Dabbar Da Ta Fi Falala Wajan Yin Layya

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Malam wacce dabba ce ta fi falala wajan yin layya da ita?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Malamai sun yi saɓani akan dabbar da ta fi falala wajan layya tafuskar nau'in dabbar. Magana mairinjayen dalili itace; Dabbar da tafi falala wajan layya Itace Raqumi Sannan Saniya Sannan Tarayyah wajan yanka Saniya haka Abu Hanifa da Shafi'i sukace.

    Saboda Abunda ya tabbata acikin shihul bukhari ( 2001) daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam wajan bayanin falalar juma'a yace: Wanda yayi wanka rananr juma'a wankan janaba sannan yayi sammako zuwa masallaci asa'ata farko kamar yagabatar da sadakar rakumine, wanda yaje asa'a tabiyu kamar yagabatar da sadakar Saniya ne, wanda yaje asa'a ta uku kamar yagabatar da rago mai qaho ne, wanda yaje asa'a ta huɗu kamar yagabatar da zakara ne, wanda yaje asa'a tabiyar kamar yagabatar da kwai ne, idan liman yafito mala'iku zasu halarto suji khuduba. Bukhari (881) da Muslim (850).

    Domin yanka ne da'ake neman kusancin Allah dashi, sai raquma tafi falala kamar hadaya, yi da Rago yafi falala akan mutane su haɗu suyi da Raqumi domin Zubar jini shine manufa a layya, Wanda yake shi kaɗai zai samu kusancin Allah da zubar dashi baki ɗaya, A cikin tumaki da awaki rago shine yafi falala, domin dashi Annabi Sallallahu Alaihu wasallam yayi layya, saboda yafi kyawun nama. Duba Al-Mugni (13/366)..Kamar Yanda yazo a fatawa Lajnah (11/398).

    Abunda ake hujja dashi cikin hadisin shine yanda aka samu fifikon kusantar Allah tsakanin Raqumi da Saniya da Tumaki da Awaki Saboda raqumi yafi kuɗi da yawa da nama da amfani, Haka Malaman mazhabobi ukun nan sukace. Abu hanifa, da Shafi'i, da Ahmad.

    Imamu Malki yace: Abunda yafi falala wajan layya shine ragon daya shekara ɗaya, sanann Saniya, sannan Raqumi.

    Domin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yayi layya da raguna guda biyu, shi kuwa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam baya aikata abu sai wanda yake yafi falala.

    Amsa akan wannan sai ace: Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya zaɓi ragone don sauqaqawa Al'ummarsa, domin suna koyi dashi, Bayaso ya taqurawa Al'ummarsa, haqiqa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya bayyana falalar raqumi akan Saniya.

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.