan makarantar Imam Shafi' ya ce: Qadi 'Iyad ya ce: "mace ba sai ta rufe fuskarta ba bisa ijtihadin malamai"

Shaikh Muhammad Nasiridddin al-Albaany (Rahimahullah) ya naqalto daga Abdil-Barr (Rahimahullah) a cikin At-Tamheed (6/364), cewar mace gaba dayanta al'aura ce ban da fuskarta da hannayenta, kuma wannan itace fahimtar malaman mazhabobi guda uku (Abu Hanifa, Malik da Ash-Shafi'i), da kuma Imam al-Awza'ee da Abu Thawr

Ibn Abdil-Barr ya ce: "Wannan shine fahimta ijma'in masu ilimi sannan kuma sun ce mace zata bude fuskarta yayin sallah da kuma lokacin da ta shiga ihrami. Sannan kuma sunce ba zata yi sallah sanye da niqab ba kuma ka da ta saka safar hannu. Wannan ya tabbatar da cewar fuska da hannaye ba al'aura bane ba kuma ya ba haramun bane kallonta ma damar ba kallon zargi ko tsana zai yi mata ba

Amman kallon sha'awah wannan kam haramun ne ko da tana sanye da kaya, to ina kuma ga kallon fuskarta (haramcin anan ya karu)

Shaykh al-Albaany ya ce: "Haka kuma na naqalto daga cikin littafin Ibn Rushd cewar fahimtar mafi yawancin malamai shine; fuskar mace ba al'aura bace ba, makamancin hakan ya tabbata a daga Imam an-Nawawy kuma wannan shine fahimtar malaman mazhaba guda uku sannan kuma akwai riwaya guda daya daga Imam Ahmad"

Ibn Qudamah al-Maqdasi (Rahimahullah) a cikin littafinsa; Al-Mughni (1/637) dangane da haramcin mace ta saka niqab da safar hannu a lokacin ihrami, ya ce: "Idan har fuska da hannaye al'aura ne, bazai zama haramun a rufe su ba. Saboda ana buqatar ganin fuskar wanda yake siya ko ake siyarwa da kaya shi kuma hannu a bayyanashi saboda karba ko bayarwa". Ibn Qudamah ya goyi bayan wannan fahimta a cikin littafinsa Al-'Umdah (p.66)

Shaykh Al-Albaany yace saka niqab ba wajibi bane ba saboda abinda Ibn Abbas (Radiyallahu anhu) ya ce: an karbo daga Al-Fadl (dan uwan sa) yana tafiya akan abin hawa tare da Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) sai mace daga qabilar Khath'am ta zo, sai Al-Fadl ya qura mata ido yana kallonta, itama ta kura masa ido. Sai Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya karkatar da fuskar Al-Fadl". Ibn Abbas (RA) yace wannan ya faru ne a lokacin hajjin bankwana

(Sahih Bukhari lambata 1513, 1855 da Sahih Muslim lambata 1334)

A cikin riwayar ance matar ta kasance kyakkyawa ce matuqa. Sai Al-Fadl ya qura mata ido yana mamakin tsananin kyawunta. Hakan ya nuna cewar fuskarta a bayyane take ba a rufe ba

(Usmannoor: wannan fa Sahabi Al-Fadl kenan. To ina kuma ga kai da ni, to anan zamu gane illar dake tattare da bayyana kwalliya da mace take yi a waje musamman irinsu Make Up da sauransu ballantana kuma har ma ta dora hoton ta a profile picture, matsalar shine ba ta san ina hoton zai je ba. Dole wataran fitina zata auku kam. Saidai muce Allah ya sa mu fi karfin zuciyarmu)

Dangane da ayar da Allah (Subhanahu wata'ala) ya ce:

(وَقُل لِّلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنْهَا ۖ)

النور (31) An-Noor

"Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya bayyana daga gare ta..."

Shaykh Al-Albaany (Rh) ya ce: "Abin nufi anan shine fadin Allah "...face abin da ya bayyana daga gare ta", Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yayi bayani cewar: "bai halatta a ga komai a jikinta ba face fuska da hannayenta". Shaykh Al-Albaany ya zayyano sahabban da suka fassarar ayar cewar ban da fuskarta da hannayenta - haka kuma ya kawo sunayen magabatan da suka sahihantar da riwayar:

Daga cikinsu da akwai Uwar muminai, Aisha (Radiyallahu anha) ta rawaito daga Abdurrazaq, Ibn Abi Hathim (Ad-Durr al-Manthoor), Ibn Abi Shaybah, Al-Bayhaqi wanda Ibn Hazm yace sahihi ne. Abdullahi Ibn Abbas (RA: Ibn Abi Shaybah, At-Tahawi, Al-Bayhaqi wanda Ibn Hazm yace sahihi ne. Sannan kuma da akwai riwayoyi guda 7 daga gareshi. Ibn Abbas (RA) ya ce: "Kada su bayyana kwalliyarsu face abinda ya bayyana daga gare ta, na nufin fuska da hannayenta". Shaykh Al-Albaany yace sahihin hadisi ne

(Jibab Al-Mar'ah, p. 59)

Ita kuma wannan riwayar da aka ce Ibn Abbas (RA) ya ce: "Allah ya umarci mata da idan sun fita su dinga rufe fuskarsu su dinga gani da idon su guda daya". Wannan hadisin da'eef ne, bai inganta ba

(Jilbab Al-Mar'atil-Muslimah, p.88)

Dangane da make up da mata suke yi kamar irinsu saka eye-liner, eye-shadow, da saka wasu kaloli a fuska, jan baki, jan farce, blusher, da kuma eye-lashes na bogi (fake eye-lashes) duk wannan haramun ne mace ta bayyanasu ga wadanda ba muharramanta ba, saidai ta boye hannun nata da safa sannan ta rufe fuskarta da niqab. Dukkan bayyana wadannan indai ba ga mazajensu ko muharramansu ba to ya ci karo da fadar Allah (Subhanahu wata'ala):

"Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya bayyana daga gare ta..."

(Suratu An-Nur aya ta 31)

Mata sai a kiyaye in kuma ba so ake a tabo fushin Allah ba, ki gama sabawa umarninSa sai kin tsufa kin zama abar tausayi sannan zai kama ki da wancan laifin da kikai lokacin kina budurwa, ko kuma ya azabtar dake yayin fitar rai, ko a kabari ko kuma a Jahannama. Allah ya kiyaye

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments