Ayoyin Allah A Sararin Samaniya

    TAMBAYA (132)

    Don Allah  ilimantar damu akan ayoyin Allah dake sararin samaniya. Kamar irinsu girman sama da fadin ta da masana kimiyya suke ta bincike akai

    ✍️AMSA A TAQAICE

    Allah (Subhanahu wata'ala) da ya halicci sama'ud dunya Shi kadaiNe yasan girmanta da fadinta. Astronomers sunce a iya Galaxy dinmu akwai taurari sama da Trillion sau Billion sau 125. Sannan kuma ahakandai akwai Galaxy samada Million 100 zuwa 300 kuma dukkansu a sama'ud dunya suke (Wallahu a'alam)

    Bismillaahir Rahmaanir Raheem

    Sararin sama tanada matuqar girma da fadi, domin kuwa dukkan wani nau'in ilimin da yake a duniyarnan da ya shafi kimiyya da fasaha kamar irinsu Medicine, Engineering, Agriculture, Microbiology da sauransu, inda za'a hadesu basukai 1% bisa 100% na ilimin abinda yake a sararin sama'ud dunya ba. Allahu Akbar !

    Bayani muke akan sama'ud dunya kadai (1st heaven) bawai sama ta 1 ba, ta 2,3,4,5,6 ko ta 7 ba ballantana kuma Aljannah wadda tana sama ta 7 kusada Sidratul Muntaha wadda fadin Aljannar musulmi 1 tafi kassai 7 da sammai 7 idan za'a hadesu waje guda, kamar yanda Allah (Subhanahu wata'ala) ya fada

    ( وَسَارِعُوا إِلَىٰ مَغْفِرَةٍ مِّن رَّبِّكُمْ وَجَنَّةٍ عَرْضُهَا السَّمَاوَاتُ وَالْأَرْضُ أُعِدَّتْ لِلْمُتَّقِينَ )

    آل عمران (133) Aal-Imran

    "Kuma ku yi gaugawa zuwa ga nman gãfara daga Ubangijinku da wata Aljanna wadda fãɗinta (dai dai da) sammai da ƙasa ne, an yi tattalinta dõmin mãsu taƙawa"

    Batun tsayin gidan ka a Aljannah kuma Allah kadai ne yasani tunda a al'adance munsan tsayin abu yafi fadinsa

    Sammai da kassai guda bakwai daya bisa daya Allah ya dorasu, ma'ana kamar dai ka samu qwarya ka wulla kobo a cikinta, dan karamin misali kenan. Idan muka koma cikin hadisin Ma'aiki SAW ya bamu labarin girman sammai a cikin tafiyar da yayi ta Isra'i da Mi'iraji inda yayi bayani akan da za'a dauki duniyarnan tamu ta Ard a wullata cikin sama ta 1, to yanda kasan an wulla zobe ne a cikin sahara. Haka kuma da zaka wulla sama ta 1 da abinda ke cikinta, ka sakata cikin sama ta 2 da bazata wuce girman zobe ba a cikin wata saharar. Haka abin yake har zuwa sama ta 7. Allah (Subhanahu wata'ala) yace

    ( أَلَمْ تَرَوْا كَيْفَ خَلَقَ اللَّهُ سَبْعَ سَمَاوَاتٍ طِبَاقًا )

    نوح (15) Nooh

    "Ba ku ga yadda Allah Ya halitta wasu sammai bakwai ɗabaƙõƙĩ a kan jũna ba?"

    Yakai dan uwa/yar uwa, da ace zaka daga kanka sama yanzun a matsayinka na wanda yake a Africa, arewacin Nigeria maybe Kano sai kace sama ta 1 ta fara ne daga can (inda idanunka suke iya gani) to wadanda suke a China, birnin Beijing daga kudanci sukuma haka zasuce a'a sama tafara daga can ne (Kaga kenan anan anyi hannun riga tsakanin wanda yake a Kano ta Nigeria dakuma wanda yake a Beijing ta China), la'akarida duniyar kamar qwan jimina take (Spherical in shape) kamar yanda Allah SWT yace "Wal'ardi ba'ada zalika duhaha" ma'ana "Kuma muka shimfida kasa bayan haka muka maida ita kamar siffar qwai (Qwan jimina)" A cikin Suratu Nuh ayata 19 kuma sai yace: "Kuma Allah ya sanya muku kasa shimfidaddiya", wannan ayar wasu mutane da ake kirada yan flatter earth suke kafa hujja da cewar ai duniya a shimfide take bawai a mulmule kamar qwai ba, wanda hakan kuskurene domin kuwa maybe iliminsu bai kai cikin ayar can ta farko ba wadda har misalinta aka bamu (Kamar qwan jimina), hakan yasa a karkace take a matakin degree 23.5° (Zaku iya duba office din wasu Principals din makarantun boko idan akwai World map in Globe form zaku gane sosai) Ina tunanin bayanin hadisin can na kamar an wulla zobe ya fito fili a misalinnan da na bayar

    Sannan kuma a cikin Suratul Mulk ayata 3 Allah (Subhanahu wata'ala) yace

    ( الَّذِي خَلَقَ سَبْعَ سَمَاوَاتٍ طِبَاقًا ۖ مَّا تَرَىٰ فِي خَلْقِ الرَّحْمَٰنِ مِن تَفَاوُتٍ ۖ فَارْجِعِ الْبَصَرَ هَلْ تَرَىٰ مِن فُطُورٍ )

    الملك (3) Al-Mulk

    Shi ne wanda Ya halitta sammai bakawi, ɗabaƙõƙi a kan jũna, bã za ka ga goggociya ba a cikin halittar (Allah) Mai rahama. Ka sãke dũbawa, ko za ka ga wata ɓaraka?

    Sannan kuma a ranar lahira gaba daya duniyarnan tamu a tafin hannun Allah (Subhanahu wata'ala) take. A nannade a hannunSa na dama kuma daukacin sammai ne kamar yanda ya fada

    ( وَمَا قَدَرُوا اللَّهَ حَقَّ قَدْرِهِ وَالْأَرْضُ جَمِيعًا قَبْضَتُهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَالسَّمَاوَاتُ مَطْوِيَّاتٌ بِيَمِينِهِ ۚ سُبْحَانَهُ وَتَعَالَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ )

    الزمر (67) Az-Zumar

    Kuma ba su ƙaddara Allah a kan haƙĩƙanin ĩkon yinsa ba: qasã duka damƙarSa ce, a Rãnar qiyãma, kuma sammai abũbuwan naɗewa ne ga dãmanSa. Tsarki ya tabbata a gare Shi, kuma Ya ɗaukaka daga barin abin da suke shirki da shi

    Komai da komai da muke iya gani da wanda ma bama iya gani a duniyarnan kokuma a sararin samaniya bauta suke ga Allah SWT ko mun gane ko bamu ganeba. Allahu Akbar !

    Wata bautar Allah yake, hakama rana da taurari, duk suna dawafi ne a sararin samaniya kamar yanda Allah ya tsara musu, kuma basa qetarewa basa gajiyawa, dan Adam da Aljanu ne kadai suke bijirewa saboda anbasu damar zabi, sai sukabi son zuciya suka bijire. Ahakan dan Adam ne yafi kowa iya bautawa Allah yanda ya dace. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah SWT, Ubangijin talikai

    Ya Allah ka tabbatar damu akan bautarKa ka rabamu da Shirka da Bidi'ah ka sa mu mutu muna bin Sunnar ManzonKa (Sallallahu alaihi wasallam) bisa fahimtar Salaf (Magabata na qwarai)

    Wallahu ta'ala a'alam

     Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

    Amsawa

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.