Shin Idan Yara Su Kai Azumi Iyaye Ake Bawa Ladan?

    TAMBAYA (103)

    Dan Allah malam wai idan yaro yayi azumi bashi ake bawa ladan ba. yaro karami wanda baifi shekara taraba goma haka. Wasune suke musu wai bashi ake bawa ladan ba

    AMSA

    Alhamdulillah

    An tambayi Shaikh Saleh al-Munajjid dangane da hukuncin ayyukan yaron da bai kai matsayin balaga ba. Ya ce:

    Na'am, yara za'a basu lada idan sukai aikin alkhairi, saboda hadisin da Imam Muslim ya rawaito a cikin Sahih dinsa (1335) daga Ibn Abbaas (Radiyallahu anhum), ya ce: "Wata mata ta daga yaronta tace: "Ya Rasulullah, shin Allah zai karbi hajjin yaron nan?" Sai Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: "Na'am, kuma zaki samu ladan hakan"

    Mawallafin littafin Mawaahib al-Jaleel fi Sharh Mukhtasar Shaykh al-Khalrrl yace akan umarnin da aka bawa yara suyi addu'a idan sun balaga: "Al-Qaraafi yace, a cikin al-Yawaaqeet fi'l-Mawaaqeet: "Yara zasu samu lada idan suka aikata aiki nagari saboda wancan hadisin na macen Khath'ami {da ta daga yaron ta ta tambayi Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yayin aikin Hajji}

    Ibn Rushd ya ce: "Munanan ayyukan yara ba'a rubuta su amman kyawawan ayyuka ana rubuta wadannan, a bayani mafi inganci"

    Ibn Abd al-Baar yace, a cikin littafin al-Tamheed, inda yayi sharhin hadisin macen Khath'ami: "...Abu'l-'Aaliyah al-Riyaahi ya ce: "Umar ibn al-Khattab ya ce: "ana rubuta kyakkyawan aikin yaron da bai balaga ba amman ba'a rubuta mummunan aikinsa"

    Mawallafin Mawaahin al-Jaleel yace, dangane da shiga Ihraam na yara a Umrah da Hajji:

    "Malamai basu samu sabani ba dangane da hukuncin yara za'a basu ladan aiki kyakkyawa (wanda suka yiwa Allah), sannan kuma ana lissafa ayyukansu marasa kyau a matsayin kuskure"

    Haka kuma a cikin Mukhtasar al-Waadihah: "Hajj ba wajibi bane akan yaro ba, har sai ya balaga, yarinya kuma har sai ta fara al'ada amman ba matsala bane idan an tafi dasu aikin Hajji. Sannan kuma mustahabbi ne kuma Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yayi hakan"

    Sannan kuma ya rawaito cewar Talhah ibn Musarrif ya ce: "Yana daya daga cikin al'adun musulmi su tafi aikin Hajji tare da yayansu don neman rahamar Allah"

    Ibn Abd al-Barr, a cikin al-Tamheed, ya ce: "Anso aje aikin Hajji tare da yara kuma ijma'in malamai sun fadi hakan". Haka kuma ya ce: "Ba abin mamaki bane, a ranar lahira, a ga yaro ya samu ladan sallah, zakkah, Hajji da sauran kyawawan ayyuka idan har yayisu kamar yanda shari'ah ta koyar saboda hakan (samun ladan) rahamar Allah ce kamar yanda Allah (Subhanahu wata'ala) yake bada lada ga mamaci idan anyi sadaka a madadinsu. Ba ku ganin cewar, malamai sun yarda akan a umarci yaro yayi sallah idan yakai shekarun wayo, kamar yanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya yi sallah tare da Anas (Radiyallahu anhu) da maraya?

    Yawancin Salaf (magabatan farko) sunce a biya Zakkar marayu, sannan kuma bazai yiwu ace baza'a ladan wannan Zakkah ba. Manyan su, da kuma wadanda suka bayar da Zakkar a madadinsu su ma zasu samu lada silar hakan, kamar yanda wanda ya kaisu aikin Hajji zai samu lada, saboda girman rahamar Ubangiji (Subhanahu wata'ala). An karbo daga Umar (Radiyallahu anhu) ya ce: "Za'a bawa yara ladan kyakkyawan aiki, amman banda mummuna". Banga wani wanda aka fifita ra'ayinsa sabanin wannan ba

    al-Ikmaal ya ce: "Malamai dayawa sunce, yara zasu samu lada idan suki bi umarnin Allah Azzawajallah, zasu samun ladan kyawawan ayyukansu amman banda zunubbansu"

    An rawaito a cikin Awaa'il al-Muqaddimaat, cewar: "Abinda ya inganta a fahimta ta shine: an karfafe su (yaron da wakilinsa) su aiwatar da hakan saboda dukkansu zasu samu lada. Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yacewa wannan macen (da tayi tambaya akan Hajjin dan ta): "...kuma zaki samu ladan hakan". Wallahu ta'ala a'alam

    Ibn Jamaa'ah ya ce: "Malaman mazhabobi hudu sunce, yara zasu samu ladan aiki nagari, ko sun balaga ko basu balaga ba. An karbo hakan daga Umar (Radiyallahu anhu). Wasu malaman sunce akwai ijmaa'in malamai akan wannan hukuncin. Idan muka tattara wadannan hujjoji waje guda zamu ga cewar fadaa'il (falala) ne hakan kamar yanda Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: "Jihadin tsoho da jihadin yaro shine Hajji da Umrah da kuma hujjar da take a cikin wancan hadisi na matar da ta daga dan ta

    Wallahu ta'ala a'alam

    Amsawa:

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.