Tarihin Sarautar Chiroma

    Sarautar CIROMA sarauta ce data Samo Asali daga kasar barno wato sarauta ce ta bareri Kuma tarihi ya tabbatar da An Fara yin wannan sarauta tin zamanin sarakunan saifawa a kasar barno kenan tana cikin sarautu tsoffafi Suma kasar Hausa Sarautar Chiroma ta Dade sosai domin Akwai ta cikin Hakiman sarakunan Habe  Kalmar CIROMA kalmace ta kanuri Kuma In mun duba zamuga Harafi shida ne ya fidda wannan suna Kuma jumla uku ce ta Hada sunan CIROMA kowacce jumla nada ma'anarta a Harshen kanuri in mun bi su daya bayan daya mun fassara su daga Kanuri zuwa Hausa zamu samu  CI na nufin lokacina ko zagayena Kalmar RO) na nufin rayuwa (Afassrarmu zamu ce Mai Rai)
     MA nanufin Mai rikewa (Mai rike kasa) in mun dunkule jumlolin cikin Hausa cikkakiya da zata fito da ma'anar sunan zamuce WANDA ZAI RIKE SARAUTA BAYAN RASUWAR MAI CI A YANZU  ma'ana CIROMA nanufin Mai jiran Gado bayan rasuwar sarki   wannan sarauta ta yadu sosai a masarautun Hausa da fulani Kuma Anfi yiwa babban Dan sarki Wanda sarkin ke fatan zamowa sarkin bayan Babu shi Dukda cewa Ana bawa wani cikin yayan gidan sarauta wannan sarauta Koda ba Dan sarkin bane na cikin sa ba Amma dai bata fiya futa daga cikin yayan sarauta ba wato Wanda zasu iya yin sarki Sarautar CIROMA sarauta ce kasaitacciya Kuma a mafi Yawan Lokaci tana dace da kasaitatun yayan sarki da suke rike da ita Sannan a tsarin girma girman sarauta tana cikin manyan sarautu a Kano ma Sarautar Chiroma na cikin Tara ta Kano  Kuma An samu Wanda suka Yi sarki daga Sarautar CIROMA

    Kamar sauran sarautu itama Sarautar CIROMA Masartan fada suna Yi Mata kirari da cewa RAGAMA DAN DATTO ZINARIYA ABAR WASOSO LABI DAN MASU GARI  DANDA  JUMUNA TANKAN TASHI TAFI SAUKAR RESHE.

    Janye Hannu: Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar wannan rubutu.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.