Auren Dan Dariqa

    TAMBAYA (125)

    Asalamu alaikum mlm muna ftn kana lpy. Mlm akan wanan fatawar naji ance mlm mutum yana iya auren wanda b mslmi b amma naji kace darika b mslmci bace amun karin haske akan wanan fatawar. Yanxu sbd mtm yana darika har za a iya hanashi aure

    ✍️AMSA A TAQAICE

    (Imam Malik (Rahimahullah) yace: "Kada ku auri mace yar Bidi'a ko kuma ku aurar da ita ga dan Bidi'ah ko gaida dan Bidi'ah..."

    (al-Mudawwanah, 1/84)

    Imam Ahmad bin Hanbal (Rahimahullah) ya fadi makamancin haka

    Sannan kuma Allah (Subhanahu wata'ala) baya karbar aiki sai wannan aikin ya cike matakai guda 3

    1) Addini (Musulunci)

    2) Ikhlas (Yi don Allah)

    3) Mutaba'a (Yanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya koyar)

    Bismillaahir Rahmaanir Raheem

    Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuh

    Tabbas dariqa ba addini ba ce kuma duk wanda kika ga ya karbi dariqa to ya jahilci fadin Allah (Subhanahu wata'ala) da yace ya kammala addininSa tun kafin rasuwar Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam)

    Domin kuwa addinin musulunci a kammale yake baya buqatar kwaskwarima, ragi ko kari kamar yanda Allah (Subhanahu wata'ala) ya fada

     الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ دِينًا

    المائدة (3) Al-Maaida

    "A yau Nã kammalã muku addininku, Kuma Nã cika ni'imaTa a kanku, Kuma Nã yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku"

    Bayyanar dariqa kuma sai aka qirqiro abubuwa kala - kala da sunan addini sannan kuma ba'a tsaya anan ba sai aka saka su a cikin addinin da yake kammalalle

    Sayyadina Umar bin Khattab (Radiyallahu anhu) yace: "Wallahi nasan ranar da aka saukar da wannan ayar, Allah ya saukar da wannan ayar ne da yammacin Arfa a ranar Juma'ah"

    (Sahihul Bukhari)

    Bayan saukar wannan ayar, Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) bai kara kwanaki 100 a duniya ba, yayi wafati

    Misalin karin da akayi a cikin addini shine bukukuwan da yan Dariqa da Yan Bidi'ah suke na Maulidi da sunan ibadah. A cikin sahabbai babu wanda yayi maulidi hakama a cikin tabi'ai da atba'ut tabi'in

    Duk da cewar yin Maulidi bidi'ah ne saidai hukuncin sa ya danganta da wadanne irin ayyuka akayi a taron Maulidi. Wasu ayyukan suna kaiwa zuwa ga shirka kai tsaye kamar kiran wani ba Allah ba ko kuma dangantawa Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) siffofin Allah Azzawajallah. To amman idan ba'a kai wannan matakin na shirka ba za'a kira wanda ya halarci wajen da fasiqi amman ba kafiri ba sannan kuma fasiqancinsa ya danganta da ayyukan bidi'ar da ya aiwatar

    Allah (Subhanahu wata'ala) baya karbar aiki sai wannan aikin ya cike matakai guda 3

    1) Addini (Musulunci)

    2) Ikhlas (Yi don Allah)

    3) Mutaba'a (Yanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya koyar)

    Dangane da batun auren dan Dariqa mai aikata bidi'o'i irinsu Maulidi shima wannan ya danganta da wanne aiki yayi a cikin Bidi'ar. Idan yayi shirka ne to bai halatta ta aure shi ba saboda fadin Allah

    وَلَا تَنكِحُوا الْمُشْرِكَاتِ حَتَّىٰ يُؤْمِنَّ ۚ وَلَأَمَةٌ مُّؤْمِنَةٌ خَيْرٌ مِّن مُّشْرِكَةٍ وَلَوْ أَعْجَبَتْكُمْ

    البقرة (221) Al-Baqara

    "Kuma kada ku auri mãtã mushirikai sai sun yi ĩmãni: Kuma lalle ne baiwa mũminaita ce mafi alhri daga ɗiya kãfira, kuma kõ da tã bã ku sha'awa..."

    Wannan auren ya rushe da Ijma'in malamai

    Idan har Bidi'ar ba ta kai matakin kafirci ba, to duk da haka malamai sun yi gargadin akan auren dan Bidi'ah

    Imam Malik (Rahimahullah) yace: "Kada ku auri mace yar Bidi'a ko kuma ku aurar da ita ga dan Bidi'ah ko gaida dan Bidi'ah..."

    (al-Mudawwanah, 1/84)

    Imam Ahmad bin Hanbal (Rahimahullah) ya fadi makamancin haka

    Malaman Mazhahabobi guda 4 sun ce banbancin aqidar addini tsakanin namiji da mace abune da ya zama tilas a dauke shi da matuqar muhimmanci. Fasiqi bai cancanci auren mumina ba. Saboda Allah Azzawajallah yace

    ( أَفَمَن كَانَ مُؤْمِنًا كَمَن كَانَ فَاسِقًا ۚ لَّا يَسْتَوُونَ )

    السجدة (18) As-Sajda

    "Shin, wanda ya zama mũmini yanã kamar wanda ya zama fãsiƙi? Bã zã su yi daidai ba"

    Ba kokwanto akan cewar Bidi'ah a cikin addini yana daga cikin mafi girman fasiqanci. Maida hankali akan aqida na nufin idan mijinta fasiqi ne ko kuma ya bayyana ga waliyyanta cewar fasiqi ne bayan auren to macen ko waliyyan suna da damar raba auren amman idan suka ce sun yarda da su ci gaba da zaman auren to aurensu yananan daram

    Don haka sai ayi taka tsantsan da irin wannan auren, tun da namiji shine gaba da mace (qawwaamah) kuma zai iya koya mata Bidi'o'i ko kuma ya hanata koyi da Sunnah. Dangane da yayansu kuma, al'amarinsu yafi muhimmanci saboda da akwai yiwuwar ya koya musu Bidi'ah ta yanda zasu bijirewa tafarkin Ahl al-Sunnah kuma hakan zaiyiwa mahaifiyarsu wahala tunda ita tana bin minhajin Ahlus Sunnah wa'l-Jamaa'ah ne

    A karshe, malaman Ahlus Sunnah sun ce Makrooh ne mace ta auri dan Bidi'ah. Ma'ana an qyamaci hakan amman inda haramcin yake shine idan aka gano yana aikata Bidi'ar da take zama shirka. Kinga anan ai ko ke bazaki so zama tare da shi ba

    Duk wanda ya rabu da wani abu saboda Allah to zai mallaka masa abinda yafi na bayan alkhairi

    Wallahu ta'ala a'alam

    (Mawqif Ahl al-Sunnah wa’l-Jamaa’ah min Ahl al-Ahwaa’ wa’l-Bida’ by Dr. Ibraaheem al-Raheeli, 1/373-388)

    Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

    Amsawa

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.