Sun Yi Zina Da Saurayin Ta Ciki Ya Shiga, Yanzu Ta Aure Shi, Mene Ne Matsayin Aurensu?

    TAMBAYA (104)

    Aslm. Wllh wataqawatace sukayi aure da saurayinta ammah kafin auran sundanyi rashinji dan hartasami Ciki kafin aure. Kuma batafadawa iyayentaba tanada Ciki wata Daya akadauramata auren ahaka gashi har sunhaihu bayan wanna Dan da sukahaifa sunkara Yara Biyu

    Shine take wasiwasi akan auran yanzu wai ya matsayin auranta. Ahuta lafiya

    AMSA

    Lahaula wala quwwata illa billah

    Laifin aikata zina yana daga cikin manyan alkaba'ira (zunubbai) domin kuwa idan ka dauke laifin Shirka, Kisa, da cin Riba to sai laifin Zina

    Saboda girman laifin ne ma Allah (Subhanahu wata'ala) a cikin Suratul Israa, yace kada mu kusanci zina;

    ( وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا )

    الإسراء (32) Al-Israa

    "Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha ce kuma tã mũnãna ga zama hanya."

    Ba ma aikata zinar ba, kusantar ta ma laifi ne babba

    Sannan kuma Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: "Da danyaku ya taba macen da ba muharramar sa ba, gara a saka kusa a kansa a buga da guduma shine yafi masa sauqi"

    (Sahihul Bukhari)

    Haka kuma lokacin da Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yayi mafarkin an nuna masa wasu mata da aka rataye mamansu da qugiya, an rura wuta tana ci ta kasansu, kamar suna cikin gidan biredi ana gasasu, sunata kwarmata ihu saboda azaba ya tambayi mala'iku mene ne laifin wadannan suka ce masa wadannan mazinata ne

    (Sahihul Bukhari)

    Dangane da hukuncin auren su, ba wanda zai ce auren su bai yi ba tunda kowanne aiki da niyya ake yin sa kuma Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: "Innamal a'amalu binniyati" ma'ana: "Kowanne aiki yana tare da niyya"

    (Bukhari da Muslim, Musnad na Imam Ahmad, Abu Dawud)

    Kafin suyi aure sunyi niyyar aikata zina kuma har ciki ya shiga

    Sannan kuma lokaci guda sai sukai niyyar aure shima wannan niyyar daban take

    Rashin sanar da iyayen nata cewar tana dauke da juna biyu shine maslaha ga rayuwarta, rayuwar mijinta da iyayenta da kuma rayuwar shi kansa abinda ke cikinnata

    Domin kuwa Allah ya rufa musu asiri, sunyi laifi a boye, to don me kuma zata yi kokarin fadawa iyayenta ga abinda sukai?

    Allah Gafurur rahim ne, yana gafarta kowanne zunubi amman banda shirka shima idan ka mutu kana yi ne. Idan Allah yaga dama yana yafe kowanne zunubi ko kuma ya yiwa bawanSa azaba gwargwadon girman zunubinsa kamar yanda ya fada a cikin Qur'ani:

    ( أَلَمْ تَعْلَمْ أَنَّ اللَّهَ لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ يُعَذِّبُ مَن يَشَاءُ وَيَغْفِرُ لِمَن يَشَاءُ ۗ وَاللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ )

    المائدة (40) Al-Maaida

    Shin, ba ka sani ba cewa lalle ne, Allah Shi ne da mulkin sammai da ƙasa, Yanã azãbtar da wanda Yake so, kuma Yanã yin gãfara ga wanda yake so, kuma Allah a dukkan kõme, Mai ĩkon yi ne?"

    Don haka daga ita har mijin nata sai suyi ta tuba (Taubatun Nasuha) akan zaluntar kansu da sukayi kamar yanda Allah ya ce:

    ( فَمَن تَابَ مِن بَعْدِ ظُلْمِهِ وَأَصْلَحَ فَإِنَّ اللَّهَ يَتُوبُ عَلَيْهِ ۗ إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ )

    المائدة (39) Al-Maaida

    "To, wanda ya tuba a bãyan zãluncinsa, kuma ya gyãra (halinsa), to, lalle ne Allah Yanã karɓar tubarsa. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai"

    Don haka auren su yananan daram, kawai su rufawa kansu asiri su ci gaba da raya sunnar Annabi (Sallallahu alaihi wasallam), ita kuma ta dinga yi masa biyayya musamman ma idan ya neme ta domin kuwa duk sanda suka raya sunnah to akwai lada mai yawa da Allah yake bayarwa ga mata da miji daga lada 10 zuwa 100 har zuwa 700 wasu kuma ya ninninka musu ba iyaka kamar dai yanda idan kuma mazina ci ya aikata zina zai samu zunubin wannan mummunan aikin

    Kamar yanda Manzon ALLAH () Ya ce: “Mala'ikan da yake hagu (wanda yake rubuta zunubi) Yana ɗaga alƙalaminsa har tsawon awanni shida bayan musulmi yayi laifi yana jiran ko zai yi da-na-sani ya roƙi gafarar ALLAH, idan ya tuba kafin haka sai Mala'ikan ya fasa rubuta shi, idan bai tuba ba, bayan wannan lokaci sai ya rubuta masa zunubi ɗaya.”

    [Saheehul Jamii: 2097]

    Haka kuma Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: "Kullu bani adam khadda'un, wa khairu khadda'un attawwabun" ma'ana: "Dukkan bani adam masu laifi ne saidai wadanda suka fi alkhairi cikinsu sune masu yawan tuba"

    (Bukhari da Muslim)

    Ya Allah ka tsaremu daga aikin da na sani ka yafe mana zunubbanmu na zahiri da na badini sannan ka bamu iyali nagari

    Wallahu ta'ala a'alam

    Amsawa:

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.